*FORCED MARIAGE*
Free Page 3-4
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Modibbo ya faɗa yana rumtse ido sbd wata baƙar azaba dake ratsa ko ina na sassan jikinsa dan sosai ta danne masa ƙafa da tsinin takalminta, a guje Escorts ɗinsa su ka yo kan Fanan yayi saurin ɗaga masu hannu yana taune lips tare da bin bayanta da kallo, wani matsiyacin kallo tayi masu gamida jan wawan tsaki tayi gaba abinda, rai a ɓace Shakur ya daka mata tsawa yace "haba Fanan! ke bakya ganin abinda kikayi ne da bazaki tsaya ki basa hƙr"? cikin massifa tace "wllh bazan basa hƙr ba kasan irin tozarcin da sukayi min ɗazu a bakin titi ne? ruwan kwata fa suka watsa min a bainan nasi ko tsayawa basuyi ba wllh sunyi kaɗan na basu hƙr aikin banza kawai ka matsa ka bani hanya Malam" ƙwafa kawai yayi ya ƙarasa inda Modibbo ke tsaye yana bin Fanan da kallo. "kayi hƙr dan Allah yarinyar nan tana da shafar Aljanu ne dan Allah kayi hƙr" jinjina kai kawai yayi ya sake basa hannu ya nufi motocinsa Escorts ɗinsa na zagaye dashi, da kallo Shakur ya bisa dashi yana addu'ar Allah yasa kar ya ɗau mataki kan Fanan sbd shi yasan wanene Ahmad Junaid Modibbo, da Fanan tasan waye yana da tabbacin da bazatayi wannan gangancin da tayi ba, but zai sameta yaja mata kunne ya gaya mata wayeshi tayi gaggawar kama kanta dan kuwa rijiya ba wajen wasan yara bane. da wannan tunanin yaja ƙafa ya koma ciki dan akwai patients sosai da zai duba da Theater da suke shirin yi nan zuwa yamma. a hankali ta turo ƙofar ɗakin tana ɓata rai, Banan ta ɗago da sauri ganin Fanan yasa ta miƙe zaune da ƙƴar tana murmushi, da ƴar yaƙe a fuskarta ta ƙaraso ta haye gadon tana cire hijabin jikinta tace "I'm sorry sweetheart na daɗe ko? wllh da ƙyar na samu Duduwa ta bani rancen dubu biyu shima sai da ta gama wulaƙantani son ranta tukun" shiru tayi ganin Banan ta miƙo mata damin kuɗi ɗaure sabbi dal dasu, manyan idanunta ta gwalalo sosai gamida dafa ƙirji tace "na shiga uku ni Hassana! ina kika samo wannan kuɗin"? tayi tambayar cikin tsoro, Banan ta girgiza kai tayi kwanciyarta tace "wani bawan Allah ne yazo duba mutanen ɗakinmu shine ya raba mana" Fanan ta ɗaga kai sama tamkar mai tunani can tace "tare suka shigo da Dr Shakur"? Banan tayi saurin gyaɗa mata kai tana murmushi tace "ƙwarai ɗazun nan suka fita tare" ta kwaɓe baki tace "to ki riƙe" "Aa Sweetheart ke zaki riƙe kije ki biya bashin da ake binmu ki biya Duduwa kuɗinta sannan ki siya mana kayan abincin da za mu yi amfani dasu" kwanciyarta tayi gefen Banan tayi ɗaiɗai sanyi Ac na kaɗata, har Banan ta fidda rai da samun amsa taji tace "tou gaskiya ba yanzu ba sai na zuwa yamma dan bansan ubanme zan tsinta a gidan sai dai in kwashi kayan takaici da zallar baƙinciki" Banan tayi murmushi tace "aikam kina ma ƙoƙari Allah ya kaimu yamman lfy" ta amsa da "Ameen" duk su ka yi shiru kowanne na saƙe-saƙe a zuciyarsa. sai yamma liƙis Fanan ta koma gida, tun sanda ta sauko a napep ɗin ta doshi ƙofar shiga gidan ta soma jiyo hayaniya na tashi, sai da taja tsaki sannan ta tura ƙofar ta shiga da sallama duk da dai tasan ba jiyota zasuyi ba, Hawwa da ƙaninta Sani ne ke ta dambatuwa bbu ji bbu gani, Duduwa na tsaye a tsakiyarsu da ɗaurin ƙirji sai ƙoƙarin rabasu take, Hawwa ta hankaɗata gefe tayi kan itacen Iya dake ci balbal da wuta tana tuƙa tuwo ta zaro ɗaya tayi kan Sani zata maka masa, da gudu yayi hanyar waje bayan