Bayan Baba ya sauke wayar ya kalli Inna cikin yanayin damuwa yace.
“Bashiru ne yake mana maganar komawar mu can”
Inna ta girgiza kai.
“Babu inda zanje, ba a tserewa mutuwa a ko'ina take”
“Na san da haka amman dai ya kamata mu bar garin nan saboda ance akwai yiyuwar su dawo, kuma kina gani kullum mutane barin garin nan suke”
“Babu inda zanje Malam, na fi son mutuwata ta same ni a inda nake”
“Ai kaji matsalarki kenan, shi kansa abun da yake ta magana kenan a lallaba masa ke”
Inna bata sake cewa komai ba, har Baba ya ci ya shude. Duk abun da suke Aminatu na dama furar tana saurarensu, bayan ta gama ta kawo ma Inna ta zauna kusa da ita ta fara bata a hankali tana sha, Inna bata hana Aminatu shayar da ita ba, duk kuwa da kasancewar zata iya sha da kanta. Sai da ta tabbatar ta koshi sannan ta rufe furar ta koma gurin girkin da take. Har ta girka ta gama bata cikin walwala da sakewar zuciya, ba na rashin yan'uwa ba, na tunanin kalaman da Inna tai mata? Ta ya zata rayu babu Inna? A hannu waye zata zauna ma? Ba ita kadai ba Baba ma ya zai ji idan suka wayi gari babu Inna? Ko da ace tana da aure rayuwa ba zata taba mata dadi babu uwa ba, balle kuma a yanzu da take tare da ita, Saurayinta Maniru ma yana cikin mutanen da yan bindigar suka kashe, bayan ta gama ta zubawa Baba nasa ta zubawa Isah a inda ake saka masa sannan ta kwashe sauran a Samira babba, ta debi ruwa ta shiga bandaki. Sai da ta cire komai na jikinta sannan ta zauna saman dutsen da suke zama idan zasu yi wanka ta fashe da kuka.
Kuka tai sosai sannan tai wanka ta fito idonta a kumbure, ta dora alwala ta shiga dakinsu tai sallah, bayan ta gama ta d hannayenta sama tana rokon Allah.“Ba ni da gata sai naka Allah, ka dauke yan'uwana a lokacin da ka so, ka sauya rayuwata zuwa yadda ka kaddara min, Allah ka yafe min ka jikan yan'uwana, ka ba mahaifiyata lafiya ka bar ni da ita Allah”
Ta karasa hawaye na sauko mata, sannan ta shafa addu'ar ta mike tsaye, ta fito waje, sai da ta zuba ma Inna ruwa a buta sannan ta rika ta, ta kaita bandaki bayan ta fito ta taimaka mata tai alwala sannan ta shimfida mata abun sallah.
“Allah ya miki albarka Auta”
Inna ta fada tana kokarin gyara zamanta, domin a zaune take sallah a yanzu. Aminatu ta kalleta kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta amsa.
“Ameen”
Ta mike tsaye.
“Bari naje na yi itace yamma ta yi”
Kai kawai Inna ta daga mata, ita kuma ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka ta ta dauki zaren da take daure itacen idan ta yi, sannan ta saka talkaminta ta fice, ba ita kadai ba kusan duk yan matan garin da ma matan aure suna zuwa daji ne su yi kara da yamma saboda dafa abinci, abu ne mai wahala ka ga gidan da ake siyen itace a yanki, yawanci duk a daji suke yin kara.
A da ta saba idan zata tafi yin kara akan biyo mata ko kuma ita ta biyawa wasu, sai dai tun bayan da aka tarwatsa rabin garin take tafiya ita kadai, saboda an tafi da wasu yan mata, wasu kuma sun yi gudun hijira, sauran da suka rage kadan ne. A gurin da ta saba tsayawa ta tsaya ta shimfida zanen sannan ta aje zaren a gefe, kana ta shiga tsintar karan, tana yi tana tuna yadda suke yi a da, ita da kawayenta, har tigengen suke cikin nishadi da walwala, sabanin yanzu da suka bar ta da kewa.
Sai da tai rabin sannan ta samu kanta da mugun faduwar gaba, marar misaltuwa, a take ta nade wanda ta tara a daure ta dauka ta nufo gida da gudunta, kowa sai kallonta yake, kamin ta iso har hawaye ya fara sauko mata, bakin kofa ta jefar da karan ta rugo da gudun gurin Inna da ke kwance tana bachi ta taba ta.“Inna...Inna.... Inn”
Bata karasa ba, Inna ta bude idonta da sauri tana kallonta.
“Lafiya Auta?”
YOU ARE READING
BAKAR WASIKA
Mystery / ThrillerTabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? Yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe n...