____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna______________****_______________
Page 🖤17🖤
Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata.
Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau.
A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba.
"Bombee"
"Na'am ta amsa a dake"
Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita.
"Shin menene ya farune kika sanja a lokaci guda,duk abinda akayi miki nasha faɗamiki kiyi haƙuri,karki bari bacin rai ya sanja miki rayuwa,abinda kikayi kimsaka mu damuwa gabaɗaya,so kike kijawo mana magana.
Yanzu inaso ki faɗamin mai kikayiwa Zulaiha danaji innayi tayi maganar?"
"Karya mata hannu nayi,sannan kuma nayi mata duka kaman yanda itama tayimin,sannan bandamu ba tacemin mayyah,amma ke tacewa mayyah,sannan tace inna isa nanuna ina son kaina,shiyasa na nunmata ina son kaina ɗin"
"Me Bombee karya mata hannu kikayi,wai nasan gaji bazatayi shuru wannan zancen ya tafiba saita ɗau mataki"
"Tsawon lokaci ai nima Zulaiha tana dukana baki taba cewa komai ba,shine ita danna rama saita ɗau mataki,to ta ɗau matakin mana"
"Kee Bombee yaushe kika fara yin maganar manya da wannan rashin ladabin haka,karki dauki wannan halin ki saka ranki,hakan babu kyau musamman ga mace"
Cikin halin damuwa Daneji tafara yiwa Bombee nasiha dajan hankali. Tun bayan kwana uku dama ta kulada yanda Bombee tafara sauyawa,koyaushe tana cikin fushi,abu kaɗan idan akayi mata saita ɗaukeshi da zafi,sannan idan abun mugunta yafaru tafi kowa dariyar mugunta.
Jiya da ragon mlm Ahmadu ya sunkuci inna laari a kunkumi,data fara dariyah har faɗuwa saida tayi,sabanin da da idan hakan yafaru saidai tayiwa mutum sannu.
Tun a lokacin Daneji tafara kula dacewar ba lafiya ba,kwana tayi tana sallah da daddare,tareda kaiwa kukanta ga Allah,akan Allah ya kare mata rayuwar ƴar tata.
Muryar Bombee ce tadawo da ita cikin tunanin data tafi,wanda hakan yasa tayi zumbur ta kalli Bombee,wacce take kallonta da mamakin wane tunani take haka.
"Inna nasan kina iya ƙoƙarin ki wajen nuna min rayuwa,sannan kuma keda baba ku kaɗai kuke nunamin so kaman yanda iyaye kewa ɗansu,nasan kuma kin kulada canzawa ta a yanzu wanda nima naji,saidai babu yadda zanyi inaga yanxu ne yanda nake,ba yanda kuke son na zama ba dafarko.
Bazan boyemiki ba,amma daga yanxu kaff garinnan samun zaman lafiyar yaro shine kar yashiga harkata,bazan iya yimiki alƙawarin zan ƙyaleshi ba"
Tun kafin Daneji tabawa Bombee amsa taji sallamar gaji a cikin gidan,wacce tajita dumm a ƙirjinta kaman ganga.
Har ta fita tadawo wajen Bombee tareda yimata gargaɗin akan karta kuskura tafito komai taji.
"Salamu alaikum ina mutanen gidanne ina ta raraka sallama,ehh zakuyi shuru mana sabo dodanniyar ƴar ku taje zata kashemun yarinya a banza. To bilahillazi bazan yarda ba,ko ni ko ku ne a cikin garinnan,mlm Ahmadu yazo yanzunnan yabani kuɗin ɗori da kuma nasiyan magani"
Tana cikin zazzaga masifarne Daneji tafito daga ɗakin su Bombee tana kallonta.
Tsayawa tayi bata ce uffanba har saida gaji takai ayah a kan masifarta tukunna.
"Naji duk abinda kikace gaji,haƙika yarinya bata kyauta ba,amma inshaaallah za'a ja mata kunne,dan Allah ayi hakuri a sasanta a hankali"
"Sasanto? Ke kika sanshi nibansanshi ba,yanzu haka ma nasaka mlm idi ya nufi gidan mai anguwa yafaɗamasa,dan baza tabs yarda ba,wannan abu ke keganinsa ƙaramar magana,amma a wajena tafi dutsen dala"
"Haba gaji,menene na kaiwa ƙara kuma,abunnan fah yara ne suka aikata ba masu hankali ba,kuma inshaaallah zan ja mata kunne bazata sake shiga harkar ƴar ki ba daga yau"
"Hmmm ke kuma tashafa,nidai sai an biya kuɗi a radu,kuma wlh zata fito waje ai saina saka an babballamin ita,gayyar tsiyah kawai"
Tana gama faɗin hakan taja tsuka tareda yin hanyar zaure,zaninta a hannun sai kuncewa yake tana gyarawa.