ya gama zaginta tass kamar haifaffan bakin tasha, daidai lkcn Fanan ta shigo gidan tana ganin abinda ke faruwa tayi baya da gudu dan ceton kanta, tana ganin tabi bayansa da gudu har sun fice daga layin ta sauke ajiyar zuciya ta dawo gidan cike da takaici, Zainab ce ta fito a guje su ka ci karo da Fanan tayi mata wata bangaza tamkar zata yada ita ƙasa tayi gaba abinta ko saurararta bata yi ba, Da sauri ta jawo hannunta cikin ƙunar rai ta ɗaga hannu ta zabga Mata Marika hagu da dama tace "dan Uwarki ni sa'arki ce da zaki bangaje ni ki wuce ko kallo ban isheki ba ko kinga ina shiga sabgarku ne a gidan nan ne"? Kuka Zainab ta fashe dashi tayi cikin gida da gudu tana faɗin "Allah ya isa ban yafe maki ba shegiya tsinananniya karuwa kawai" Wani ɓacin rai ne ya dirar mata tayi cikin gidan A fusace tana ayyana yadda zataci uban Zainab a gidan yau dan ita ba Banan bace bazata ɗauki irin wannan cin zarafin ba, Duduwa na zaune saman kujera ƴar tsugunno tana sharen hawaye da gefen zaninta dan sosai ta bugu sakamakon hankaɗawar da Hawwa tayi mata bana wasa bane, kukan da Zainab ta shigo dashi yasa ta miƙewa a zabure tana gyra zaman zanin jikinta tace "lafiyar ki kuwa"? cikin gunjin kuka tace "waccan tsinanniyar ce ta mareni hagu da dama ina jin ma idona ɗaya ya fashe" ta faɗi tana rumtse ido ɗaya cikin sharri, Cikin Sababi da tashin Hankali Duduwa ta Miƙe tana gyara ɗaurin zanin ta tace "Lallai Yau za'ayi kambu a gidan nan Wllh tllh bazan yadda wata ƴar iska ta riƙa dokarmin "ƴaƴa dan kawai ina zaune a gidan nan, bara ta shigo inji meye dalilin dukanki da tayi dan uwar data haifi uwart...kafin ta ƙarasa Fanan ta yiwa tsakar gidan dirar mikiya tana huci, tun daga nesa ta cire hijab da takalmi da jakarta, ta tattare sket ɗinta yayi sama tayi kan Zainab gadan-gadan ba tare da ta kula Duduwa dake ta surfa massifa ba. cafko Zainab Fanan tayi ta wurgata gefe gamida shaƙe mata wiya ga jikin bango, cikin muryar ɓacin rai tace "wa kike kira da karuwa? dan uwarki sa'arkice ni"? ta faɗi tana kai mata naushi a baki, duk yadda Duduwa ke ƙoƙarin ƙwace Zainab a hannun Fanan amma ta kasa, Iya dai na zaune kollon inda suke ba ta yi balle tayi rabon faɗa, a haka Hawwa ta shigo ta samesu, tana ganin yadda Fanan ke dukan Zainab ta siye faɗan rigimar ta dawo tsakaninsu suka fara dambatuwa har suka iso bakin rijiya, Zainab da Duduwa suka fara ɗaukan Abubuwa suka dukan Fanan dasu suna zaginta ta uwa ta uba suna mata mugun fata ganin tayi nasarar kada Hawwa a ƙasa, ganin abun bana masu hankali bane Iya tazo ta fara rabasu tana riƙe Fanan amma sam taƙi sauraronta, haka faɗanta yake baya mutuwa ga kuma wawiyar zuciya kamar dangin kutare, da ƙyar Iya tayi nasarar rabasu tana massifa, bayan komai ya lafa ganin Sani ya shigo gidan da gudu Fanan tayi kan jakarta ta ɗauka sbd tasan halinsa, ta zuge zip ɗin jakarta ta ciro dubu biyu ta cillawa Duduwa tayi ɗakinsu ta buɗe ta shiga, kan yaloluwar katifar su ta zube ta fashe da wani matsanancin kuka mai taɓa zuciya. taci kuka harta gode Allah har hakan ya haifar mata da ciwon kai daga nan nauyayyan bacci ya ɗauketa, sai bayan isha ta farka ta miƙe a razane ta fito tsakar gida, ruwa taja a rijiya ta shiga wanka sai data ɗauro arlawala ta dawo ɗakin tayi sallar magariba da isha, a gaggauce ta shirya cikin doguwar rigar atamfa da hijab har ƙasa ta kullo ƙofar ɗakinsu tayi ficewarta ba