08/09

21 1 0
                                    

*_Tyiping📲📲_*

    🪐✨🪐
   *_DARASI!!_*
     🪐✨🪐

    *PAID BOOK*

          Na
*UMMU MAHER (MISS GREEN☘️💚)*

*Wattpad*
Rabiatu333

Wannan littafin na kudi ne ki biya naira 300kacal katin MTN
Ta wannan no din Amman ta what's app
07068606171
Sai kiyi screen short na katin ki turo.

ko ta wannan account din👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith Bank.

Idan kina son Shiga dukka grps Dina kuma 500 zaki biya wato VIP,idan kuma regular ne 300 ne.

Ina Yan kasuwa masu son a Dora musu wannan littafin adukkanin shafi na to ga Dama ta Samu,ki biya naira 500 dinki kacal,ni kuma in saka Miki a dukkanin shafi na.

Sai na jiku masoya Ummu Maher miss green.

    

     *08/09*

. . . . .har yanzu mahaifina bai farfaƊo daga suman da ya yi ba,sai dai yana numfashi,hankali na ya tashi sosai don likitoci sun faɗamin Mu biyu aka kawo mu ni da mahaifina,kuma tunda aka kawo mu ƴan sintirin da suka kawo mu sune suke biyan kuɗin.

  Amma tana gidan goggo mahaifiyarta sai faɗa ta ke mata na rashin mutuncin da ke yi,gashi yanzu daga ni har mahaifina babu mu babu labarinmu,sharce hawaye ta yi da majina ta ce"wallahi Goggo ni fa ban san yadda a kayi yarinyar na neme ta na rasa ba,daga tura ta talla tun jiya bata dawo ba,idan zubarda kuɗin tallan ta yi ta dawo mana,shi kuma Malam da karan baninsa ya tafi nemo ta,gashi yanzu babu labarinsu su duka".sai ta cigaba da kukanta.

Tun da ta fara maganar Goggo ke yi mata wani banzan kallo,sai da ta gama sannan ta ce"wai ni kuwa Amaturrahman kina da kirki kuwa?"cewa fa ki ka yi wai mahaifinta ya yi karanbani?shi da ƴarsa sai yaƙi fita nemanta saboda sakaci da kuma rashin hankali?,ke irin wannan riƙon na yi miki a rayuwarki?tambayar ki na ke yi?".kamar za ta daki Amma ranar ta yi suna cikin wannan halin ne a kayi sallama a ƙofar gida.

Kallon banza Goggo ta yiwa Amma sannan ta ce"w/kslm waye?".ta ɗauki mayafinta ta leƙa.

Salati ta fara yi tana kiran sunan Allah tana cewa"to shikken Mlm Bashir yanzu zamu taho insha Allah",da sauri ta dawo tana faɗawa Amma wai ƴan sintiri ne jiya suka kai su  Fahima da mahaifinta asibiti,kuma tunda safe akaje cen gidan Amma ba a sameta ba,shine Bashir ya ce yasan kina nan gidan.

Bakin Amma bai mutu ba da abinda ya faru da mijinta da ƴar ta ba sai cewa ta yi"Hmm su Bashir an riƙa wajen iya gulma yanzu har yasan nan na taho?".

lokacin har Goggo ta saka hijabi ta ɗakko kuɗi ta ɗaure a bakin zaninta"ta ce to maras tunani idan kin gama gulmar mutane ki tashi mu tafi?wa wiya kawai mara tunani,har a wannan halin da ake ciki bakin ki bai mutu ba".
***    ***    ***

abin mamaki Sakinat tana fara kuka hankalin Ammar ya tashi,ya kalli Khalisat da ke jikin Mahaifiyarsa tana kuka ya daka mata wata uwar tsawa ya ce"shut up!ki yiwa mutane shiru munafuka wato daman bakya son matata ko?to wallahi ko waye zai ƙi matata ko waye wallahi tallahi saina rabu dashi".ya faɗi hakan cikin yaran fillanci ya riƙe hannun Sakinat suka yi wuce warsu,Sakinat harda wani la fewa ajikin Mijinta tana yiwa su Ammi gwalo.

Ni kuwa na ce oh Sakinat kamar abin arziƙi haɗa ɗa da uwa,Duniya ina zaki damu😭.ya Allah ka haɗa mu da surukan arziƙi Amin.

Sororo Ammi ta yi tana kallon bayan ɗanta Ammar,shi kuma tasa ƙaddarar kenan mace,jiya i yanzu yana tare da ƙanwarsa suna hira kamar abin arziƙi,amman yau daga zuwan matarsa har komai ya watse.

Wasu zafafan hawaye ne ya fara zubowa Ammi a ƙwarmin idanunta, bata san sanda Khalisat ta saka hannu ta fara share mata hawaye ba,ita ma Khalisat ɗin kuka ta ke na tausayin kansu"Ammi ki yi haƙuri don Allah kinji,komai ya yi farko yana da ƙarshe kada ki saka wannan abin a ranki kinji?".rungume junansu sukayi suna tausayin kansu dana Ammar.

Har sun manta da tsayuwar Amir sai da sukaji yana cewa"haƙiƙa Sakinat ba ƙaramar butulu ba ce da ta manta,da duk abin arziƙin da ki ka yi mata ta butulce miki,ta zaɓi taci miki mutunci ta kassara miki rayuwaɓ,ta zaɓi hanyar musguna miki ta hanyar mallake miki ɗanki,amman babu komai aƙwai Allah."

Matar Amir ma har kuka ta yi don ganin abinda ya faru,tana yawan ji a littafin hausa da sauran kafofi yadda ƴaƴa suke wulaƙanta iyayensu, amman bata taɓa gani da idanun ta ba sai yau.

a ranar Sakinat ta saka mijinta a gaba kamar mayya suka tafi Abuja,shi kuwa Amir saboda haushi daman alokacin ya tafi gida,saboda takaicin hali irin na Ammar ace ka rasa wanda zaka ƙunta tawa a rayuwarka sai mahaifiyarka wacce tasha wahala a rayuwarta don rayuwarka ta ginu?gaskiya abin aƙwai lauje cikin naɗi.
Ranar gidan Ammi kamar ana zaman makoki,gidan shiru don ɗan wannan zuwan da Ammar ya yi komai sun ƙara shaƙuwa sosai,ranar kusan raba dare Ammi da Khaisat sukayi suna kaiwa Allah kukansu ta hanyar yin nafilfilu.


Abin mamaki ranar Amma ta saka rigima wai mu koma gida alhalin har yanzu mahaifina bai farfaɗo ba,aranar na sake tabbatar da rashin tausayin Amma,Goggo ce tace mata idan ta gaji a yini ɗayan da ta yi,to ta tafi gida ita za tayi jinyar sa tunda shima ɗanta ne,jin wannan da Amma ta yi yasa ta zauna amman ba don ranta yaso ba don biyunnan da ta yi bata yi sana'a ba abin yana matuƙar damun ta sosai.

Hmm kuji fa rashin tausayi irin na wasu matan,mijinki yana ƙwance bashi da lafiya,mijin da ki ke saka ran samun aljanna ta ƙarƙashinsa amman ace kina nuna masa rashin tausayi haka?😭.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

A ranar likitoci sukayi bincike wai mahaifina ya. . . .

Yasin idan kuna comments da yawa zan ƙara yawan tyiping oh.



*Miss green ce🍀🍃*

DARASIWhere stories live. Discover now