Chapter 1

15 2 0
                                    

Aisha galadima
*Fulani shatu*
Bakatsina ❤️💯

Assalamu Alaikum
Wannan littafi kagagge ne banyi dan wata/wani ba.
Allah ya bani ikon gama shi lafia
Ameen
Taku a koda yaushe yar mutan katsinawa 📝❤️.

(1)
Mommy I'm coming cewar wata yarinya tana saukowa daga stairs sanye take cikin body hug pink colour da jeans black ,kafar nan tasha pink sneakers wanda daga saman shoes din leg chain ne jere wanda ya kawata kafar, ida saukowa tayi na qare mata kallo black beauty ce mai madaidaicin eyes wanda lashes suka kwata sosai eye ball dinta brown ne wanda suka kara ma idon kyau and her nose is so MashaAllah dai dai, lips dinta shima so cute sai shinning yake dagani ta shafa masu lip gloss, girarta cikakka wadda kalo daya zakayi mata kayi tunanin caving dinta akayi sai dai haka Allah yayi mata ita, black scarf ne a kanta wanda aka jashi baya, wani kwantaccen gashi ne yayi luf farkon head dinta, hannunta na kalla naga tana danna wayarta qirar iphone 13 pro, sauri take amma ba zaka gane hakan ba sai wanda ya santa, hanyar kitchen tayi tana kiran mommy gani , harara mommyn tayi tana cewa yanzu AIZA komi naki ba zakiyi cikin sauri ba tun yaushe nake kiranki kina ceman gaki nan sai ynz kika sauko almost 30 minutes kenan fa, ina maki addu'a Allah ya rabaki da nawar nan haba mutum komi nashi a hankali kamar baki da lakka eyeeee, shiru tayi dan tasan tayi laifi, muryar daddy taji alamun zai shigo kitchen din yana fadin waya tabaman daughter na haka tunda safen nan, mommy ta kalleshi time din da ya ida shigowa kitchen din tace Abba tun dazu nake kiranta fa tazo mu hada breakfast din nan amma tayi halin nata, murmushi daddy yayi yana cewa zonan daughter, AIZA tayi saurin zuwa tayi ma daddy side hug tace good morning my one and only daddy! Chicks dinta daddy yaja yana amsa mata morning angel, how are you? Hope you slept well? Sake rankwafowa tayi ta gefen daddy tace Sure daddy , I'm good alhamdulillah , daga haka suka cigaba da hada breakfast din hada daddy suna yi suna fira abun zarrr burgewa, kana ganinsu kasan happy family ne.
                   After sun gama breakfast din suna zaune saman dining AIZA tace daddy ina son naje holliday wurin Aunty sophy please daddy don't say NO please! Kallonta mommy tayi tace ke baki gajia da tafia ne i think ko 2month ba'ayi ba kikaje bauchi ynz kuma zaki tsiro da wata tafia, ai laifin Abba ne da yake biye maki , Ynz ita kanta Sophia din jiya da mukayi waya tace man end of this month zasu zo saboda Hajia tace ta gaji da zama acan kuma , daria suka sa har daddy yana cewa ai hajjaju sai ita nan ta damu a kaita wurin diyarta tunda mu bamu sonta kuma ynz har angaji ko 3 month ba'ayi da tafiyarta ba fa, daria Aiza tasa tace daddy kasan halinta fa ni ranar nan dana kira YA ABUL  nace ya hada ni da granny qin yarda tayi wai tayi fushi...shiyasa nake so naje sai mu dawo tare dasu , Mommy tace ai gara dai kizo ki wuce school din nan da tafiye tafiye din nan haba, Abba yace sai kin fi kowa kewarta idan ta tafi nan zaki zo kina cewa Abba AIZA dai shiru yaushe zasu samu holiday ? Daria aka sa har mommy din tana cewa ita ba zatayi ba.
AIZA ce zaune saman gado tana sanye da pajamas dinta tana chat alamu sun nuna tana jindadin chat din, mommy ce ta shigo tace mata gobe ta fito da wuri zasuyi snacks wanda zata tafi da shi bauchi, tohm mommy InshaAllah rufe kofar mommy tayi ta tafi part din daddy, ta gama chat din ta sauka ta shiga toilet ta fito da alamun ruwa a fuskarta wanda ke nuni da Alwala tayi, Carpet ta shinfida ta saka dogon hijab dinta ta kabbara sallah tayi Shafa'i da wutir sannan tayi dogon addu'a ta kwashe carpet din ta kashe light din dakin ta kwanta abunta.

Story of a young girlWhere stories live. Discover now