05/06

13 2 2
                                    

*_Tyiping📲📲_*

    🪐✨🪐
   *_DARASI!!_*
     🪐✨🪐

    *PAID BOOK*

          Na
UMMU MAHER (MISS GREEN☘️💚)

*Wattpad*
Rabiatu333

Wannan littafin na kudi ne ki biya naira 300kacal katin MTN
Ta wannan no din Amman ta what's app
07068606171
Sai kiyi screen short na katin ki turo.

ko ta wannan account din👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith Bank.

Idan kina son Shiga dukka grps Dina kuma 500 zaki biya wato VIP,idan kuma regular ne 300 ne.

Ina Yan kasuwa masu son a Dora musu wannan littafin adukkanin shafi na to ga Dama ta Samu,ki biya naira 500 dinki kacal,ni kuma in saka Miki a dukkanin shafi na.

Sai na jiku masoya Ummu Maher miss green.



       06/07
 

. . . . .har nazo ƙwanar layinmu sai naji kamar ana  bina a baya,ga warin taba dana wiwi ya haɗe waje ɗaya suna bada wani irin ɗoyi me wari,sauri na fara yi ina waiwayansu don tun ina hangosu daga nesa yanzu kurkusa na ke hango su.

  Gudu sosai na fara yi amman kun san gudun mace dana miji ba iri ɗaya bane dai gashi sun cimma ni,kuka na farayi ina basu haƙuri amman ko sauraro banga suna yi ba,don ko ɗigon tausayi babu a fuskarsu,abinda naga ɗaya daga cikinsu yana shirin aikatawa ne yasa na buɗe bakina na taƙarƙare na rusa uban ihu,yana zuge ta zugen wandonsa yana lasar
Baƙin  bakinsa wanda ya gaji da shan tabar wiwi.

Wata shaƙa babban nasu ya kawo min tare da duka na akai nan da nan na daina ganin komai sai duhu,saurin ɗaukata suka yi da ya ke dare ne babu wanda ya gansu suka shiga dani wani kango.
"Kai ba-ba ya zamuyi da wannan yarinyar kada fa a kamamu".?

"au tsoron kamen ka
Ke  kai" ?,kawai mu ƙwashi rabonmu mu mu wuce mu bar ƴar talla masu son kuɗin jaraba ai daman ƙarshen son kuɗi kenan",ya faɗi hakan yana lashe bakinsa.

   "Haba Amma ta ya ya zaki ƙwanta ki yi ta bacci amman kuma ƴarki bata dawo ba har yanzu?ki duba agogo ƙarfe goma na dare fa?gaskiya Amma wannan mummunar ɗabi'ar da ki ka ɗakko ba za ta haifa miki ɗa mai ido ba",yana faɗar hakan ya yi hanyar waje yana cigaba da mitarsa kamar zai cinye ta,amman matar nan Ƙara juyawarta ta yi tana baccinta har da minshari,Haruna ma da ya ke ƙarami kuka ya dinga kuka ganin Fahima bata dawo ba,don ya saba ita ke kaishi ya yi fitsari.

A hankali ya ke tafiya yana ɗan duba lungu2 na layinsu,ƙwatsam ya hango wani lungu,ci ke da ƴan daba suna shawarwari a tsakaninsu akan su aikata mata ko kada suyi.

  Shahada ya yi yaje wajen ya haskosu da babbar fitilarsa,da sauri suka jiyo dukkansu kana ganinsa kasan shine mahaifin yarinyar nan don har hasken da ƙyau irin na fulani duk na shi ne.

  "Aha kace kazo ne ka karɓi ƴar ka ko"?.

sai suka tuntsire da wata mahaukaciyar dariya suna nuna baban Fahima.

Kukan kura ya yi ya bige mutum biyu Alokaci guda da ya ke sun bugu sosai suka zube a wajen,saura mutum biyu,da sauri ya  yo kansu suma suka fita da gudu,ya tsugunna yana hawaye har sun fara yagawa Fahima kayanta abin tausayi.

Kawai sai yaji saukar wani abu a bayansa tun daga nan bai ƙara sanin inda ya ke ba.



    ***      ***    ***

Da wuri Sakinat ta dira a garin yola babban birnin adamawa,tana sanye da glass baƙi no respect wanda  ya gaji da haɗuwa yana sheƙi da walwali.

Ta saka ƙananun kaya komai na jikinta ana gani ita daman ƙirar slindium ne da ita babu cinya babu sharaɓa sai fari wanda har yawa ya yi mata saboda bleaching.