Kafafun nan furuuru,kana ganinta kasan daga gaban murhu ta taso.
Sai wajen goshin la'asar kafin mlm Ahmdu ya shigo gidan,suna can wajen mai gari kan case ɗin karayar da Bombee tayiwa Zulaiha.
"Sannu mlm ka dawo?"
"Eh sai yanxu muka samu ƙurar ta lafah"
"To Allah ya kiyaye ta gaba,ka basu kuɗin gyaran ina?"
"Ban basu ba,cewa nayi bazan bada ba ai tsautsayine,sannan kaff anguwar nan babu wanda bai san irin izayar da ƴayan mlm idi ke ganwa Bombee ba tun tana ƙarama,haka mukayi shuru muka kauda idanuwan mu,sai yanzu kuma dan tayiwa ƴar su ace nabada kuɗi,suma suje suyi jinyarta suji idan da daɗi"
"Amma mlm bakace haka ba,kafi kowa sanin irin hatsarin dake tattareda yarinyar nan idan zata dunga ɗaukar hukunci,bai kamata muyi shuru bamuyiwa tufkar hanci ba,saboda da alama tafara warewa daga yanda muka tukata"
"Zancenki haƙƙune,amma to yakike ganin zamuyi,mlm Alwasu yariga ya faɗamana akan kar mu kuskura mu koma gareshi,amma zan leƙa ta wajensa nayi masa bayani,wataƙila bazai rasa wani abu dazayyi mana ba"
Shuru sukayi jugum kowa yana saƙa abu daban a ransa.
Saida aka ɗauki kwana uku ana case ɗin Zulaiha da Bombee kafim abin ya lafah,itadai an barta da ciwon hannu,babu damar zuwa makaranta.
Yanzu Bombee ta ɗan samu lafiya a wajen yan ajinsu. Tunda ga wannan lokacin Bombee ta daina kula kowa,koyaushe harkar gabanta take,makaranta ma ba hanya ɗaya suke bi da innayi ba,da alama inna laari ta gargaɗeta akan karta dunga shiga harkarta.
Saida akayi darasi ɗaya aka sakeyi kafin Bombee tashigo ajin,da alama wani wajen tabi ,dan tunda wuri innayi tashigo makarantar.
Batayiwa kowa magana ba ta nufi wajen zamanta,haɗa ido sukayi da Zulaiha wacce har yanzu hannunta yana saƙale da wuyanta.
Wani mungun murmushi Bombee tayiwa Zulaiha,mai ɗauke da gagarɗi a tareda.
Aikuwa da alama saƙon ta dake son isarwa ya isa inda takeso,don lokaci guda jikinta yafara rawa,tayi saurin sunkuyar da idonta.
Bombee tana zama taji muryar malaminnasu yana magana.
"Ke Bombee tashi ki fita daga ajinnan,dan iskanci sai yanzu kike zuwa makaranta"
"Kayi haƙuri mlm,innata ce ta aikeni,kuma anyimin horon makara a waje"
"Babu ruwana da wannan horon,ki fitamin a aji yanzu nan,dama ana faɗan ke hatsabibiya ce ashe dagaskene,dolema ki bar makarantar nan"
Kallon mlmin Bombee take,tareda yin tunani a ranta. Kenan shima dama baya ƙaunarta kaman sauran mutane,saboda tanada ilimi shiyasa yake kulata ashe,duk wannan tsawon lokacin kallon hatsabibiyah yakeyi mata.
"Shikenan mlm zan fita,amma kaman yanda na aikatawa Zulaiha yauma zanyiwa Abdul ɗan nursery 3 a hanyar tafiyah,inya tambayeni menene dalili saina ce jawo maka akayi.
Yanzu hakama idan na fita ƙiransa zanyi muyi wasa a can gefe"
Zaro ido malamin yayi jin Bombee ta ambaci sunan ɗan sa dayake ji dashi,yaushe yarinyar nan tazama haka?
Ya faɗa a ransa,zaman sa lafiya ya rabu da ita,idan takaryawa abdul ɗinsa hannu yau ya zaiji.
"Ahah babu komai koma kiyi zamanki ma,basai kin fita ba"
Jijjiga kai tayi tareda faɗaɗa murmushinta kana ta zauna.
