14&15

23 1 0
                                    

*Tyiping📲*

*✨🌈DARASI!!🌈✨*
(Topic)

By
*Ummu Maher(Miss green💚🍀)*

*(wattpad)*:Rabiatu333

*(Arewabooks)*:rabiattu0444

*14/15*

"Ammi don Allah ki daina kukan nan, da saka damuwa aranki abinda yaya Ammar ya ke buƙata a wajenki kawai addu'a ya kamata ki dinga yi masa,damuwarki za ta haifarwa da Yaya matsala sosai aruyuwarsa,don haka ki share hawayenki ki yi masa addu'a insha Allah Sakinat sai ta girbi abinda ta aikata miki,don raba ɗa da uwa ba ƙaramin abu ba ne."

"insha Allah auta na daina kukan nan daga yanzu".

dariya Khalisat ta yi sannan ta ce"Ammi a kullum idan na tuno wacece Sakinat a cen baya abin har mamaki ya ke bani,kamar ba ita ce ƴar aikin ki a baya ba,kucaka ƙazama."

dariya Ammi ta yi wanda ya fi kuka ciwo tana tuno wacece Sakinat a ba ya.


*Asalin labarin Sakinat*

kamar yadda Khalisat ta faɗa Sakinat mai aiki ce a gidansu tun zamanin mahaifinsu yana nan kafin daga bisani kuma ya yi hatsari ya rasu.

Sakinar ƴar asalin maiduguri ce a cen aka haifeta ita kaɗai ce awajen mahaifinta tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu,bayan mahaifiyarta ta rasu ne suka koma garin adamawa anan kuma riƙonta ya koma gun yayar mahaifinta.

Yayar mahaifinta ita ce ta kai Sakinat wajen aiki da kanta don ta ce tunda taƙi talla dole ne ta yi aiki,gidan farko da aka kaita yaron gidan ya yi mata fyaɗe daga nan kuma suka jo ne da yaron gidan don kullum Sakinat tana ɗakinsa,duk sanda
Za suyi mu'amala sai ya bata wata ƙwaya ta hana ɗaukar juna biyu,sakinat kuwa bata san ko na me ye ba don ba tada ilimin da za ta gane.
Kwatsa rannan mahaifiyar yaron ta gansu ta yiwa Sakinat korar kare,daga nan ta koma gidan yayar mahaifinta mai suna Abuwalle.

Abuwalle mace ce mai shegen son kuɗi da son duniya don haka babu daɗewa ta samo wa Sakinat aiki a gidansu Ammar.
Tun ranar da Sakinat ta fara aiki a gisansu Khalisat Ammar ya dawo daga tafiya daga ƙasar germany,Tun da Sakinat taga Ammar hankalinta ya tashi don kyaunsa da nutsuwarsa ba ƙaramin dagula mata lissafi ya yi ba.

Ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta don ko kallo bata ishe sa,ko mopping ta ke idan ta hangosa ɓuya take saboda matuƙar ta gansa to fa zuciyarta ta yi ta bugawa kenan,har sai ya bar wajen da kusan awanni sannan za ta samu damar fitowa don cigaba da aiki.

Ammi ba macece mai takura ba saboda ba ta ɗaya daga cikin matan da ke wahalar da ƴan aikinsu ba,saboda macece mai mutunci da kuma karamci.

Ana cikin haka ne Sakinat ta fara wani irin ciwo,idan ciwon na ta ya tashi har aman jini ta ke,babu shiri Ammi da Alhaji Muhammad Lamiɗo wato mahaifin su Ammar suka kai Sakinat asibiti.

Tashin farko bayan likita ya gama gwaji ya ce ai Sakinat tana da ciwon zuciya,adinga yi mata duk abinda ta keso saboda idan ba haka ba ciwon ba zai warke ba.

Hankalinsu ya tashi sosai bayan sun dawo gida shima Ammar ya dawo ganin da Sakinat suke tare ya yi gaba zuwa cikin babban farlon gidansu,yana zama sai ga su Ammi sun shigo.

Suka saka Sakinat a gaba da tambayar abinda ya ke damunta kai tsaye ta ce ita Ammar ta ke so. . . ..

Kuyi haƙuri wani busy ne shiga ne👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻.

*Miss green ce*

DARASIWhere stories live. Discover now