8.

7 2 0
                                    


~Nasara tana da iyaye dayawa amma faduwa, Faduwa bata da Uba

Inji Hausawa









"Me kike chewa neh?" Zarah ta tambaye matar da take tsaye tana hararar Mamanta.

"Zarah.." Matar ta fara fada idon ta ya chiko da kwalla. "My Baby." Ta fada ta matso kusa da Zarah da ta matsa baya.

"Wacece ke?" Zarah ta kara tambaya.

"Itache Mahaifiyar ki, Zarah. Ita ta haife ki." Zarah ta girgiza kanta bata so ta yarda. "Itace Asalin Mahaifiyar ki." Mai Martaba ya kalli Shafaatu yaga yanda idanuwanta suka chiko da kwalla. Abinda be taba gani ba a tsawon shekaru ashirin da suka wuce. Shafaatu ta fita daga 'Dakin da sauri duk suka bita da kallo harda Zarah.

"Baba dagaske ne?" Zarah ta tambaya. Mai Martaba kawai girgiza kai yayi kafin ya fita daga dakin. Zarah ta dawo da idanuwanta kan matar da aka kira da Mamanta.

"Zarah 'ya ta. Come to Maama." Beebalo ta fadi da kwalla a Cikin idanuwanta. Zarah bazata iya jurewa ba kawai ta fice daga dakin ta koma dakin ta. Dogarai da bayi suka yi ta gaishe da Zarah amma Zarah riƙe kanta kawai takeyi saboda kada ta fashe da kuka.

~°~

Sokoto caliphate
Sokoto, Nigeria

"Wallahi Khalifa I'm confused." Mubarak ya fadi yaja dogon numfashi. "Nayi tunanin Duniya na kasa gane waye ya ke bibiyan rayuwata har ya fara samun Zarah yanzu yana faɗa mata wai she should stay Away from me. Waye shi kuma me na mai?" Mubarak ya tambaye kanshi yayin da Khalifa ya shiga Cikin tunani.

"To Amma ka taba haduwa dashi ne?" Khalifa ya tambaye Mubarak.

Mubarak ya girgiza kanshi, "a'a. Amma ya turo min message har so Uku ta message gashi private number yake amfani da. Messages ɗin duka barazana akeyi min."

"Track the messages." Suna chikin maganar Nan Anas ya shigo katon falon su inda suke zama.

"Hello Guys!!!! Who missed me?" Anas ya fadi yana gyara babban rigar shi wanda akayi ma aiki irin ta masu sarauta. Dariya dukkansu sukayi kafin suka mai Maraba.

****

Borno caliphate,
Borno, Nigeria

"Shafaatu." Mai Martaba ya kira sunan ta yana matsawa inda take kaɗan kaɗan. Ta kura ma bangon dakin ta tana kallo chikin takaichi.
"Sweet Dina." Mai Martaba ya fadi da wata murya mai sanyi dan ya bata dariya. Amma Shafaatu bata juyo ba.
"Listen, I know I was wrong. Amma dole che tasani nayi hakan. Kin che sede na nemo mata wata Uwar kuma Shafaatu wallahi bany Dan na chuche ki ba. Dukda Zarah kema diyar ki che Amma Beebalo ita ta haife ta...." Be karasa maganar shi ba Shafaatu ta katse shi ta juyo ta kalle shi.

"Kada ka ƙara kiran Beebalo Maman Zarah! Mai Martaba Ni na reni Zarah da hannu na. Ni na riƙe ta tun bata banban ta fari daga baƙi. A baya na na goye ta, Mai Martaba. Amma Lokaci daya, Lokaci daya zata dawo Tache min tana da iko akan Zarah..." Lebben ta rawa ya fara bata karasa abinda take faɗa ba ta fashe da kuka. Kuka irin na takaici.

Mai Martaba ya janyo ta zuwa jikin shi kuma batayi musu ba. "Nasani, Shafaatu. Amma wannan saboda 'yata ne.. saboda yarmu."

Shafaatu ta dakatar da kukan ta ta daga ido ta kalli Mai martaba. "Yanzu saboda Nache ba sa hannu na a bikin Zarah shiyasa zaka yi min haka? Ban taɓa haihuwa ba Mai martaba Allah ya san yanda nike son Zarah..."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 17, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NOT A PRINCE, BUT MINE Where stories live. Discover now