7.

5 1 0
                                    

~Duk nisan jifa kasa zata dawo

Nasan kun sani tunatarwa ne

















BORNO, NIGERIA

"Mama Yanzu me kike so nayi? Banda'de da tambayan Zarah kudi bah gaskiya bazan iya kara tambayan ta ba." Azumi ta jijjiga kanta chikin damuwa. "Kiche wa Baba yayi hakuri ya nemo chefanan wannan karan. Bazan iya ba Allah."

Maman ta ta banka mata wani harara, "Ni ina ruwana? Kawai abinda nasani shine ki bani kuɗi nayi chefane. Allah na tuba idan ba talauci da yama uban naki yawa ba, yaushe ma har zanzo ina tambyan ki kuɗi idan da yana bani."

Azumi tayi kaman zatayi kuka, "Amma mama ina kawowa fah. Kuma baba yana baki dai dai gwargwado. Kuma kinsan bana samun kuɗi sosai. Idan ma na samu ai ku nake kawo ma wa."

Maman ta ja tsaki,"Idan kika kara chewa baki da kuɗi sena fasa miki baki. Kina zaune a gidan sarki, Tare da sarauniya da gimbiya kuma kiche mun baki da kuɗi? Kina ruwa yarinya."

Azumi kuka ne Kawai bata fashe dashi ba saidai Kawai ta tashi ta yafa gyalen ta. "Ya Zanyi dole naje nayi bara tunda kin maida ni ma barachiya." Ta tashi daga kujerar tsugunne da take zaune a tsakar gida.

Ta tafi sumi sumi ta wuche ta fita.

~°~

Beebalo tana ta kalle kalle ta kan kame jakan ta a kirjin ta. Ta Daga kai taga dogon ginin.

"Muhhamad Yanzu kaine ka zama Sarki?" Ta Tambaya Mai Martaba. Yayi Murmushi a maimakon ya bata amsa, Se ya shiga cikin Fadar. Yayi mata Alama da kai da ta shigo.
Cikin tsoro da mamaki beebalo ta shigo Fadar nan take kuwa ta sake bakinta. Ashe ya shigo da ita Throne Room dinshi ne. The Royal Furniture, The Decorations, the setting, everything screamed Elegance and Executive. Daga Gani kasan ba Ƙaramin kuɗi aka zuba anan ba.

Wata baiwa ta fito daga wani kofa ta durkusa har kasa ta gaishe su. Beebalo har sai taji kunyan amsawa dan koda baiwa che, ta fita kyan gani. Sarkin ya fada mata wani abu wanda Beebalo bataji menene yache bah saboda ita hankalin ta baya wurin. Tana ta kallan abin Al Ajabi.

Bayan mintina kaɗan Wata Mata Me Alkyabba ta sauko daga stairs. Beebalo Kayan Gold din dake hannun ta ne ya dauke mata hankali. Mai Martaba ya Karasa inda matarshi Take yayi Murmushi.

"Shafaatu," Ya fadi. Shafaatu daman ita haushin shi takeji toh bata ma kalleshi ba. Ita dai tana ta kallon matar da ya shigo da ita.

"Ga Habiba. Beebalo."

For a moment Shafaatu thought she didn't hear Right. She thought Her husband spoke Tagalog or Gestuh, or Spanish, something like that.

Seda ta kara kallon matar da aka kira Beebalo taga dai Dagaske yake. Beebalo tayi baƙi ta lalache ita ko Shafaatu tayi Fari tayi kiba.

Tables Turn!

***

Azumi keta sauri ta riƙe jakarta kan kam wata mota tazo tasha gaban ta.
Idan ta seda ya kusa fitowa da taga waye a Motar, " Zarah." Ta fadi kafin ta buɗe kofar motar ta shiga seat din gaba.

"Where were you going to cikin sauri haka?" Zarah ta Tambaya tana kallon ta irin kallon da idan baka da gaskiya zaka yi tunanin an gane me kayi ne. Azumi ta hadiye miyau da kyar dan kusan bata da gaskiya.

"Naje gidan mama ne." Azumi Said refusing to have an eye contact with Zarah. Zarah tayi shiru na mintina tana mata kallon tuhuman da bata san dalilin yinshi ba.

NOT A PRINCE, BUT MINE Where stories live. Discover now