Borno Empire,
Borno state, Nigeria"Lalle barkanku da zuwa." Jakadiya ta fadi da Murmushi a fuskan ta. Ta jagoranche su zuwa inda aka shimfida carpet mai laushi da ottomans da aka jera.
Yarima da mutanen shi suka hau kai suka zauna ayayinda masu aiki suka rin'ka ajiye kwanukan abin ta'ba wa kala kala.
Jakadiya ta tafi don ta isar ma da Gimbiya zuwan ba'kon.
•••
Azumi ta ma'kala ma Gimbiya Zarah sar'ka amma Zarah ta Lura tana so tafadi wani Abu. Zarah ta ga yanda bakin Azumi ke bude wa kamar dai za ta che wani abu sai kuma ta Rufe.
"Azumi me kike so ki che?" Zarah ta tambaya tana kallon ta ta mirror din da ke gabanta.
Azumi ta sauke lumfashi sannan ta Kalli Zarah ta mirror din, "Zarah ni fa ina ganin gwara ki aminche da wannan. Ba wai kasalandan nake miki a lamuran ba amma you should look into this. Kullum sede kiyi ta watsa wa mahaifiyarki kasa a ido." Ta yi shuru tana tsoran me Zarah za ta che
"Saboda bana aminchewa shi ne ya zama chin fuska?" Ta Kalli Azumi kafin ta chigaba, "Wannan fa akan rayuwata ne na har abada. Making a rash decision would only cheat me. Ni dai soyyaya ta gaskiya nake bukata ba wai kudi ko mulki ba. To Amma ni agani na duk mazan Yanzu ba haka suke ba. Suna kaunar su mallaki mache da kudi ko dukiya Dan duk a tunaninsu mata suna da san ku'di..."
Zarah bata Gama maganarta ba Jakadiya ta 'kwan'kwasa kofa. Azumi che ta juya da sauri ta je ta bude kofar.
"Allah ya taimaki Gimbiya ba'kin ki sun karaso."
Zarah ta tashi daga gaban vanity table din sannan ta girgiza kananta alamar toh.
Jakadiya ta yi Murmushi ta juya ta futa.
Zarah che ta saukar da numfashi kafin ta Kalli Azumi. Ta Dora Alkyabban ta kafin ta fita Azumi kuma ta bita a baya
•••
Sallama ahankali tayi kafin ta hau carpet din ta zauna daga Chan karshe. Azumi kuma ta tsaya daga bayan ta.
"Barkan ki da Zuwa, Gimbiya." Khalifa ya fadi da Murmushi
"Zarah nake." Zarah ta fadi batare da 'daure fuska ba kuma ba da Murmushi ba.
"Ni kuma sunana Khalifa." Ya juya ya Kalli mutumin dake bayanshi, "To wannan Mubarak ne shi ne personal gard di na. Duk inda kika ganni za ki ganshi. We've been together for like ten years now."
Zarah tayi gajeruwar dariya kafin itama ta nuna Azumi, "Kamar dai Azumi. Sede ita friend dina che ba maid ba." tayi murmushin gefen baki sannan itama Azumi ta maida mata da Murmushi
Ya 'dage jira 'daya tare da jinjina Kai, "I really love your rashin girman Kai."
"As you said." Zarah ta fadi
Khalifa se be tanka abin da tache ba sai ya fara magana. "Naji labarin kin sha Koran 'ya'yan sarakuna da dama wai ke ba Wanda ya miki. Anche baki da Raayin Maza to amma ni dai nazo gwada saa na ne." Yayi Murmushi kafin ya chigaba, "Duk da dai ni daban ne da su. You can never reject me because I have that effect on ladies."
Zarah tayi dariya kafin ta 'daga gira 'daya, "Really?"
"Yup. Zaki ga yanda zan rusa katangar da kika gina ma kanki."
"We shall see. Inji bature." Zarah ta fadi da dariya.
•••
Kasanchewar dare ya riga yayi se aka share musu chamber din dake west wing din Masarautar. Aka bashi chamber shi da Mubarak suma sauran da aka zo dasu aka basu wani chambern. Khalifa yaji dadin haka sosai da kuma karramawa da akayi musu.
YOU ARE READING
NOT A PRINCE, BUT MINE
FantasyAna chikin haka, She invited The Emir of Sokoto's son. The prince of the Sokoto caliphate. Amma amai makon shi ya rusa katangar dana gina ma kaina, wani ne Chan nadaban ne ya rusa ta. Wani wanda babu wanda ya ta'ba tunanin zai iya. Dive into my Stor...