04

37 4 0
                                    

*💧💧RUƘUƘI.....!*

_TOP TEN BATCH B._

*©️HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writer

*FEEDOHM.*
Wattpad:Feedohm.

*Tun daga farko har ƙarshen labarin sadaukar wa ne mutane uku, JAMILA ABDULLAHI IBRAHIM, HANNATU (Mamn abadi), SAMIRA BELLO ABDULLAHI (Elham) Alkhairin Allah ya kai maku a duk inda kuke.*

FREE PAGE.
04

Ta watsa mashi dara daran idanuwan ta cikin nashi ta na faɗin "Wai wannan bala'in na menene? Ina ce kowa da kabarin shi Abdallah? Ko na ce ba zan yi ba? Ko ko zan gudu ne? Dan Allah ka rabu da ni, da wankan da sallan, duka zan haɗa in yi, idan na tashi daga bacci.!

"Aƙwai matsala.! Ya faɗa a fili yana kallon ta.

A zafafe ta ce "Ka yi maganin ta Abdallah! Allah ya shi ne shaida, iyayena ba su takura mini ba, don haka kai ma ba za ka takura mini ba, ina ce sai mutun ya balaga sannan a fara mashi irin waɗannan tsawwale tsawwalen, to ni ban balaga ba, don ban haihu ba, ina da sauran lokaci gaba, haka fa da azumi ka tsawwala mini sai da na yi 12, kamata, ba tausayi bare imani, abunda bai wuce inyi uku ko huɗu ba a gida ba. "

Cikin tsananin mamaki ya ce "Wa ya faɗa miki haka.?

Ta murguɗa baki ta koma ta zauna, a hankali ya taka har inda ta ke zaune, ya duƙa tare da ɗaura hannun shi saman cinyar ta ya ce "Duk wanda ya faɗa miki haka ya maki ƙarya Hanan, shekarun balagar mace suna farawa daga 9years, ya danganta da lokacin da ta fara ganin al'adar ta.!

"Dad ya maka ƙarya kenan.?

Ya girgiza kai yana kallon ta, ta ture hannun shi daga cinyar ta tana faɗin "To ba zan yi ba, Abdallah idan kai ke raba aljanna idan na zo shiga ka hanani...! Ta fashe da kuka tare da birkicewa bisa gadon.

Nan da nan jikin shi ya hau ƙyarma, kamar ya kife ƙasa ya miƙe ya bita bisa gadon, tare da ɗagota ya maido jikin shi yana faɗin "Ba haka ni ke nufi ba, ki yi haƙuri dan Allah, ban yi don haka don in baƙanta miki ba, stop crying please...!

Ta fara ƙoƙarin fizge jikin ta, amma ya rungume ta gam ya ɗaura kan shi saman ƙafar ta yana lallashi haɗi da bata haƙuri, domin jin kukan ta ya ke har cikin ran shi, zai fi sauƙi a sara mishi adda fiye da ta yi kuka, jiki sa ya ɗau ɓari, da ƙyar ya samu ta daina kuka sannan ya samu natsuwa, sallan da bata yi ba kenan, bai kuma sake mata maganar ba gudun ɓacin ran ta, ya lallaɓata suka fita suka yi breakfast, sannan ya dawo da ita ɗaki kamar mara lafiya tana cika tana batsewa ya ƙwantar ya bi ta da bargo dare da sumbatar forehead ɗin ta, sannan ya gama shirin shi ya fita office lokacin har 9am ta wuce.

ABDALLAH FAROUK, shine cikakken sunan shi, ɗa na farko ga Alhaji Farouku bawan Allah, da hajiya murya, suna da arziki sosai, saboda tsohon ma'aikacin gwamnatin ne, sannan ya riƙe noma da kiwo hannu biyu biyu, ita kuma ƴar kasuwa ce, suna da yara biyu, da Abdallah sai ƙanwar sa Aminatu, su duka sun yi aure, iyayen su sun tsaya masu sun samu ilmin addini da na boko dai dai gwargwado, domin shi Abdallah Phd gare shi ɓangaren accounting, shine ya ke aiki a uba bank matsayin manager, saboda yana da sha'awar aikin banki tun yana ƙarami, yayin da Amina ta karanci physic kuma iyakar ta degree tana teaching a wata government secondary school, ƙyaƙyƙyawa ne na asali kuma ɗan ƙwalisa mai cike da izza da ƙasaita, idan ka ga yana magana a gida ne! Yana da ƙyawun mu'amala da jama'a, taimako da kyautatawa, sai dai yana da banzan hali da ya zame masa ɗabi'a ta rashin son baƙa, mummunar mace, sannan yana masifar son ƘYAU! Wannan ƘYAU shine ya ruɗe shi har ya auri Hanan! Ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata.

HANAN JAMEEL, yarinya yar gatan Dady, ƴar asalin Sokoto, aiki ya kawo babban ta Katsina, rainon madara, yayen bournvita, rarrafen carpet! Ƙyaƙyƙyawa ta gaske, sai dai ƙyawun ɗan maciji, bata san komai ba sai latsar waya, ta fara karatu a germany ta dawo gida a cewar ta, bata iya bawa ƙwalwar ta wahala, tunda take bata taɓa zuwa islamiyya ba, shiyasa su kai hannun riga da tarbiyya, duk duniya ba ta da wani abu mai mutunci sama da iyayen ta, a idon ta, su ne kaɗai su ka cancanci girmamawa a duniya....

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 04, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RUƘUƘI Where stories live. Discover now