*💧💧RUƘUƘI.....!*
_TOP TEN BATCH B._
*©️HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writer*FEEDOHM.*
Wattpad:Feedohm.*Tun daga farko har ƙarshen labarin sadaukar wa ne mutane uku, JAMILA ABDULLAHI IBRAHIM, HANNATU (Mamn abadi), SAMIRA BELLO ABDULLAHI (Elham) Alkhairin Allah ya kai maku a duk inda kuke.*
FREE PAGE.
02Ya nufi fridge ɗin ya ɗauko, yana jin kan shi a dagule, har ga Allah ya fara gajiya da wannan shegiyar mandi ɗin, abu facau duk lemun tsami, ya ja ƙaramin tsaki, wata uku kenan da auren su, amma sau uku kacal ta taɓa girka mashi abinci, na farko indomie, na biyu caɓalɓalin shinkafa da romo, wai ahaka fried rice ta girka da taimakon ƴan WhatsApp group ɗin su, na uku kuma faten cabbage da bread, shi kam wannan tunda uwar ta haife shi bai taɓa jin haka ba.
Hakimar na zaune ya dawo ya zauna, yayin da ta ƙyalƙyale da dariya lokacin da wata a group ɗin ke tambayar _Dan Allah a koya mani sinasir da miyar talotalo da ƙwai, sannan a koya mani haɗin natural drink mai shegen daɗi, oga na hanya yace lallai shi ya ke so._
"Ƴar wahala, a kitchen za ku ƙare.! Ta faɗa a zahiri, sannan ta fara typing _Sinasir sai ku, ai ni bana iya wannan wahalar, a saukar alƙur'ani miji ne zai ciyar da ke, aikin ki ƙwalliyar da zata faranta mishi, amma kun ɗaukar wa kan ku wahala, kawai ki mashi order a restaurant._
_Ya fi son na girka mishi da kai na_ Ta maido mata amsa.
_Ok ke kika ji zaki iya, for miyan talotalo kam, kiyi blending kayan miya, garlic, clove, cabbage, cucumber, scent leave, idan kina so ki haɗa da flesh ɗin ki Markaɗe da su spices, da oil, ki zuba a tukunya ki rufe, har sai ta danƙare, ana zuba flour don ta yi haske._
Kafin ta maido mata, wata ta tambayi farashin gram na Gold.
Har ƙyarma ta ke wajen maida mata reply da _Jiya da teddy ya siyo mani earing 10gram, ya ce 350k, kin ga 35k each gram._
Yana tallabe da hannu, da ƙyar ya iya cin rabin tsatstsamar mandi rice, ya ture tare da jan ɗan siririn tsaki ta yadda ba zata iya jiyo shi ba, wani irin ƙugi cikin shi yayi alamun tsananin yunwa, ya kalli agogon dake falon mai ɗauke da pictures ɗin su na biki, dare ya yi ga kuma gajiya, da babu abunda zai hana shi fita ya nemi abinci, sannan baya iya jin zai shiga kitchen ya dafa wani abu a yadda ya ke jin jikin shi, ɗan gyaran murya yayi ko zata kalle shi, amma bata ko kalli inda ya ke ba, ya miƙe ya je kitchen ya ɗauko plate da ƙaramar knife, sannan ya buɗe fridge ya ɗauko coke da apple guda biyu ya dawo ya zauna ya na faɗin "Pie a aje wayan aci apple ."
Ta yatsina fuska ta ce "You know, ban cika son red apple ba."
Ya murmusa tare da shigingiɗawa yana lumshe fararen idanun shi, ya yanka apple ɗin shi ya soma ci a hankali yana kallon ta, wani irin so ya ke mata mai tsananin gaske, wanda hakan ke saka shi kasa ganin laifin ta, so yake ya riƙa tarairayar ta kamar ƙwai ta yadda jikin ta ba zai taɓa canzawa ba, yana son taushi, haske haɗi da santsi fatar ta, ƙyawunta da cikar surarta ya tsaya haka har abada, duk da wani lokacin yana son ya nuna mata ɓacin ran shi, amma sai zuciyar shi ta tunatar dashi, idan mace tana shiga damuwa tana baƙi haɗi da muni, bisa dole ya ke shanye duk abunda zata mashi, saboda tsakani ga Allah ya tsani baƙar mace nesa ba kusa ba, shi fa ko irin wannan chocolate skin ɗin baya ƙauna, kawai fara tas ƴar gidan madara, because duk cikin family ɗin shi babu baƙi, sai Uncle ɗin shi da ya auro wata jaka baƙa da ke haifa mashi ɗiya kamar baƙin tukunya.
Bai aune ba, ya ga past 12am, ya lumshe ido yana kallon ta, cikin muryar bacci ya ce "Mu je mu ƙwanta."
"Ka je ina zuwa." Ta bashi amsa a takaice.