🍇 _Abdoul maneou_🍇
FREE PAGE 5to6
_____________Fitowa mukayi daga cikin ɗakin Iya muka sameta a waje
"zamu je mu dawo" adawo lafiya ta mana muka wuce lokacin da nazo fita daga gidan sai da na fara leƙawa waje saboda kar Fatime bala'i ta maƙale a ƙofa muna fita da riƙe mu ba shiri, da na leƙa na tabbata ba kowa, sannan na fito ina cewa Ma'u ke fito ba kowa fa,
muka kama hanyar gidansu Feenarh a hanya sai tsalle_tsallenmu mukeyi har muka isa k'ofar gidansu,
bulo na ɗauka na wurga cikin gidan nasu ,na kuma daukan wani na daki ƙofar gidan dashi,.saiga Feenarh tafito da sauri"ke wai meyake damunki??" duk sanda kika zo da jifa ne zan gane kin iso?" tafaɗa tana tambayata
kallon tara saura kwata nayi mata sannan nace " so kike na shigo wannan mugun yayan naki ya dake ni ko?"nima na bata amsa ina tambayarta
"gaskiya yayanki akwai mugun hali gareshi" ina bata fuska nafaɗa dan har zuciyata yayanta mugune ,kallo na tayi bataji daɗin abunda nace ba, na kalleta nima nace nafaɗa,nikam
kuzo mutafi majalisar cin amana muyi shawara achan cewar Ma'utafiya mukayi Chan wani waje da ake cewa majalisar cin amana muka shige wata 'yar bukka mu ka zazzauna a ƙasa Feenarh ta kalleni tohm yanzu mai za'ayi ,
gira d'aya na daga nache" oho"
Ma'u tayi saurin kallona "gaskiya ke dai ƴar iskace ya ma za'ayi wai kice mana oho"
Feenarh ta ƙarbi zancen da cewa "nikam ina ga kawai zanje nabawa Fatime bala'i haƙuri kawai in yaso ta daken a wuce gun inb......"kan bala'i idan kin isa shegiya nake ,kuce bani bace jikar A'i "
na katse wa Feenarh maganarta ina ta hura hanci ni a dole ta ɓata min rai
"dallah kutashi mutafi anfasa sulhun ,dan halak kafasa" na fita a fusace amma sai nayi turuss saboda ganin Fatime a gabana tana kallona bata rai nayi zan wuce ta jawo rigata kiiiii tadawo dani baya ta na cewa "ke dawo nan "
"ba ruwanki dani ban shiga harkarki ba"nafaɗa mata haka,
wata dariyar rainin hankali ta shek'e da ita "wallahi yau kwananki yak'are domin kuwa sai na ci ubanki la'ada waje" tafada tana kara finciko rigata,
karar gudu naji daga bayana ina juya naga su Ma'u ne suka arce suka barni,,
"lallai yau ku taro wa kanku masifa" nafada araina ina k'wafa
sauƙar bulala naji ajiki na ina d'ago wa naga Fatime tana niyyar kaimin wani gashi yara sun fara taruwa ,kamar ni uwar daba za'a kama a daka a hanya ,
fincikewa nayi zan tafi tak'ara jan rigata
berettt rigata ta ɓarke
"kutt idan kin isa Allah ya tsinemin"
na fada raina a bace nayi kanta da duka ta ko ina nake dukanta, dan zuciyata ta ɓaci duk wani fitsarata bana son ataba mutunci na ,
kwarfo ƙafarta nayi saboda naga yadda yaya ado yakeyi mana nida safiya,
wanwar tafaɗi akasa sai da na mata dukan da ko tashi bazata iya ba sannan nayi tafiyata,
ina ayyana irin bala'in dasu Ma'u suka saka kansu a cikigida nakoma abuna na samu Baffa a ƙofar gida na gaida shi sannan nayi cikin gida
a tsakar gida na samu Fadwa tana ta wasa daukanta nayi ina mata wasa mukayi cikin ɗaki..🍇🍇
ABUJA
MAITAMA ESTATEcikin bacci Maan yake jin wani abu mai laushi yana tab'a masa jiki
yasan ba kowa bace Angelina ce ƙara gyara kwanciyar sa yayi ya juya mata baya ,ita ma da taga haka sai ta hau kansa tafara tattakashi rabuwa yayi da ita ,farcenta,
ta ni tsama sa acikin duvet ɗin nasa
"auuchhh " yafaɗa ya na mik'ewa zaune jawo ta yayi jikinsa yana shafa gashin jikinta
"what do you need"? ( mekike buƙata) yafaɗa yana cigaba da shafata, daga ƙarshe ya sauƙo daga kan gadon ya had'a mata madara yabata "oyya maza kizo Kisha madara"
ya wuce bathroom brush yayi sannan yafaɗa bathtub yayi wankansa tsaff sannan yafito as usual kamar yadda yasa ba shirin sa
baƙar armless yasaka agaban rigan ansaka dolce gabbana da short nica,
sai da yabata lokaci sosai wajen gyaran sumarsa sannan yasaka bandana akansa yaɗauko angelina suka fito.a parlo ya sami yan gidan gaba-ɗaya kowa ya hallara amma har yanzu bai ga Fannarh ba,
zuwa yayi ya rungume Daddy yana cewa "good morning Dad"
"morning son" Daddy yafad'a yana shafa kansa,bata fuska yayi a shagwabe yace Daddy kaina yana nuna masa gyaran gashinsa,
kallon sa Daddy yayi sannan ya girgiza kai
"Allah ya shirye ka" dubi abunda kake kamar wani Fannarh, bangaren Ammurh yakoma ita ma yagaida sannan ya mik'a wa Umair hannu suka gaisa.
YOU ARE READING
ABDUL_MANI
RandomTYCOON a business person of exceptional wealth, power, influence.....rich man