01

111 6 2
                                    

*Tyiping📲📲*

🪐✨🪐
*_DARASI_*
🪐✨🪐

Na
*UMMU MAHER(MISS GREEN☘️💚*

Gaskiya wannan littafin tun kafin in fara rubutashi hannuna yake kaikayi,saboda littafine da zai tabo wani abu da yake faruwa acikin al'umma saboda talaucin da suke ciki sannan sai kiga iyaye suna jefa yayansu acikin mummunan hali,misali ko su kaisu aikatau,ko su kaisu Bara daga nan rayuwar yaran ta shiga cikin wani hali.

Tsokaci:ban yadda wani ko wata yayi amfani da wannan littafin ba wajen canza wani abu ba,wannan littafin mallaki na ne a kiyaye doka ce.



Bismillahir-Rahmanir_Rahim.

*_My parents_*

01

......."Wai ni indo me kika dauki kanki ne da ban isa in gaya miki magana kiji ba,kullum sai kin dorawa wannan yarinyar tallah saboda me zaki ringa kokarin keta duk wata doka da zan saka agidannan?".

"Mlm bafa ka isa ka hanani dorawa wannan yarinyar tallah ba tunda ba kaine kake daukar dawainiyar ta ba,matukar kanason in daina dora mata to kadinga kula da komai nata ciki harda ciyar damu dukkanmu",tana kaiwa nan tayi tafiyarta tana yan kunkuni da karfi.

Shiru Mlm yayi ya goge wata kwalla da ta zubo masa a Idanunsa.

Talla ne akan Fahima itama tana goge hawayen daya cika mata kurmin idanunta sannan ta shigo gidan,ta karaso inda mahaifinta yake ta ce"Baba don Allah kayi hakuri ka daina biyewa Amma saboda ranka zai dinga baci ni kuma banason abinda zai bata maka rai don Allah kayi hakuri".

shafa kan kyakkyawar yarinyar yayi sannan yace"Fahima Allah yayi miki albarka kinji,kema Allah yabaki masu yi miki biyayya kinji".

Cikin tausayin mahaifina na ce"Amin Baba".

Ina tafe ina waiwayen mahaifina da ya kasa fita har yanzu yana nan wajen dana barshi,haushin mahaifiyata ya kara ninkuwa acikin zuciyata,da wannan tunanin na karasa shiga cikin gidan.

"Ke!"

Da sauri na kalli Amma wacce ta kasance mahaifiyata sannan ta ce"Saboda kinyi tsiyar taki kin zubarmin da kudi shine ko sallama ba zakiyi min ba kawai sai ki shigo gida kina neman fadamin kan tukunyar girki ki jazamin siyan maganin da ban shirya ba".

Kallon mahaifiyata nayi wadda na mayar kamar tv tun shigowa cikin gidan,wato ita babu ruwanta da konewa ta ita kudinta ne ya dameta,Amma kenan ita babu ruwanta kudinta kawai ta saka a gabanta.

Jiki na a sanyaye na shige cikin dan rubabban dakinmu wanda kana ganin ginin gidan kasan tsohon ginin ne,runtse idanuna nayi na kalli silin din dakin ina tunanin rayuwar da mahaifana suke yi,kwatata Amma wato mahaifiyata bata mutunta mahaifina kullum cikin fada da gaya mishi bakaken maganganu kawai don bashi da kudi,ina cikin tunanin Kannena suka shigo dakin da na ke,Khalil,sai nusaiba,da Haruna,kannena ukune kacal don Amma tun kan Harun tace ta daina haihuwa da babanmu wai ta gaji da haihuwa ba'a yi mata ragon suna,don haka yanzu shekarun Harun Biyar Amman Amma ta daina Haihuwa,hatta Harun Amma Bata ji kunyar Dora masa talla ba,duk kannena suna talla,kowa da Safiya tayi zai tafi nashi tallan.

Muryar Nusaiba ce naji tana cewa,Anty Fahima wannan mutumin nan da kika hanani zuwa wajenshi,shine yau ya kirawoni wai inzo zai Bani alewa shine ni kuma na gudu.

Kallon yarinyar na Shiga yi hawayen tausayin yarinyar suka Shiga zarya a idanuna,"Anty kuka kike don Allah ki daina kuka idan kina kuka Nima zanyi".

"Ba kuka na ke ba y'ar kanwata,ki gayawa Amma wannan maganar kinji,don ba'asan zuciyarshi ba ".

"Wallahi Anty Amma ba zata yarda ba dukana za tayi rannan ba na Gaya mata ba,shine tace wai k'arya nake kuma wai Kada na sake in gayawa kowa,idan ba haka ba zata zaneni".

DARASIWhere stories live. Discover now