*💧💧RUƘUƘI.....!*
_TOP TEN BATCH B._
*©️HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writer*FEEDOHM.*
Wattpad:Feedohm._DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI, WANNAN LABARIN IS BASED ON TRUE LIFE STORY, IDAN YA YI DAI DAI DA NA KI, TO BA NA KI BA NE, ALLAH YA BAMU IKON RUBUTA DAI DAI, KA TSARE MU DA RUBUTA ABINDA ZAI ZAMA BARAZANA GARE MU, RANAR DA BABU ISASHSHE SAI ƘAI..._
*Tun daga farko har ƙarshen labarin sadaukar wa ne ga mutane uku, JAMILA ABDULLAHI IBRAHIM, HANNATU (Mamn abadi), SAMIRA BELLO ABDULLAHI (Elham) Alkhairin Allah ya kai maku a duk inda kuke.*
FREE PAGE.
*01*A hankali ta ɗaga kai saitin window tana kallon yadda gajimare ya baƙiƙƙirin, yayin da wata ya shige cikin duhuwa, sai jefi jefin taurari a sararin samaniya, a lokacin ne zaka tsammaci kowanne ɗan adam ke hutawa, banda ita da Allah ya ɗaurawa baƙar ƙaddara, ta koma taɓas ta zauna hawaye na bin kuncin ta, a hankali ta lumshe idon ta, ta saka fuskar ta cikin tafukan hannayen ta, tana jiyo sautin haushin karnuka da kukan tsuntsaye, kusan minti arba'in alarm ɗin ƙaramar wayar ta ya hau vibrating, ta ɗago fuskar ta, idanun ta a lumshe, hawaye na bin kuncin ta, kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki ta miƙe daga zaman dirshan ɗin da ta yi a tsakar ɗakin, ta ɗauki zanin Atampha ta rufawa kan ta, sannan ta buɗe ɗakin a hankali tana leƙen falo, yayin da take amfani da hasken screen ɗin wayar ta wajen tabbatar da babu wani mahaluƙi a falon, sannan ta fito saɗaf saɗaf ta nufi bedroom ɗin mamallakin gidan, ta tura a hankali tare da addu'ar kada wani abu ya mata togiya da muradin ta, ɗakin yayi tsananin duhu har ba ta iya ganin gaban ta, sai dai zuciyar ta, bata makance ba, ta lumshe idonta tana bin umurnin zuciyar ta, wajen kai ta ga cikar muradin ta, kafafun ta suka tokare da katakon tafkeken gadon, yayin da haske ya gauraya ɗakin, ta buɗe idon ta da sauri cike da firici, ta yi tozali da shi yana ƙwance fuskar sa na kallon sama, yayin da fararen idanun sa suka kaɗa sukai jawur! Ke nan ba ita kaɗai ba ce bacci ya ƙaurace ma idanun ta? Ba ita kaɗai ba ce hawayen ta suka gagara tsayawa ba? Ba ta yi mamakin ganin shi a haka ba, ya zuba mata ido cike da tambayoyi daban daban.
A bisa faffaɗen ƙirjin sa, cikar muradin ta ke ƙwance tana bacci cikin ƙwanciyar hankali, ta lumshe ido tana faɗin "Me na zo yi.?
Ya girgiza kai a hankali, cikin ƙunci ya ce "Na san zaki zo Maryama.!
Ta kulle idon ta, tare da kawar da fuskar ta gefe, tana jin wani ɗaci a zuciyar ta, a hankali ta ce "Ba kuma san fasa zuwa ba Abdallah, har sai lokacin da na raba Fatima da wannan muguwar rayuwar."
"Ina da yaƙinin muradin ki, ba zai taɓa cika ba har abada, ki amshi ta yi na, mu haɗu mu haskaka rayuwar abinda kike kira da muradin ki."
"Har abada! Har abada! Wannan lalataccen tayin na ka, ba zai amsuwa ba, ni da ƴata ba zamu taɓa zama ƙarƙashin mugun mutun irin ka ba! Abdallah ko da zan yi dare dubu saba'in ina zuwa ba tare da cimma manufa ta ba, wallahil azim ba zan gushe ba, har sai na cimma ta."
"Ƴar ki ko ta wa.?
"Ko ya za ka kira ta! Abinda na sani, ƴar Ungu mallaki na ce! Ba kuma zan taɓa barin ta zauna gidan mutumin da ya zalunci mahaifiyar ta ba, mutumin da ya kashe mini ƴar uwa ba! Abdallah dole ka bani ƴata ko da duka duniya zata mara maka baya."
"Ni kuma na maki alƙawarin, da ke da ƴata dukkan ku, zaku zauna a ƙarƙashin wannan mutumin, zai haska maku rayuwa fiye da zato, zai gyara kuskuren shi.... ."
Bata saurare shi ba, ta saka hannu tana kiciniyar ɗauke yarinyar, yayin da ya rungume ta gama yana kallon ta...
*******