08

1.1K 74 26
                                    

"Mutuwata zata fi min sauki fiye da aikata abun da kuka bukace ni da shi"

Abun da ya fito daga bakin Baba kenan. Wanda hakan ya saka Aminatu bude idonta duk kuwa da kasancewar bata da tabbacin idan ta bude idon zata ga mutane, domin kamin ta rufe idon haske ne kawai take iya gani.
Sai dai kallon be kare mata ma, domin ta yi arba da fuskar mahaifinta da suka haske da katuwar fitila mai haske.

"Kai ba shi giďa"

Idan suka ce aba wa mutum giďa yana nufin a halbe ka, take dayan ya daga bingida da zimmar harbin Baba sai bindigar ta ki tashi. Dayan ya sake daga ma ita ma taki tashi.

"Kaga wani tsohon shige... Sa mai wuka"

Dayan ya fada yana buga masa kan bindigar. Sai biyu suka kama shi suka kwantar da shi, dayan ya saka zabgegiyar wukarsa ya fara gagarawa a wuyan Baba, nan ma wukar bata kama ba.

"Shege, samo dutse yau ba maganin karhe ba ko maganin mutuwa ka kasha sai mun kashe ka"

Ban da kallon Baba babu abun da Aminatu take, ta kasa kuka hawayenta sun kafe, kamar yadda zuciyarta ta wanke tass, kwakwalwarta kuma ta zama fanko babu tunanin komai a ciki. Bata iya jin komai sai kalmar shahadar da Baba ke yi, duk yadda ta so ta kawar da kanta daga kallon yadda suke fasa kan Baba da katon dutse sai ta kasa ko da kwakkwaran motsi. Wani irin sanyi ne marar misaltuwa ya taso mata ya baibaye ilahirin jikinta, sai ta soma jin abu na mata yawo a cikin kai kamar hatsi.

"Baba..."

Ta furta daker tana kallon yadda suka rabe masa kai biyu a cikin dakin mahaifiyarta da suka harbe bayan sun kashe Ya Isah.

"Tashi ki saka tufafinki"

Dayan ya fada, sai ta kalleshi, duk da kasancewar hasken fitilar ba ya iya bari ya ta ga fuskokinsu, ba kuma dan ta fahimci abun da yake fada mata ba, sai dan hasketa da yai da fitila da yai, kana kallon kwayar idonta ka san bata cikin hayyacinta. Dayan ya kai mata mugun shuri a cinyarta.

"Saka tufafinki dan ubanki"

Maimakon ta saka tufafin sai ta juyarda fuskarta ta kalli inda ya shuri ta, ta kai hannu ta taba.

"Baba...."

Ta furta domin har yanzu tana jin sautin kalmar shahadar da yake a kunnenta, dayan ya fisgota sai ta mike tsaye sam ta manta a sirara take, yau ga ranar da bata kunyar siraicinta, ranar da dimauta da bakinciki suka saka ta manta babu sutura a jikinki.

"Wuce mu tafi"

Ta kalli inda mai maganar yake tana jin kamar ta taba jin kalmar. Tasss ya wanke mata fuska da wani irin mari mai zafi, sai ta rikice ta fara kuka.

"Inna.... Baba.... Wayyo Baba.... "

"Saka tufafinki"

Ras ta ji abun da ya fada, kuma ta fahimce shi, hakan yasa tai saurin nufar inda tufafin suke ta dauka, sai dai a maimakon ta saka sai ta rike tufafin tana ganin komai kamar a mafarki. Dayan cikinsu ne ya fisgota ya turo keyarta waje, sai ta samu kanta da bin bayan wadanda suke gabanta, abun da bata sani ba ashe a sauran gidajen nan ma sun fito da sauran matan da suka rage, tafiya kawai take tana jin kamar ba kasa take takawa ba, hade ta sukai da sauran matan dake ta rawar jikin tsoro, domin sun kasu kashi kashi ne, suna shiga gidaje. Kamar wandanda suka fito yakin duniya, haka kowa ganinsu, karyar mutun yace ga iyakarsu sai dai ya kiyasta a kiyasinsa ya fadi iya abun da idonsa ya gane masa, babura ne ko wane da goyon mutum uku dauke da makamai, wasu kuma mutum biyu ne a kai, wasu kuma a kafa sun saka manyan samarin maza a gaba dauke da hatsin da suka kwasa.
Ba Aminatu ce kadai mace da suka tafi da ita ba, sai dai Aminatu ita kadai ce tsirara a cikin matan da suka kora zuwa daji, kamar sun kora dabbobi haka suka saka matan a gaba, wasu kuma suna daga gefe duk wanda yai kokarin guduwa daga cikin matan sai a halbeshi. Wasu mazan kuma suna bayan su Aminatu dauke da hatsin da suka dora musu, suna tafe suna dukan mazan a baya. Tafiya suke ta yi Aminatu na rumgume da tufafinta, bakinta kuma be daina furta Baba ba, da muryar da ita kadai zata iya ji, tana jin ta taka abu har ya huda fatarta ya shiga cikin kafarta, sai dai ko kadan tashin hankali be barta ta ji zafi ba, ko da ma ta ji bata isa ya tsaya cirewa ba, a cikin matan da suka tura gaba har da masu goyo, da kananan yan mata da matan auren, babu mai waiwaye balle ya taimaki wani, a cikin masu goyon wandanda yayansu suka fi takura musu da kuka sai su fige yaran su jefar, tsofafin da suka fara gazawa kuma sai su halbe su, masu sauran jini a jika kuma suna tafe suna dukansu. Zalincin da mutanen nan suke sai ka rantse da Allah ba zuciyar dan'adam ce a jikinsu ba. Ba su san wani abu tausayi ba, ba su ragowa ba, ba su san rai yana da muhimmancin ba, ba su wani abu imani ba, ba su san ragowa ba. Tun cikin dare suke tafiya a kafa suna ratsa wani irin jeji da Aminatu bata taba mafarkin gani ba, ba su isa inda za su je ba sai da hasken asuba ya fara ketowa.
Ba ita kadai ba mata da yawa idan ka duba kafafuwansa zaka tarar sun kumbura, saboda babu mai talkami a kafarsa, kuma da yawa sun taka kaya wasu kuma ice ya shiga kafar amman ba damar cirewa, sai dai kai ta taka kafar a haka.

BAKAR WASIKAWhere stories live. Discover now