*FORCED MARRIAGE*
Free page 7-8
A hankali ya kwantar da kansa jikin motar idonsa a lumshe, zuciyarsa na masa wani irin zafi da raɗaɗi, a take ya fara jin nadamar zuwansa dan kuwa tunda uwarsa ta haifesa ba'a taɓa wulaƙantasa ba irin haka, har ynzu bai daina jin raɗaɗin marin da tai masa, lips ɗinsa ya taune da ƙarfin tsiya lkc ɗaya ya saki wani ƙayataccen murmushi, dole ma ya hukunta yarinyar nan ko ƴar gidan uban waye ita, ya buɗe murfin motar zai shiga kenan ya jiyo sallama a bayansa, ya juyo yana ƙare mata kallo, a nutse Banan ta gaishesa ya amsa yana ɓoye damuwarsa, tayi shiru can dai ta daure tace "nazo na baka haƙuri ne akan abinda ƴar uwata tayi maka, dan girman Allah kayi haƙuri ka yafe mata In sha Allahu bazata ƙara ba da kaina zan mata mgn" ƙayataccen murmushi ya sakar mata, nutsuwar yarinyar na mugun birgesa, tafi ƴar uwarta hankali da nutsuwa uwa uba ga haƙuri. "karki damu ba komai ya wuce" ta saki murmushi har dimple ɗinta suka lotsa tace "Thank u! Allah ya ƙara girma sai anjima" ta faɗi tana ƙoƙarin juyawa, yace "uhm minti biyu please" ta juyo da dara-daran idonta tana kallonsa yace "ya jikin naki hope da sauƙi dai ko"? ta Sakar masa murmushinta mai kyau tace "Alhmdllh naji sauƙi" yace "Ma sha Allah! ni dama abinda ya kawoni kenan fa sai tsautsayi ya haɗani da wnn marar kunyar Tween sister ɗinki" ta ƙyalƙyale da dariya har fararen haƙoranta suka fito, sosai ya shagala da kallonta yana sakin wani sanyayan murmushi wani irin daɗi na mamaye masa zuciya, can ta tsakaita da dariyan tace "kayi haƙuri haka halinta yake saurin fushi ne da ita amma bazata sake maka rashin kunya ba kaji" ta faɗa tana langwaɓar da kai, ya ɗan taɓe baki yace "ba komai fa ya wuce" tace "tou ngd sosai ni zan koma ciki" yace "wait please ɗan bani phone number ɗinki ma dinga gaisawa" tayi shiru kamar mai tunani can dai tasa hannu ta karɓi tanfatsetsiyar wayar da ya miƙo mata, ta saka mishi ta juya tayi tafiyarta, yabi bayanta da kallo sai da ta shiga gidan snn ya baro unguwar. Zaune ta samu Fanan sai girgiza ƙafa take, Banan ta dubeta da murmushi tace "taso mu wuce kar muyi letti" sai da ta zabga mata harara snn ta raɓa ta gefenta tayi gaba, Banan tabi bayanta jiki a sanyaye. Shamsu ne zaune saman motarsa, yau tun safe yake dakon jiran fitowarta dan tun jiya rabon da ya ganta balle ya tsokaneta, murmushi yayi sanda ya hangota tana Tahowa daga layin su Banan na bayanta, yadda ta ɗaure fuska da yanayin tafiyarta yasa ya gane ta, da ke ranan lahadi ne layin shiru bbu mutane, blue ɗin hijab ne a jikinsu har ƙasa, ya kafa mata ido har ta karaso titi ta tsaya daga gefen motarsa ta tsayar da abun hawa suka hau, tada motarsa yyi ya hau kan titin ya bi bayan napep ɗin da ta hau. Bai wani sha wahalan bin napep ɗin ba don bbu motoci sosai kan titin, Tafiyar minti kusan goma suka yi keken ya sha kwana shima ya bi bayansa, faka motar yayi ganin mai napep ɗin ya saukesu yayi tafiyarsa, su kuma suka doshi gate ɗin shiga makaranta, da sauri ya fito daga motar yaje yasha gabanta, Fanan da har yanzu fuskarta ba walwala ta ɗago tana kallon Shamsu, Banan dai tayi shigewarta ciki ganin Fanan taƙi kulata, Shamsu ya ɗaga mata gira ɗaya yace "ya garin ya jin daɗi"? yayi maganar yana shafa ɗan guntun gemunsa yana mata wani mayataccen kallo, takaici ya hanata mgn ta raɓa ta gefensa zata shige ciki ya fizgo hannunta da ƙarfi ta faɗo jikinsa, cikin wani irin matsanancin