Chewin gum ne abakinta tana taunarsa yana ƙara ƙara ras-ƙara ras,alamar za ta yi rashin mutunci kenan .
Bata sha wahalar gane gidansu Ammar ba don rabonta da zuwa shekara shida kenan,kallon gidan ta ke tana ya mutsa fuskarta,taja trolley ɗinta tana wani yauƙi da yanga kamar mutanen gidan suna kallonta.

Hanan tana sama tana hango ta,da sauri  ta sauko don ba ta son Ammi tasan abinda zai faru don wallahi ba za ta bari wannan matar ta shigo musu gida ba,suna cikin farin cikinsu ta kawo musu baƙin ciki.

  "Ke makira ina zaki"?.

Hanan ta faɗi hakan tana ɗaga mata gira tare da tare hanya.

Wani banzan kallo Sakinat ta yi mata ta  cire gilashinta tana kallonta ta ƙasan glass ɗin, sannan ta  ce"Hmm Hanno ki ke ko wa?to ma dai ko me ye sunanki?,ko wannan siririyar bafulata na bata isa ta ce za ta hanani shiga wannan ruɓaɓɓan gidanba wanda ko albarkacin fenti ba ya samu.

Idanun Hanan suka yi jawur jin zagin rashin mutuncin da Sakinat ta ke musu,da sauri ta nuna Sakinat da hannu ta ce"Hmm da ba asan asalin balbela ba da sai ta ce daga misra ta ke,ke kin manta gidan na ki uban ko albarkacin siminti bana tunanin ya samu"?.

"kuma kinga gidannan kaf babu siriri sai wannan makauniyar uwar ta ki wacce har ta mutu bata gani saboda baƙin cikinki dana wannan baƙin basa muden uban  na ki,kuma kaf gidan na mu babu wanda ya fito ba ta hanya ta halak ba,wani kuwa sai da a kayi cikinsa sannan aka yi aure. . .

Cikin matsanancin fushi Sakinat ta kaiwa Hanan wani mari,Hanan ta shafa wajen da hannunta ta ce"ko yanzu Sakinat na fiki cin ribar zance tunda gashi har kinyi mari saboda fusata,amman fa baki mari banza ba don ba a marin wannan ƙyaƙyawar fuskar tawa a zauna lafiya ko mijinki ne kuwa ballan tana ma ke."

wani mari Hanan ta kaiwa Sakinat wanda sai da yasa ta riƙe hannun  ƙofar shiga farlon,wata shaƙa Sakinat ta kaiwa Hanan,ta kama maƙogoron ta Hanan ta kama kararin mutuwa,Ammi ta fito za ta gidan barka ta hango abinda ya ke faruwa.

  Da sauri ta ƙaraso tana  rabasu tana mamakin ƙarfin hali irin na Sakinat,sa ƙer Ammi ta ɓanɓare Hanan ta ƙwanta luf a hannun Ammi kamar ba ta numfashi.

Sakinat tayo kan Ammi za ta haɗasu duka,suka jiyo sallama Ammi na kallon tsinanniyar shigar da Sakinat ta yi wai a matsayin matar Aure matar ɗanta tilo.

Amir ne da matarsa har da ƴaƴansa biyu,sosai sukayi mamakin ganin Sakinat a gidansu Ammar don sun san takun saƙar da ke tsakaninsu.

Amir ya ce"Ammi lfy me ya samu Hanan ɗin?wani abu ne ya same ta?."

gaba ki ɗaya ya tambayeta,Ammi ta  shaida masa duk abinda ta gani a lokacin da tazo,bata gama ƙarasawa ba me gayya me aiki ya fito yana sanye da kayan motsa jiki don bai san abinda ya ke faruwa ba,yana zuwa Sakinat ta saki kuka ta faɗa jikinsa kamar ƴar yarinya.
***   ***    ***

A wajen mahaifin Fahima ya faɗi baya motsi,ƴan patrol suka zo wucewa suka hango ƴan daban nan suna Ɗaukar Fahima,da sauri suka zo wajen suna zuwa suka arce da gudu amman an kama guda ɗaya.

Aka kai su Fahima asibiti aka fara yi musu taimakon gaggawa,sai dai mahaifin Fahima har yanzu bai farfaɗo ba amman Fahima ta farfaɗo.

Allah sai kun fara comments zan fara yin sa da yawa.


*Miss green ce*

DARASIWhere stories live. Discover now