20/21

47 3 0
                                    

*DARASI!!*

  Free page 20/21

Rabiatu Bashir
(ummu maher)miss green.

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu ta online zasu biya 2k*

Sakinat ce a zaune tana waya da Falmata, kana ganin Sakinat kasan ranta a ɓace ya ke ta ce"Falmata yau watanmu biyar da zuwa wajen bokannan amman har yanzu banji wani chanji ba da zaisa in gane ina da ciki,abin yana damuna Falmata ni dai idan babu hali kawai mu chanja wani bokan kawai ina ganin zaifi ko"?.

shiru Falmata ta yi tana mamakin hali irinna Sakinat don duk bin bokaye irin na Falmata bata ka ma ƙafar Sakinat ba,ko da ya ke Sakinat ta yi mata zarra a fannin kuɗi dole ta fita fitowa gari.

"Eh aƙwai wani boka da na ke tunanin zai iya wannan aikin wanda matuƙar ya yi miki aiki to fa shikkenan,zaki ganki da ciki a jikinki ko da na aljanu ne kuwa".

da sauri Sakinat ta ce"haba Falmata ya zaki ce wai ko da na aljanu ne,idan na samu cikin aljanu ai an samu matsala lafiyayye na ke son haifa".

Ƴar dariya ce ta kusa kufcewa Falmata don tasan duk wannan yawon da suke yi ba lallai ne ta haihu ba,don tun tana budurwa ta gama zubarda abinda tun a waje".

Ƙalubale gareku ƴan mata ku daure ku riƙe mutuncinku domin shi mutunci madara ne,kuma daga inda namiji ya yi amfani da ke ko da ciki bai shiga ba to kin gama cutar kanki,gwara duk rintsi ki daure ki kaiwa oganki(mijinki)budurcinki na ƴa mace,wallahu a 'alam.

Nan dai Sakinat da Falmata suka shirya zuwa har Ghana wajen wani tsohon mushriki don Sakinat ta samu Haihuwa,washe gari da wuri suka ɗauki hanya don ma jirgi zasu shiga sai Accra(Ghana).

Sun sami layi sosai don haka suka jira har layinsu yazo,suna shiga Sakinat ta fara toshe hancinta don wani irin mugun warin da wannan mushrikin bokan ya ke,Falmata ta riƙe hannun Sakinat tana janta don ta daina rufe idon,don idan bokannan ya zuciya zai iya gamaw dasu duka ya shanye musu jini.
Tun kafin su faɗi abinda ya kawosu Bokan ya fara faɗa musu duk abinda suke so ayi musu,ya janyo wani glass yana nuna musu abinda ke ciki.

Wata yarinya suka hango kyakkyawar Bafulata na suka hango yarinyar ba za ta wuce 13zuwa14 ba,cikin tsoro Sakinat  ta ce"boka wannan kuma wacece?menene haɗinmu da ita?"

cikin sauri bokannan ya buɗe mushen bakinsa ya ce"ita wannan yarinyar ita ce za ta kawo ƙarshen matsalarki."



Alhmdh.

Anan na kawo ƙarshen book 1,kuma na gama free page idan ka tashi biyan kuɗinka ka neme ni ta  wannan number.

07068606171

Ga
Details

*Littafin na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun baki biyani ba,Gamai buƙata n cigaban labarin zai biya ₦300 normal* group...Vip group
₦500... Special₦1k....zaku iya Turo da katin MTN ta wannan number 07068606171
ko kuma ku tura ta wannan account number  2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith Bank.

*Miss green ce*

DARASIWhere stories live. Discover now