Kamo hanyar gida tayi ita kaɗai,bata da abokiya ko kuma aboki,iya ƙanwarta ce,itama kuma anrabasu tun ranar da abinnan yafaru,bazata iya cigaba dajanta jikinta ba,bayan tasan basonta take ba.
Maganar bello taji a bayanta,wanda hakan yabata mamaki,musamman da taji da ita yake,rabonta dashi tun sanda yayi mata duka wancan watan.
"Ke ki tsaya a inda kike,hhhhh bantaba zaton yanda kike har zaki iya karya wani ma,waninma ƙanwata,ke wacece face dodanniya abar kawarwa. Bakiyi mamaki ba daban tareki ba kaman ko yaushe a hanyar gidanku,gaji ce ta hanani sumar dake tun wancan lokaci,saboda abinda kikayi yana sabo,amma yanzu zanga wazai ƙwaceki a wajena,mutuwa ma zaitayi shakkar ƙwatarki yau a wajena,saina saitamiki notin dayake son kuncewa a cikin kanki.
Duk maganar dayakeyi Bombee batace masa uffanba,sai binsa kawai take da idonta a duk lokacin dayaje ya zagayota.
Abinda bai kuladashi ba shine,yanzu idonta a tsaye yake babu alamar tsoro ko firgici sa'banin da,da yanzu ta tsugunna tana bashi haƙuri.
"Ohh ashe naga da alama har ƴar jarumta kika samo koh?"
Toshe hancinta tayi da hannunta tareda cewa.
"Banta'ba kulaba sai yau,ashe kai mungun ƙazami ne,bnada ɗoyi babu abinda kakeyi,ga baki a dafe kana yaro ƙarami ka fara shaye shaye,shayeshayen ma na ƙananan ɗan iska,banza shashasha."
Daga bellon har su sule shuru sukayi suna kallon Bombee,wacce ta kafe bello da ido tana zubamasa magana babu alamar tsoro.
Hannu ya ɗaga ya zanga mari mari a fuska.
Haka tayi ƙiƙim bata matsa daga inda take tsayeba,tofar da yawun dayake bakinta tayi mai haɗe da jini.
"Waifah irin wannan marin kakemin da sainaji tsoronka koh,ashe ma bakada ƙarfi,duk yunwa da sigari ta cinyeka,amma bari kaji nawa yayake?
Tun kafin yagama haddace mai tace a ƙwaƙwalwarsa yaji wani mari a kuncinsa,ba iya marin ba harda wani zafi daya jiyarceshi a wajen.
Tangal tangal yayi kafin yasamu ya cake,hannunsa yasaka a wajen tareda zaro ido lokacin dayayi arba a hannunsa,jinine jajur a hannunsa.
Hannayenta biyu ta saka a wuyansa,ta nutsa faratanta a wajen.
Ihu yasaka iya ƙarfinsa saboda ciwon daya ziyarceshi.
"Banfara ɗaukar mataki ba saida nashiryah,ko babban mutum idan yanason cin galaba a kaina bazai iya ba ballanta ku ƙananan ƙwari,kusaka a ranku bazaku iyah cin galaba a kaina ba ko kaɗan,mai son gwadawa kuma ga wajenan,mai tsoro ka fasa"
Sakin wuyannasa tayi,ta barshi a tsugunne yana tarin wahala,kan kaceme jini ya wanke gefen rigarsa inda ta karzamasa zanen faratunta.
"Ana zugaka shugaban yara,nibanga sarauta anan ba,dan haka na karbi sarautar daga yau,ko kanaso ko baka so ka bani matsayinka,Sannan babban jan kunne kar kowa yasake ɗagamin yatsa cikinku,idan kunji kun tsira"
Tana maganar tana fita cikin murya kaman ba tata ba,sannan kuma tanayi tana wata irin dariyah kaman shaiɗaniya.
Kallon sule tayi wanda tun ɗazu ya jefar da bulalar take hannunsa ta dukan Bombee ɗin.
"Ka tahomin da jakata gida,sannan duk wanda yakeda niyyar ɗaukar mataki akaina shima kada ya fasa"
Daga haka ta bar lungun ta nufi gidansu.🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are
YOU ARE READING
BAƘAR AYAH
Action..........."Hajiya kar burin ɗaukar fansa ya shiga ranki,ki kasa gane wane irin makami kike son sokawa kanki da kuma danginki. Kawota cikin zuri'arki tabbas zata magancemiki Masifar da kike ciki,saidai kina ƙoƙarin korar macijiyane da wata macijiyar...