Part 1-2

16 2 0
                                    

*FORCED MARIAGE*

Nu'aiyma Abdullahi Tafida

Marubuciyar👇
Tweens ne
Nu'aiymatou
Almansoor
Cin Amana ko Fansa?
Ɓadda Kama
One Blood
And Now
Forced Mariage

_All Thanks to Allah SWT for the privilege to start this book...my special greetings to My lovely Family😍my siblings and cousins ain't left behind too, ina son ku gabaɗaya....my lovely fans that have waited so long for Nu'aiyma Abdull! ga *FORCED MARIAGE* I know u all will love it In sha Allah, big Warnig⚠️Haƙƙin mallakata ne ban yadda a juyamin lbr tako wane siga ba tare da izinina ba! and please muyi respecting juna ni da ku banason kace-nace fiction ne gabaɗaya._

Page 1-2

A hankali yake cin fruit Salad ɗin dake gabansa kansa a sunkuye yana murmushin nan nasa mai kyau da ya kai ga har ana iya ganin dimples dinsa, ya girgiza kai sannan ya dago yana kallon matashiyar matar dake zaune
kan kujerar dake kallon nasa fuskarta a daure ta kafa masa ido tana kallo, murmushi ya kuma yi mai sauti zaiyi magana ta rigasa a fusace tace "oh ga mahaukaciya na magana ko Shakur? yau ni ce ma na zama abun dariyar ka kenan"? ya ɗan marairaice ya ajiye fork din hannunsa yace "ba haka bane Mum! kiyi hakuri ki fahimce ni" ya faɗa yana ɗan shafa kwantacciyar sumarsa, da damuwa ya kuma faɗin "kinsan komai lkc ne Mum ki daina damun kanki just prayer Everything will be fine In sha Allah" kallonsa kawai take bbu ko ƙiftawa, shafa kansa ya kuma yi har lkcn fuskarsa na ɗauke da damuwa yana kallon Mum ɗin tasa, sallamar da aka yi yasa duk suka maida hankalinsu ga bakin ƙofa tare da amsa sallamar, miƙewa Mum tayi ganin su Ilham ta ƙarasa da fara'arta tana masu sannu da zuwa, suka Ƙaraso cikin falon aka shiga gaggaisawa, Shakur ya miƙe fuska ba walwala yana kallon Mum ɗin tasa still bai daina shafa kan nasa ba da ya riga da ya zame masa jiki yace "to sai na kuma dawowa ko zuwa gobe" tace "A'a ka dai dawo zuwa anjima da daddare bamu gama magana da kai ba" yayi murmushin sa mau ƙayatarwa yace "in sha Allah" bowl ɗin fruit Salad ɗin da ya ci ya ɗauka zai kai kitchen tace "A'a ka bar shi kawaI za'a kwashe" yace "No bari in kai Mum akwai abinda zan ɗauka ne" bata sake kula shi ba, ya nufi kitchen da bowl ɗin ya ajiye sannan ya fito yayi ma Freinds ɗin nata sallama ya fice daga falon yana kallon agogon hannun sa, gun motarsa ya nufa yana tafe
yana waigen bayansa har yayi ficewarsa. baki ta kuma taɓewa a karo na biyu tace "eh naji rantamin dubu biyun ai kema kinsan zan biyaki abinki Duduwa" "kin tabbatar"? tsaki taja ciki-ciki tana yarfa hannuwa tace "matsalata dake mayyar kuɗi ce ke! sam bakida tausayi Duduwa taya ina tare da marar lafiya a asibiti dubu biyun da zaki rantamin na riƙe a hannuna sbd kuɗin hannuna sunyi ƙasa amma sai wani ja min rai kike kinsan nafi ƙarfin wulaƙanci wllh dole ce ta kawo hakan amma ba komai ni ynzu rashin lafiyar ƴar uwata shine damuwata" Matar ta ɗan taɓe baki haɗe da jan tsaki ta zuge jakarta dake saƙale a wuyanta ta ciro naira dubu biyu ta zungura mata, itama da ƙarfi ta fizge kuɗin tayi waje tana ƙunƙuni, tafe take tana waigen abun hawa, ring ɗin wayarta ne ya dakatar da ita ta tsaya ta ciro ta a jakarta dake saƙale a kafaɗarta, no ɗin dake yawo a sreen ɗinta ne yasa ta jan tsaki taci gaba da tafiyarta cikin takunta mai jan hankali, fara ce siririya mai shekaru sha bakwai, sanye take da riga da skirt ɗin atamfa orange colour mai ratsin ash da brown, hijabin jikinta ma orange ne ya wuce gwiwa da kaɗan, haka ma takalmin ƙafarta orange