fushi wanda ita kanta batasan tana da shi ba! ta sauke masa wasu lafiyayyun marika hagu da dama tana nunasa da yatsa tace "zaren ba kalar yadin bane yaro! kaje ka nemi ƴan iska daidai kai ɗan iska fasiƙi ƙazamin banza da wofi, na rantse da Allah ko kallona ka sakeyi sai nayi ƙarar ka" ta faɗa cikin kausasa murya ta shigewarta cikin makarantar tana masa wani mugun kallo, ya shafa kumatunsa guda biyu yabar ƙofar makarantar da sauri ya shige mota yabar wajen da mugun gudu. Shamsu ne zaune ranar Sunday da freinds ɗinsa a gidan wani abokinsu Sameer, ya Kai ƙarshen lbrinsa yana murmushi ya ɗauki kwalban wine ɗin gabansa yana sha, duk suka yi tsit suna kallon sa kowa da mamaki bayyane a fuskarsa, miƙewa Sameer yayi yana taɓe baki yace "amma ka bada maza wllh, na sha surprise ɗinka, duk wannan ajin naka da Kyan ka da kuɗin ka da iliminka da wayewar ka mace ta mare ka ka ƙyaleta? u let her go scot free? Just like dat" murmushi kawai Shamsu yake yana ayyana muguntar da yake shiryawa a ransa, duk abokan nasa suka masa caa da surutu ko wannensu rai a ɓace" sai da ya bari suka yi shiru don Kansu snn yace "nima har kun ɓata min rai tunda kuka iya mance wanene Shamsu boy, an gaya maku Shamsu Zata Mara ta tafi scot free" Idriss ya miƙe yace "nonsense after she've disgraced u in public and u let her go, me kuma kake tunanin zaka mata da za ka burge mu?" Dariya duk freinds ɗinsa suka dinga yi, hakan ya sake tunzurasa ya ɗaga kai yana kallonsu yace "ai abinda zan mata sai ya sa tayi da ta sanin haifota da uwarta tayi a duniya, ni ina da reason ɗina na ƙyaleta a ranar sbd abun ya faru ne a gaban ɗalibai. Idriss ya bushe da dariya yana nunasa yace "ya wuce kace zaka yi rapin ɗinta ko kuma ka sa a zuba mata acid, ko a nakasata, kai dai
nasan baka kisa, dats d only thin u can do, nothing more then dat, kuma still baka burge mu ba wllh, yarinya ƴar talaka ta ɗaga hannu ta sharara maka mari anya tasan waye kai kuwa"? ya miƙe tsaye yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, ya saki wani murmushin mugunta yace "wllh tllh da kunsan abinda nake shiryawa yarinyar nan da wllh kun tausaya mata, dani take zance ai" yana kaiwa nan ya fice yana karkaɗa mukullin motarsa. Slowly Shakur yake tuƙa motar zuciyarsa fal tunanin abinda Modibbo yace Fanan tayi masa, shi kam ya gama yadda cewar yarinyar nata shafar Aljanu, a hanya ya tsaya yayi magrib snn ya iso gida zuciyarsa fal tunani,bbu kowa falonsu sai TV dake aiki, yana haurawa sama suka kusan cin karo da Safna, tayi baya da sauri ta bi gefensa zata wuce ya fizgota yace "me ya kawo ki gidan nan"? duk da ta tsorata amma bata nuna masa ba ta dake tace "wnn kuma naga ai ba matsalarka bace ya Shakur" matse ta yayi a bango tayi ƴar ƙara hakan yasa ya saketa da sauri ya buge mata baki sannan ya shige ɗakinsa gudun kar Mumy ta gansa, sai da ta tabbatar ya shige ɗakinsa ta ɗaga murya tace "Allah ya Isar min mugu kawai" tana kaiwa nan ta sauka ƙasa da sauri. Shakur ne kwance ɗakin mum ɗinsa da daddare, tana shafa kansa tace "dama ina son muyi wata magana ne shisa na kiraka, Shakur ya Miƙe zaune yana fuskantar Mum ɗinsa da kyau yace "ina ji" sai da ta gama abinda take sannan ta juya tana kallonsa tace "kan Safna ne Shakur, kai ma kanka kasan irin son da take maka ba sai na gaya maka ba dai ko, so ka daina yawan cin zalinta sbd bakada mata bayan Safna kuma nan bada jimawa ba" nan da nan ya Haɗe rai yana kallonta