tare da tama kowa na gidan mgn, tafe take tana addu'ar Allah yasa ta samu abun hawa harta fice daga layinsu ta iso bakin titi, tafi minti goma tsaye snn ta samu abun hawa. tana turo ƙofar ɗakin taga Banan zaune tana cin kayan fruits, cike da mamaki ta samu wuri ta zauna ganin ledojin cake away da kayan fruits kala-kala ajiye a gefe. "ina kika samo wnn kuma" Banan ta ɗan ɓata fuska tace "wasu ne suka kawo sukace inji wnn mutumin na ɗazu da safe" Fanan tayi kicin-kicin da fuska tana salati tace "sai kika karɓa ko dayake bakida wayo haka kawai bakisan mutum ba bakisan zuciyarsa a kanmu ba haka ya ɗauki zunzurutun kuɗi ɗazu da safe ya baki ynzu kuma ya kawo maki wnn abun tou meyake nufi kenan" Banan ta kwantar da kanta cikin gajiyawa tace "don Allah ki cire duk wani mugun tunani a ranki ki tsarkake zuciyarki Sweetheart, wnn mutumin yana da kirki sosai taimako kawai yak..." bata ƙarasa ba Fanan ta katseta a tsawace tace "yana da kirkin ne yau da safe ya tozartani a tsakiyar titi su ka yi tafiyarsu suka barni? bama buƙatar wani taimakonsa ya taimaka ya rufa mana asiri ya fita a rayuwarmu muji da abinda ke gabanmu" yadda ta haƙiƙance tana surfa mata bala'i kai kace ɗiyarta ce, sai tayi mata shiru bata sake ce mata uffan ba.*PLATEAU* Unguwa ce mai ɗauke da ƙarancin mutane da suke rayuwa a cikinta a silent place sbd bata cika hayaniyar mutane sai tarin sanyin ni'ima mai daɗi sakamakon kusancin su da ruwan take, unguwace mai dake ɗauke da manyan ma'aikata da ƙusoshin gwamnati da kuma manya-manya masu kuɗi ga kuma tarin ƴan yahoo boy'z domin duk yawancin su sunfi sha'awar zaman unguwar, rayuwar su gwanin ban sha'awa bbu ruwan wani da wani suna rayuwa ne tamkar a ƙasar waje. *PLATEAU ROWS FAMILY ESTATE* Estate ne mai ɗauke da tarin dangi a cikinta, haɗin kai mai tattare da zaman lfy, sam bbu hayaniya a cikin wnn Family kasancewarsu wayayyun ƴan boko, ga tsantsar haɗin kai da fahimtar junan su, kyawawan Family masu matuƙar ƙaunar junan su, Alhj Usman Modibbo Yaƙasai, haifaffan ɗan garin Niger ne amma asalinsa fulanin saiy ne, sanannan mai kuɗi ne yayi tashe tun a lkcn da duniya ke kwance snn kuma take zaune lfy, Marigayi Alhj Usman Modibbo yaƙasai babban ɗan siyasa ne daya taka rawar gani a ƙasar Niger, ya riƙe muƙamai dadama a wnn lkcn, ya rasu yabar tarin dukiya da ƴaƴansa uku, gabaɗaya Familyn Alhj Usman Modibbo Yaƙasai bbu talaka a ciki domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu, tun kafin rasuwarsa ya gida wnn katafaren Estate ɗin ya tattare kan ƙannensa da yayyansa kowa na zaune da iyalinsa, matansa biyu, Hjy Jamila itace matarsa Babba wacce akayi masu aure tun saurayi da budurwa sai, sai dai Allah bai bata haihuwa ba harya auro wata bafulata Mai suna Baɗɗo, ita ce ta haifa masa yara uku mata biyu namiji ɗaya, Ahmad Junaid shine Babba sai Surayya sai Auta Ramlat, yana da ƙaninsa wanda suke kira da Baba Giɗaɗo wanda ya maye musu gurbin mahaifinsu kasancewar shi kaɗai suke uwa ɗaya uba ɗaya da Alhj Usaman duk sauran mazaunan cikin Estate ɗin ƴan uwansa ne dai na kusa amma da Baba Giɗaɗo ne kaɗai suka fito ciki ɗaya, bayan rasuwar Alhj Usaman Modibbo da wata huɗu uwar gidansa Hjy Jamila ma tabi bayansa mutuwar da ta girgiza kowa, bayan wasu ƴan lokuta Ƙaninsa Baba Giɗaɗo ya buƙaci auren Baɗɗo tsohuwar matar marigayi wato yayansa amma sam taƙi yarda, duk da shima yana da mata sai dai