ne, jakar hannunta kadai ne brown, tafi minti goma tana  tsaye bakin titin tana jiran abun hawa, tsaki ta kuma ja tana taune gefen lips ɗinta cike da takaici. tayi nisa sosai a tunanin halin da ta baro Tween sister ɗinta a ciki, da kuma irin bahaguwar rayuwar da su ke yi, hannayenta rungume a ƙirjinta ta afka duniyar tunani ba tare da ta farga ba, fuu! motocin suka wuce ta gabanta bayan sun wanke mata jiki da ruɓaɓɓen ruwan kwatar dake kan titin, kallon jikinta take tun daga sama har ƙasa cikin tsananin takaici da zallar ɓacin rai, a hankali ta ɗago tabi bayan motocin da kallo tana huci *MODIBBO* ne rubuce ga baki ɗaya motocin biyar da suka wuce, lumshe idanu tayi wasu zafafan hawayen tsantsar takaici da ɓacin rai suka wanke mata fuska, gefen hijabinta tasa ta goge ta koma cikin gida ta canja kaya ta dawo bakin titin tana dakon jiran abun hawa, yana zaune saman motarsa ƙirar marcedez tazo ta fice ta gabansa sumi-sumi, duk abinda ya faru ɗazu akan idonsa, duk yadda yaso danne dariyarsa amma ya kasa, sai da tazo gab dashi ya fashe da dariya tamkar zai kifa, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta ba tare da ta tanka masa ba sbd inda sabo ta saba ko ficewa tazo yi ta layin sai ya tsokane ta itakam tana mamakinsa, bata taɓa tanka masa ba amma tana da cikinsa, ynzu ma taji haushin abinda yayi mata amma ynzu batada lkcn tanka masa amma tabbas in kere na yawo zabo na yawo wataran zasu haɗe, da ƙyar ta samu mai napep sai da su ka yi ciniki sannan ta shiga suka baro wajen. a harabar babban clinic tropical ya ajiyeta, ta sakko daga napep ɗin ta xuge zip ɗin jakarta ta sallamesa ta juya zata tafi kenan tamkar ance ta waiga taga motocin Modibbo da suka tozartata ɗazu, cikin rawar ciki ta ƙarasa tana ƙurawa sunan dake manne a bayan motar ido, jinjina kai tayi bayan ta tabbatar ta gyara tsayuwarta da kyau tana jiran fitowarsu. fitowarsa kenan daga Office ɗinsa riƙe da suit ɗinsa ya nufi ward ɗin patient ɗin nasa cikin takunsa mai ɗaukar hankali, hannu ya kai kan handle ɗin ɗakin zai shiga kenan ya tsinkayo su kusan biyar shine agaba escorts ɗinsa na take masa baya kusan su huɗu, yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda sky blue da hula kalar kayan sai baƙaƙen takalma da baƙin eyesglasess ɗin da manna a kyakkyawar farar fuskar tasa, cikin sakin fuska Shakur ya ƙarasa wajensu ya basa hannu suka gaisa, shima cikin sakin fuska ya amsa masa yana tambayarsa ya aiki yace Alhmdllh, Shakur da kansa yayi ma Modibbo jagora suka shiga zagaye ɗakunan marassa lafiya dan dama abinda ya kawosa kenan, ya kan zo duk weekend dan taimakawa marasa ƙarfi, turo ƙofar ɗakin su ka yi a hankali Shakur ne a gaba Modibbo a bayansa, marassa lafiyan suka shiga gaisawa dasu ɗaya bayan Modibbo na tambayar meke damunsu har suka iso gadon ƙarshe da yake gado huɗu ne a ɗakin. kwance take tayi lulluɓi da hijabinta tana rawar sanyi, kujera Modibbo yaja ya zauna yana kallonta, gyaran murya yace "ya jikin ki meke damunki" a hankali ta yaye hijabin jikinta ta miƙe zaune da ƙyar tana fuzgar numfashi, sai da ta ɗan dawo daidai cikin muryar marassa lafiya tace "Alhmdllh" zuba mata firgitattun idanunsa cikin tsananin tausayi kasancewarsa mutum mai mugun tausayi ya kuma fahimci yarinyar tana cikin zafin ciwo, fara ce tass siririya