yace "so na kuma Mumy gsky ni inada wadda nakeso" ta ɗan hararesa sannan ta ci gaba da maganarta "ɗazu tazo ta same ni tana kuka tace ka dok..." Mikewa Shakur yayi ransa a ɓace yace "tace miki me Mumy? ni fa wllh bana sonta ina da wacce nakeso, so ni bata kai matsayin in so ta ba, me zanyi da macen da bata da aji kuma marar kunya" yana kai wa nan yace "sai da safe Mum" ya fice daga ɗakin Mumy ta bisa da kallo, Yana komawa ɗaki ya shiga Neman layinta ransa a ɓace amma duk bai samu ba, hakan ya kuma ɓata masa rai, kulle ɗakinsa yayi da makulli snn ya dauki makullin fridge dinsa ya bude ya Ciro ruwa masu sanyi ya zuba a cup ya shanye nan take yaji zuciyarsa ta ɗan masa sanyi, ya kashe bedside lamp ɗinsa ya tako gaban gadon ya zauna wayarsa riƙe a hannunsa yana gwada kiran wayar Fanan, tana kwance tayi zurfi sosai cikin tunani, Banan ta jima da yin bacci amma ita baccin yaƙi ɗaukarta sakamakon wani irin faɗuwar gaba da ta tsinci kanta a ciki tun safe, gabaɗaya batada wani sukuni haka ta wuni sukuku, Banan tayi mata tambayar duniya amma tace mata ba komai, ring ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta afka, ta ciro wayar a ƙarƙashin pillow tana duban sunan Dr Shakur dake yawo kan screen ɗin wayar, ɗaga kiran tayi ta kai kunnenta jiki a sanyaye, cikin wata kasalalliyar murya tayi masa sallama, sai da ya sauke ajiyar zuciya yace "wa'alaiki salam! na tashe ki kina bacci ko"? ta shafo gefen kumatunta tana taɓe baki tace "ba komai ban kwanta ba na daiyi mamakin kiranka ne a wnn daren" ya kwantar da kansa cike da shauƙi yace "haka kawai na tsinci kaina da son jin daddaɗar muryar nan taki da ya iya yima mutane rashin kunya" wani murmushi mai sauti ne ya suɓuce mata wanda ya sake fito da zallar kyawunta "hum naji kuma ngd, ya kake ya gida ya aiki"? yace "lfy lou ya mai jiki"? tace "to gode Allah gata nan tayi bacci, yace "Ma sha Allah, rabbi ya ƙara afuwa" ta amsa da "Ameen" shiru ne ya biyo baya, can dai Shakur ya sosa ƙeya yace "uhm Fanan in tambayeki mana" tace "ina jinka" tayi maganar tana gyara kwanciyarta "samarinki nawa"? ta gwalalo ido waje sosai sai kuma ta ƙƴalƙƴale da dariya sosai tace "wnn wace irin tambaya ce sai kace ɗan jarida? tou ni ban taɓa ma yin saurayi ba" cike da mamaki yace "kina nufin bbu wanda ya taɓa cewa yana sonki"? ta taɓe baki tace "Aa nice dai kawai bbu ruwana da kulasu" "sbd me?" taji jefo mata tambayar, a taƙaice tace "masa sbd duk yawancinsu ƴan iska ne" ya girgiza kai yana jinjina ƙuruciya irin nata yace "wnn ba hujja bace Fanan" ta sauke ajiyar zuciya tace "bazaka gane bane wllh ina da hujjata" "tou faɗamin meye hujjar"? Fanan ta gyara zama sosai ta labarta masa duk abinda yake mata har marin da tayi masa, a kiɗime yace "kika maresa why Fanan irin waƴan nan yaran fa basa jin kwaɓa meya kaiki ga aikata wnn aikin bakya tsoron abinda zai je ya dawo"? tayi masa shiru jikinta duk a sanyaye tuni zuciyarta tayi rauni hawaye ya wanke mata fuska, jin ta fara shashsheƙa ya rumtse idanu yana jin kukanta har a zuciyarsa, nan ya hau rarrashinta sai da ya tabbayar tayi shiru yace "ki kwanta kiyi bacci gobe da yamma zanzo gidanku muyi maganar" kai kawai ta gyaɗa masa su ka yi sallama._Gobe zan gama free page In sha Allah, na buɗe paid group na fara saka wanda su ka yi payment so a hanzarta a biya mu afka cikin lbrn FORCED MARRIAGE dan jin yadda zata kaya, wattsap me for more information 22793414725_