Allah bai basu haihuwa ba, bai takura mata ba, akwai wani kamfen da suka taɓa zuwa a can ƙauyensu nan ya haɗu da ƴar uwarsa da ta taɓa aure acan wani ƙauyen dake kusan su, ƙaddarar rayuwa ya rabasu da mijin ta dawo garinsu da zama, lkc ɗaya yaji Amina ta kwanta masa kasancewarta kyakkyawa uwa uba hankali da nutsuwa, a farko taso masa gardama sbd har ynzu tana ƙaunar mijinta ga kuma ƴaƴanta da ta baro a ƙuncin rayuwa, da ƙyar aka shawo kanta shima sai da aka sako manya a maganar ta amince badan ranta naso ba. Amina mace ce mai kirki da sanin yakamata shisa tasu tazo ɗaya da Baɗɗo wacce suke kira da Fulani, Mama Fulani ta koyar da Amina abubuwa dadama irin nasu na matan birni tun tana jin kunyarta har ta dawo ta saki jiki da ita tana mata kallon yayar da suka fito ciki ɗaya, cikin ikon Allah da hikimarsa shekara ɗaya da aurensu da Baba Giɗaɗo ta haifi ƴan biyu mace da namiji, Bilal da Basma, kyawawan yara masu shiga rai wanda Mama Fulani ta ɗauki so da ƙauna ta ɗora musu, wasa-wasa har riƙon Basma ya dawo hannun Mama Fulani, duk Amina ta samu wasu ƴaƴan amma har gobe bata daina tunanin ƴaƴan data bari acan wajen tsohon miji, sau dayawa ta kanyi kuka sosai Baba Giɗaɗo da Mama Fulani ne ke ƙoƙarin kwantar mata da hankali, su Tweens sun girma shekarunsu sha biyar yayinda Ramlat ke da sha bakwai Aunty Surayya kuwa tayi aure harda ƴarta, Ahmad Junaid shine ya gaji mahaifinsa wajen tausayin na ƙasa dashi inda shima ya tsunduma a harkar siyasa yake neman takarar kujerar gouverno da taimakon Baba Giɗaɗo da sauran Uncle's nasa na cikin Estate ɗin. haka wnn Family suke rayuwarsu cikin tsananin so da ƙaunar junansu, anan cikin dangi wasu mazan suka zaɓi matan aure cikin zuƙa-zuƙan ƴan matan Estate ɗin, akayi bikinsu suma suke zaune cikin Estate ɗin sbd wnn shine Al'adar su, bbu abinda bbu a cikin wnn estate ɗin kama daga makarantar Islamiyya, wajen wasan buga ƙwallo, wajajen exercice,wajen awimming pool,libarary snn ga wani katafaran holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan ƙyale-ƙyale yana zagaye da kujerun zama, an gina shi ne sbd taron sada zumunci wanda sukeyi a duk ƙarshen wata, duk sa'annin Ahmad sunyi aure a lkcn amma banda shi harkar Siyasa kawai yasa a gaba, ganin haka Uncle's nasa suka sakasa a gaba har aka haɗasa da wata cousine ɗinsa Amal wadda itama suke zaune da iyayanta a cikin Estate ɗin, bbu wani so ko shaƙuwa a tsakaninsu, a haka dai Amal take haƙurin zama dashi kasancewarta wayayyar mace, tun tana haƙuri da halinsa har itama ta sharesa suke zaman doya da manja, wnn dalilin yasa wata ɗaya takk matsaloli suka yiwa rayuwar aurensu ɗaurin goro, Amal ta kasance mace mai son jiki da ragwanci ƴar gayu ce sosai kuma tana da kyau amma fa sangartacciya ce sam batajin kwaɓa sbd ta taso cikin gata da tarairayar uwa da uba kasancewar ita kaɗai iyayan ta suka haifa, shisa suka samu banbancin Ra'ayi da Modibbo, duk da irin tarin dukiyar da suke da shi sam! bayason abincin ƴan aiki, shi a tsarin rayuwarsa ma bayason wasu maids amma sbd ragwancin Amal yasa ya zuba ma'aikata a part ɗinta su sukeyin komai na ɓangaren harda girki shiyasa kullum sai yaci abinci a part ɗin Mama Fulani yake shigowa.
#Back to story, ƴar uwa karki bari ayi wnn tafiyar bbu ke! salon na daban ne.👌🏻snn kuyi share sbd Allah da manzonsa
isn't free book it's #300 via wattsap me for more information +22793414725