🍇 _Abdul Maneou_🍇
PAGE 27to28
___________"Innalillahi wa'innailahi raji'un,wane ɗan nawa aka sawa Bomb??? bangane ba"AMMURH ta faɗa cike da tashin hankali akan fuskarta.
"Calm down UMAYYARH me yasa kike son tada hankalin ki???,can't you see your son nearest you???" DADDY yake tambayan AMMURH.
Girgiza kai AMMURH tayi kamar wata statue, ruwa DADDY ya mik'o mata, slowly ta karɓi ruwan tasha, tana sauƙe ajiyar zuciya.
"Ki kwantar da hankalinki, domin ki fahimci abinda nake nufi"
DADDY ya kwashe duk wani abunda SITTI ta faɗa masa ya gaya mata."Amma ina mai baki umarnin kada haka ya d'aga hankalinki domin ɗanki Sadauki ne jarumi kuma, gashinan Allah ya tsare miki shi ya dawo dashi lafiya" .
Suna cikin Maganar ne MAAN ya fito sanye da cardigan sky blue ajikinsa, saboda yanayin garin yau anyi ruwa da yamma, yanzu kuma da dare yayi garin ya ɗau sanyi.
Tafiyarsa yake cikin kwanciyar hankali hannunsa riƙe da IPHONE dinsa ya na dannawa, kallonsa AMMURH tayi daga sama har ƙasa.
3Quater ne ajikinsa irin mai baƙin nan, gaba-ɗaya kwantaccun gashin ƙafarsa sun fito sun ƙara taimakawa wajen fitowa da asalin kyawun fatarsa wanda hutu ya zauna mata.
"Hey you.... where are going??????"
AMMURH ta jefo masa tambaya, ɗan kawar da kansa gefe ya yi kana ya sauƙe ajiyar zuciya, yana shafa sajensa, yace "AMMURH zanyi magana da P.A ne yanzu" ."Uhnm to shi P.A din yau ba zaizo bane, sai kaje ka sameshi" AMMURH ta fada tana tsare shi da ido.
"shhhhhhh" ya ɗan ja iska kamar mai shishutun yaji kana yace " AMMURH to ai uhnm..." sai kuma ya yi shiru dan bai san kuma mai zaice ba.
"Ina jinka, na ji kuma kayi shiru" ta ƙura masa ido tana jiran taji mai zai fad'a.
Walking slowly ya juya zai bar wajen, dan totally yau ɗin baison wata doguwar magana.
"SADAUKI zo nan"
DADDY ya faɗa ya na nuna masa kusa dashi.Zama ya yi kusa da DADDY yana langwaɓe kansa
"SON me kake sonyi ne????" lumshe idanunsa ya yi kafin ya buɗe su tarr akan AMMURH yana cewa DADDY Ina son na faɗa masa yashirya ina son gobe naje naga OMAIR ne"
yayi maganar a rarrabe .
Murmushi DADDY ya yi kafin yace "Allah yakaimu, kama iya tafiya MUMMY'S SON" ya faɗa yana nuna masa hanya.
Gently ya mik'e ya nufi ƙofa cikin sassarfa.
Sautin da yaji ne ya sa shi dakata wa cike da mamaki,
"What the hell is this???"
kamar zai wuce sai kuma ya ɗan dakata domin ya gaskata kunnensa,"AHHH OMG SHH UHMM"
sautin da yake ji yana fitowa daga bayan window ɗin ɗakin.kallon gun yayi sosai "tabbas nan ɗakin SARINA ne, to me takeyi haka????" ya jefowa kansa tambaya.
Hannun ya miƙa da nufin ya leƙa ya ga meyake faruwa, sai kuma ya fasa ya ɗaga ka faɗa alamun menene ruwansa shikam.
ya kaɗa kansa yayi apartment ɗin su P.A
Su P.A suna zaune suka hango MAAN tun daga nesa, gaba-ɗaya suka miƙe tsaye suka k'ame, kallon su yake yi ɗaya bayan ɗaya kafin yayi ɗan tsaki, "dallah ku saki jikinku" ya faɗa a hankali, kafin ya kalli P.A yace "ka shirya gobe around 9am zaka kaini wancen ƘAUYEN da ka kai OMAIR"
"okay SIR" P.A ya faɗa.
kallon su SADIO ya yi kafin ya juya ya wuce ɓangarensu.
YOU ARE READING
ABDUL_MANI
RandomTYCOON a business person of exceptional wealth, power, influence.....rich man