*💧💧RUƘUƘI.....!*
_TOP TEN BATCH B._
*©️HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writer*FEEDOHM.*
Wattpad:Feedohm.*Tun daga farko har ƙarshen labarin sadaukar wa ne mutane uku, JAMILA ABDULLAHI IBRAHIM, HANNATU (Mamn abadi), SAMIRA BELLO ABDULLAHI (Elham) Alkhairin Allah ya kai maku a duk inda kuke.*
FREE PAGE.
03Unɗa na zaune ɗaki tana son fitowa tana shakkar kashedin Ungu, sai ga babameɗɗe ya shigo gidan kayan jikin sa duk jini, daga nan ta ji yana tambayar Dada buta, ta yi karaf ta fito, ta bashi ta koma kusa da Ungu ta zauna tana faɗin "Ai dai kin ji shi ya ce a bashi gora.?
Ta gyaɗa mata kai alamun ta ji, bayan ya wanke jikin shi, ya shiga ɗaki ya canza kaya, sannan ya dawo tsakar gida ya zauna, cikin tashin hankali ya ke bawa su Dada labarin irin rashin imanin da su aikata, idanun shi suka kaɗa su ka yi jawur lokacin da yake faɗin "Haka gidan buba, a gaban shi suka yi ma matar shi fyaɗe, sannan su ka yi mata yankan rago bayan sun saka bindiga sun dagargaza nonuwan ta, sannan suka kora yaran shi ƴan mata biyu daji, suka yanke mashi ƙafa."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'u..! Abunda Dada ke faɗa kenan, yayin da hawaye suke bin fuskar ta.
"Wannan bala'i har ina? Dan Allah ka yi ma Allah da manzan sa mu yi ƙaura daga garin nan, kamar yadda jama'a ke yi." Dada ta faɗa.
A sanyaye ya ce "In yi ƙaura in tafi ina? In bar jama'a ta? Ko kin mance ni ne mai gari? Ko kin manta da nauyin da Allah ya ɗaura mini na kula da haƙƙin mutane? So kike in gudu in bar su? Su yi ya ya.?
Dada bata kuma cewa komai ba, Ita kam Ungu mutuwar tsaye ta yi a gurin da ta ke, jikin ta na rawa, yayin da Unɗa ta dafa guiwar shi tana faɗin "Babameɗɗe ba inda za mu je mu bar gonar mu, kawai Allah ya isan su, to yanzu wa zai dafa mana shinkafar tunda sun kashe matar gidan.?
A sanyaye ya tambaye ta "Wace irin shinkafa Maryama.?
"Shinkafa dai babameɗɗe tunda yana da kuɗi, ka ga sai mutun ya je da ƙwanon shi da cokali, ka da ma a cuce shi da sunan ba ƙwano."
Sai yanzu ya fahimce ta sarai, ya girgiza kai yana faɗin "Maryama ki kiyayi ranar da za'a zo cin shinkafar gidan ku, a ranar ke ba zaki iya ci ba, jama'a ne zasu ci maki."
"To he me babameɗɗe? Aradun Allah sai na ci ko a ɓoye ne, su ma su zo su ci, banza ce ta faɗi."
Ya shafi kanta, cike da tausayin ta ya ce "Ƙwarai kuwa banza ta faɗi Maryama, banzar da har ki mutu ba zaki manta da ita ba."
Dada ta hana ta bashi amsa ta hanyar umurtarta "Je ki ɗauko hamsin ki amso mini kuka da daddawa gurin Iya."
"Ni kam Aradun Allah ba'a siye gurin ta, gwamma in je gidan su Hari in sawo miki duk tsadar su."
Babameɗɗe ya ce "Ta dawo ne.?
"Ta dawo aradu, riƙe da zani kamar mayya. "Unɗa ta bashi amsa kamar tana jira.
Ya yi mata kallon kashedi, ta yi gum tana haɗiyar miyau, ya ɗaga murya ya ƙwala ma Iya kira " Hanne.!
Daga ɗaki Iya ta amsa "Iyeh! Kira ka ke.?
Ya yi banza da ita, sai gata ta fito riƙe da cinyar kaza a hannun ta tana ci, ya kalle ta cike da tuhuma ya ce "Ina kika je? Duk tashin hankalin jiya ban ji motsin ki ba? Sannan yanzu kin fito da nama a hannun ki? Ina kika same shi.?.
Iya ta fashe da kuka ta ce "Dama ya za'ayi ka ji ni malan? Bayan ba ta ni ka ke ba, hankalin ka na ga matar ka da yayan ka? Allah ya sani banbancin da ake nuna mini gidan nan ya ishe ni, ina jin harbin bindigar nan na nufo ɗakin ka, sai naga kayi ɗakin Ade, na ƙwala maka kira ka yi watsi da ni, ka je ka ɓoye matar ka da yayan ka, ni banza ko oho, haka na shiga daji na samu bishiya na hawo da ƙyar na tsira...! Ta cigaba da shashshekar kuka.