mai manyan idanu da dogon hanci amma gabaɗaya ta rame ta zabge kwarmin idonta ya faɗa ciki sosai, juyowa yayi su ka yi ido huɗu da Shakur dake tsaye kansu, Modibbo ya girgiza kai yace "Allah ya sawwaƙe and ina wacce kuke tare"? Fanan ta buɗe baki za ta yi mgn Shakur yace "ita da Tween sister ɗinta ne ta ɗan fita shisa, sauran maganar muje office mu ƙarasa zan maka bayani" Modibbo ya jinjina masa kai yabi wurin da kallo, bbu komai na ciye-ciye irin na marassa lafiya sai wani bushashshan koko dake ajiye gefenta cikin cup, ajiyar zuciya ya sauke yasa hannu cikin Aljihunsa ya ciro bandir ɗin ƴan dubu-dubu sabbi dal a ajiye saman ƙafafunta, da kallo tabi bayansa dashi lkc ɗaya hawaye suka zubo mata tace "ubangiji ya haskaka duniyarka da lahirarka" ta ƙarasa faɗa cikin raunin murya gamida kwantar da kanta jikin gadon tana share hawaye, juyowa yayi gabaɗayansa cike da jin daɗin addu'ar da tai masa har ya kasa ɓoye farincikinsa ya sakar mata murmushi snn ya fice daga ɗakin yabi bayan Shakur zuwa Office ɗinsa. "what! ciwon ƙoda fa kace Shakur ƙaramar yarinya irin wannan ce ke da ciwon ƙoda? ya Subhanallah" Modibbo ya faɗa yana cire hular kansa ya ajiye saman teburin yasa hannayansa duka biyu ya shafo kwantacciyar suman kansa, murmushin takaici Shakur ya saki yace "haba kai kuwa aikina ne fa ai ita cuta batada haka zata kama ko babba ko ƙarami bbu ruwansa, ni karan kaina tun zuwansa da na fahimci Ƙodarta ta lalace na shiga tashin hankali da damuwa kuma nake massifar tausayin su, abinda xai baka mamaki shine wllh tllh satinsu biyu a asibitin nan daidai da rana ɗaya ban taɓa ganin wani nasu yazo da sunan duba jikin Banan, Fanan itace ke kaikomo wajen kula da ƴar uwarta abun gwanin ban tausayi, sanda nake tambayarta iyayensu sai ce min tayi sun rasu, na dai ƙƴaleta ne kawai amma ban gamsu ba" ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya ɗauki hularsa ya sanya yace "to Allah ya kyauta but for now wane taimako ya kamata wllh a shirye nake da in taimaka mata" Shakur yace "kasan abu ne mai buƙatar shiri, ina jiran jikinta ya ɗan warware ne na basu sallama, cikin wayo da dabara zanyi ƙoƙarin gano gidansu har na samu ganawa da wani nata sbd ba zamu ɗauki yarinyar mutane muyi mata irin wannan aiki mai haɗarin gaske ba tare da sa hannun wani nata ba" sun jima sosai suna tattaunawa, Modibbo yace "to shikenan Allah ya taimaka yayi kyakkyawan jagoranci ni zan fice" Shakur ya rakosa har waje suna ɗan tattaunawa, Fanan tafi minti talatin tsaye cikin rana tana dakon jiran fitowar masu motocin, ko damuwa da halin da ta baro Banan a ciki ba tayi sbd tsabar massifar dake cinta, ta cika tayi fam ƙiris take jira ta fashe, tun daga nesa ta tsinkayo sun nufo motocin nasu, wannan karon Escorts ɗinsa ne agaba shi da Dr Shakur na baya alamun mgn suke, lkc ɗaya taja jinin jikinta sbd yadda yayi mata mugun kwarjini, ta haɗiye massifar tata tana yin ƙwafa, fuu ta baro wajen zata shige ciki, Shakur na hangota ya kalli Modibbo yace "yawwa kaga ƴar uwar tata" Modibbo ya ɗago ya ƙura ma Fanan ido lkc ɗaya gabansa ya yake ya faɗi, cikin basarwa yace "Ma sha Allah, Allah ya bata lfy" ya faɗa gamida miƙa masa hannu yayi masa sallama, sunzo zasu wuce ta gaban juna da gangan Fanan ta takesa da ƙarfin tsiya tayi gaba abinta.

Isn't free book it's #300 wattsap me for more information +22793474125

FORCED MARIAGEOù les histoires vivent. Découvrez maintenant