༺༻🌹༺༻
࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍*🇧ᝪN ᝪN ᝪ...!*
[𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍
༺༻🌹༺༻*Տᴛ⌾ℛℽ & ᗯℛⅈᴛᴛℰℕ*
*ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩*©®-'Yᴀʀ 𝓢𝓲𝓭𝓲 ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ*🌹ℙaℊℰ❏☞9-10*
Tun misalin K'arfe hud'u da minti biyar Hanan ta kammala duk wasu ayyuka da za ta yi na cikin gida, daga bisani ne kuma ta shi ga 'toilet' don watsa ruwa, ta na fito wa ta shige d'aki ta gyara jikinta tsaf! Ta fito cikin shigar atampa d'inkin riga da zani me dogon hannu da wuya, kayan sun yi matuk'ar yi ma ta kyau sosai tamkar sabuwar amarya.
Samun waje ta yi ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun da ke jere a falon, ya yin da ta tuna rashin dawowar Rumaisa gidan ne kuma zuciyarta ta dugunzuma ranta ya b'aci take fuskarta ta canja, duk wasu alamomin damuwa da b'acin rai su ka bayyana kan fuskarta, da sauri ta mik'e tsaye zuciyarta na tafarfasa ji ta ke tamkar ta fashe da kuka dan tsananin takaici da damuwa, wani sashi na zuciyar ta ne ya rink'a rarrashinta tare da sak'a ma ta cewar yanzu za ta dawo, takaici ya yi katutu cikin zuciyar Hanan gami da taraddadin dawowar mahaifinta.
Zciyar ta ta ci gaba da sak'a ma ta cewa 'muddin Rumaisa ta dawo ranta ne zai mugun b'aci duk da cewa ba ta tava yin irin hakan ba' Hanan ta jinjina kai bayan da ta ke ci gaba da wasu sak'e-sak'en zucin na dangane da irin hukuncin da za ta yi wa Rumaisa da zarar ta dawo, domin kuwa babu abin da Hanan tafi tsana irin yaro ya fita ya kai har dare, bare kuma a ce Rumaisa wadda ta d'auki so da k'auna ta d'ora ma ta.
Wannan ya sa ta d'aukar wa zuciyarta alk'awarin muddin Rumaisa ta dawo sai ta zane ta, sai dai kuma har a lokacin Rumaisa ba ta dawo ba, dan haka duk wa ta walwala da farin ciki su ka k'aurace wa Hanan.
Hankalin Hanan ya yi matuk'ar tashi ganin yadda lokaci ya ke ta k'ara tafiya ba tare da Rumaisa ta dawo ba, har wajen misalin k'arfe shida da rabi Hanan ke jiran isowar Rumaisa, ga gidan ba kowa, tunaninta d'aya inda za ta sami Rumaisa, wai shin ina Rumaisa ta tafi?, ta juma ta na sak'a hakan, dan ko zama ta kasa yi a tsaye take ta na ta zaga tsakiyar falon.
Ka sa jure ganin hakan ta yi ba shiri ta d'auki mayafi ta yafa ko takalmi ba ta saka ba ta lek'a waje, sai dai kuma wajen ma babu kowa, face wani k'aramin shago da ke bud'e, layin dai tamkar an yi shara haka ta rink'a kallonsa domin babu yaro ko k'waya d'aya wanda za ta iya aika, ko dan magriba ta gabato ne kuma oho! ta fad'a a ranta bayan ta jinjina kai, daga bisani kuma ta tab'e baki kad'an.
Komawa cikin gida ta yi ta d'auko takalmi sannan ta fito bayan da ta janyo k'ofar gidan ta rufe.
Kai tsaye shagon da ke bud'e ta nufa ta na lallek'a cikin shagon kamar mara gaskiya, babu kowa ciki al'amarin da ya k'ara ba ta mamaki kenan cikin zuciyarta ta ce 'wannan wanne irin al'amari ne a ce layin ba kowa shagon ma ga shi a bud'e amma babu kowa? kai! Jama'a', Ta na gama fad'ar hakan ta ji yo magana kamar daga sama a bayanta "Ki na son siyan wani abu ne?" da sauri gabanta ya yanke ya fad'i k'irjinta ya rink'a bugawa da sauri-sauri, dan ba ta yi tsammanin jin wannan sautin ba.
Ba shiri ta waigo da sauri dan ganin me magana, matashin yaro ne da ba zai wuce kimanin shekaru ashirin da biyu zuwa da uku ba, ta na kallonsa ta ja ajjiyar zuciya mai k'arfi kafin ta ce "Deeni da man kai ne? wallahi duk ka sa na tsorata, ga layin na ga ba kowa, ga shagon a bud'e shi ma kuma babu kowa ciki" dariya Deeni ya yi kafin ya ce "kin san unguwar ta mu daman ba ta cika yawan mutane ba, kuma ga lokacin masallaci ya gabato shiyasa ki ka ga shuru ba mutane a layin, ni ma ba nisa na yi ba, ina hango me shigo wa, wani abun za ki siya kuma kika zo da kanki Anti Hanan me makon ki aiko Rumaisa?"

YOU ARE READING
BONONO...! [𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]
Short StoryRayuwa mai cike da ban al'ajabi gami da hargitsi, ya yin da sharri ke juya wa ya koma wajen mai shi.