🍇 _Abdul Maneou_🍇
PAGE 31to32________MAAN ya na gama faɗin haka ya sanya Bluetooth a kunnensa tare da jingina da kujera ya lumshe idonsa.
slowly drivern ya fara jan motar zuwa airport, wajen da privet jet ɗinsu ya ke, a hankali ya zuro fararen k'afafunsa daga cikin motar, kana ya zaro jikinsa daga motar a hankali cike da nutsuwarsa da kamewa, idanunsa akan wayarsa, ya wuce cikin jet ɗin ya zauna.
cikin abinda bai fi 4minutes ba jirgin ya d'aga zuwa sama, within 50minutes jirginsu ya sauk'a a Jigawa state, cikin garin dutse.
gidan ABBAN SARINA su ka wuce domin ya huta, daga nan su wuce cikin ƙauyen JAKA.
Cike da farin ciki FARHA ta zo da gudu da rungume MAAN, cikin murmushinsa ya shafa kanta ya na ce wa "FARHA me kike ci naga girma haka????"
murmushi ta yi tare da rufe fuska.Hannunta ya riƙe tare da cewa "ina MAMI???"
"tana parlo".Shiga cikin main parlon su ka yi shida FARHA, parlon duka ya ɗauki k'amshin turarensa.
Saman 1seater ya zauna, "A'a lale marhabun da mutanen BAHRAIN, yaushe agari???"
cute smile ya sake mata yana shafa sumar kansa, cikin vocal voice ɗinsa yace "MAMI jiya na dawo".murmushi MAMI ta yi "kaiii ABDOUL baka gajiya da tafiye_tafiye, yau kana can ƙasar gobe kana wancen".
"MAMI yanayin kasuwancin ne haka, amma nima duk ban son yawan tafiye-tafiyen" MAAN ya faɗa agajiye .
"Uhnmmm" MAMI ta faɗa, tare da sake cewa "Allah ya shiryeka, ni kam Allah ya nu na mana matar da zaka aura, muga iya inda rashin son maganarka zata ƙare" .
kamar MAMI ta soka masa allura, haka MAAN ya miƙe, ya na duba wristwatch ɗinsa, "MAMI I have to go" . ya faɗa cikin sanyin murya.
"Allah ya ki ya ye, ka gaida min OMAIR" .
Slowly ya ɗaga kansa yana fita daga parlon, cikin haiba da kwarjini ya ke tafiya .
Hannu MAAN ya ɗagawa P.A da sauri P.A ya nufi parking space ɗin da yake compound ɗin gidan .
Land cruiser ƙirar (TOYOTA) suka ɗauka, kana suka nufi in da MAAN yake zaune, da hanzari SADIO ya fito ya na ce wa "Sir".
Gently MAAN ya ɗago idanunsa ya na kallon SADIO kafin ya miƙe cikin kuzari ya nufi in da motar take.
shiga ya yi ya zauna, tare da jawo system ɗinsa, ya na danna system ya ɗaura saman lab ɗinsa, gaba-ɗaya ya maida hankalinsa kanta .
ya yin da suke ta zabga gudu saman kyakykyawar kwaltar Jigawaaa.
******************
Ɓangaren su Alhaji Atiku kamar yadda suka shirya tafiya zuwa wajen BOKA LALA, da dukukun safiya suka ɗauki hanyar ƙasurgumin dajin da ake kira da ƘARE KUKANKA, ƙarfe 8am suka isa cikin dajin, tafiya suka fara yi a saman wani tsauni mai matakala dayawa akanta .Sun je daf da bakin ƙofar sai batt suka ga wani Mummunar hallita ya bayyana agabansu, tare da kwashewa da wata hatsabibiyar dariya .
"yaku ɓatattu sannunku da zuwa masarautar BOKA LALA muna muku barka da zuwa, me ya ke tafe daku????" .
Cikin rawar jiki Alhaji Saminu ya bud'e baki "Assala....." cikin wata gigitacciyar tsawa aka ce masa "kaiii bil adama dakata,mu ba'a mana sallama anan, domin, rahamar Allah bata samun mu anan, gyara bakinka" ku shigo tare da cire kayanku gabaɗaya domin dodo zeeko sai shayar daku jini, indai kuna son tabbatuwar burinku" .
zare idanu su ka yi, wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli wancen, "idan baku iya shigowa kujuya inda kuka fito".
Alhaji Atiku ne yaja tsaki cikin dakiyar zuciya, ya saka kansa acikin ƙaramar hukumar da take saman dutsen, wajen baƙiƙirin ya ke ko tafin hannunka baka iya gani, sun ɗauki minti biyar kafin suka ga wani haske kamar walkiya ya wuce ta gabansu, kana hasken candle ya bayyana.
YOU ARE READING
ABDUL_MANI
RandomTYCOON a business person of exceptional wealth, power, influence.....rich man