Chapter (3)

3 2 0
                                    

(Bauchi)
Dukansu zaune suke ana ta fira hada Abba( mijin aunty sophia) da ABUL daya dawo daga aiki ana fira, ABUL sai aika ma AIZA wani kallo yake wanda ita batasan yanayi bama zaune take Moha ya daura kanshi a saman cinyarta yana game a wayarta, hajja ce tayi gyaran murya tace toh AIZATU goben zamu juya tare da ummaru ko? Kallon kallo aka fara cikin parlour din Mama tayi saurin cewa hajja ki bari ending month din nan sai mu tafi gaba daya, wani kallo hajja ta maka ma mama tace amma dai sahia kin rainani minene kuma enti mant (ending month) , mama na murmushi tace hajja karshen watan nan kinga ya kusa karewa sai mu tafi gaba daya, tashi kawai hajja tayi ta tafi dakinta, a hankali kowa ya tashi ya fara tafia dakinshi, mama na tashi ABUL ya taso ya dawo wurin AIZA fira suka cigaba basu suka tashi ba har sai wurin 12 sannan suka tafi suka kwanta.

Haka dai rayuwar ta kasance ma AIZA a bauchi wata irin shakuwa ta kara shiga tsakaninta da ABUL har aiki take raka shi, ya kaita wurare sosai a bauchi har yankari sunje tayi enjoying zuwan nan sosai.
Motocci ne jere a farfajiyar gidan jibgajibga guda 2 , ABUL ne zaune a driver seat gefenshi kuma AIZA ce baya kuma moha ne , dayar motar kuma Hajja ce, Mama dasu fatima da Aisha sai driver da zai kaisu bude masu wangalelen gate din akai suka kutsa kai saman titi sai muce Allah ya kaisu lafia.
Tafia akayi mai dadi AIZA da ABUL suna fira hankalinsu kwance ko nisan tafiyar basuji bana duk da suna tsayawa su kayi sallah da cin abinci , basu suka iso ba sai bayan magrib, bayan sunyi sallah aka ci abinci akayi fira sai aka nufi part din hajja su momma anan suke kwana suna da daki a part din hajja din, fatima da Aisha kuma dakin AIZA suka ce zasu kwana, YA ABUL kuma dama yana da daki anan part dinmu can ya tafi.
Bayan kwana 4 su momma suka tafi, AIZA hada kuka because shine ganin da zata masu sai kuma tazo hutu nigeria saboda next month zata tafi school, hawaye take ABUL ya ciro handkerchief a share mata hawaye yace mat zai dawo kafin ta tafi shi zai kaita Airport ma, dadi ne ya kamata sai tayi shiru a haka Daddy, Mommy , Hajja da AIZA sukayi ta masu waving har suka fice daga gidan.

Tafia ta tashi sai shirye shirye take taje katsina ta dawo, gobe zata tafi ta kira ya Abul yace mata ba zai samu zuwa ba katse wayar tayi tana hawaye, ita bata son soyayya ba amma ta dauki ABUL wani part na jikinta tana girmamashi yana shagwabata sosai mutane da yawa na masu kallon masoya amma su a wurinsu ba haka bane, knocking kofarta taji anayi tace come in , kara knocking din akayi ta tashi a zuciye taga wanene wannan kuma tana bude taga AbUL tsaye bata son time din da tayi hugging dinshi ba sai hawaye kuma, lallashi yayi sannan ya kama hannunta zuwa parlour, mommy ce zaune tana waya suka shigo kallo tsaya ta masu ta dauke kai ta cigaba da wayarta hanyar dining sukayi yaja mata kujera ta zauna ya zuba mata abinci shima ya zauna ya zuba suka cigaba da cin abincin, after sun gama part din hajja suka tafi hada mommy can suka iske daddy nan akayi ta fira har dare anan AIZA tace zata kwana wurin hajjarta nan aka barsu suka tafi.
Da safe kallo daya zakyi ma AIZA kasan tasha kuka flight din 9 zata bi zuwa California,
Su duka gidan suka rakata airport din zata shiga departure anan suka tsaya hawaye take sosai ta rungume mommy , mommy itama riqewa kawai take amma itama kamar tayi kuka, wurin daddy taje shima tyi hugging dinshi tana kuka ya share mata hawaye yace nan da 2 weeks zanzo kinji ko so kada ki damu okay, gyada mashi kai tayi taje tayi hugging din hajja itama addu'a tayi mata sannan taje wurin ABUL tsayawa tayi ta kalleshi sai kuma ta fada jikinshi wani kukan ta sake saki lallashinta yayi a haka ta shige tana waiwayensu tana hawaye , ta saba zuwa country's da dama amma ba ita kadai ba ita dadu daddy da mommy shiyasa taji wannan tafiyar different.

              (Los Angeles International Airport )
Tafia take tana danna wayarta trolley dinta tana janta hankalinta na akan wayar taji ta buge wata mata saurin dagowa tayi tace sorry mah, sai taga matar tace bakomai diyata, she was so surprise da taji hausa bakin matar, a haka matar ta wuce itama ta wuce ta shiga chab sai gidansu da yake anan kasar, tana zuwa Juliet tazo da sauri ta anshi trolley din suka
shiga gidan wanda yake abun burgewa daga wajen gidan mota ce guda 1 cikin tint dinta.
Parlour din ta zauna juliet ta kai mata kayanta a dakinta ta dawo tana mata sannu da zuwa, amsawa tayi ta tashi ta shiga dakinta ta shiga wanka ta dauro alwala tazo ta rama sallolin da suka wuce mata, wayarta ta dauko ta chanja sim dinta ta kira daddy tace ta iso suka gaisa da mommy sannan ta kira Abul shima aje wayar tayi ta tashi ta shirya cikin wata gown alamu dai ta barci ce iyakarta gwuiwa batasa scarf ba dogon gashinta ya bayyana sai sheki da kamshi yake dining area ta wuce juliet ta gabatar mata da abinci taci tasha ruwa ta mike tace ma juliet  I'm exhausted, I'll see you tomorrow morning goodnight, daga haka ta wuce ta kwanta.

Sai bayan 1 week bayan ta huta ta fara shiga school sun fara lectures alhamdulillah kuma tana ganewa sosai.
     
                           (Stanford university)
Zaune take cikin car dinta tana ta kallon students nata kai da kawowa, numfashi taja kafin ta bude car din ta fito, wani irin kyau naga ta kara tana sanye cikin Abaya blue colour , kafarta na kalla naga tana sanye ta leg chain dinta guda 2 silver and gold wanda yake kara ma kafarta kyau, sanye take cikin gucci flat shoe hannunta riqe da wani hardcover sunglass ne wanda ya kwata fuskarta da shi wani kofa naga ta nufa , tana shiga naga ashe hall ne students ne zaune kowa na harkar gabanshi, wuri ta samu ta zauna bayan ta zauna lecturer ya shigo suka fara daukar lecture.

Story of a young girlWhere stories live. Discover now