Chapter (4)

4 2 0
                                    

Sauri take ta fito cikin shigar hausawa sake duba wristwatch dinta tayi tayi tsoki tace nasan ma ya shiga , wurin motar ta taje ta shiga ta bata wuta sai school, tana zuwa ta iske ana ta lectures haka ta shiga all eyes on her abunda bataso kenan dama, bayan angama lectures din ta fito ita da wata friend dinta Ameesha fira suke har suka iso wurin da tayi parking car dinta mamaki ne ya kamata ganin motar fess kallon motar take sosai ita dai tasan jiya bayan ta dawo daga motar tayi kura kuma bata kai ta car wash ba , haka dai ta shiga suka wuce ta aje Ameesha gida ta wuce gida, tana shiga ta kira jessica ko ta kai mata mota car wash tace a'a , tayi mamaki sosai sai ta share ta wuce daki kawai, da daddare ta shirya cikin wani palazzo black tasa top white, tasa veil ta nade kanta ta dauki car key dinta da wayarta da side bag dinta ta fito sai kamshi take gaskia AIZA classy babe ce, tana fitowa tace ma jessica tazo su wuce, wani babban restaurant ne sukaje suka zauna , Wani murya taji ta ce masu good evening beautiful ladies here is the menu, dagowa tayi like ascent dinshi kamar bahaushe , dagowa tayi taga fuskarshi marks ne ko eyes dinshi ba'a gani saboda p-cap din da ya matso da ita sosai, ansa tayi order abunda tke so jessica ma haka, aka kawo masu suka ci suka gama suka wuce taso ta kara ganin mutumin nan Amma har suka fita bata ganshi ba.
After 3 month zaune AIZA take a balcony tana waya hankali kwance wurin yana da dadin zama daga gefe garden ne , hango wani giant mutum tayi yana tunkarar motarta katse wayar tayi taga ikon Allah hangoshi tayi yana ta kakkabe motar sai taga kuma yana wanke motar , she is speechless after all lokacin nan dama shi yake wanke mata mota bata taba ganinshi ba, sai da ta bari ya kusa gamawa sai tayi murmushi taje wurin da yake tace Hi gentleman, juyowa yayi ya kalleta ya dauke kai yace Hello ya cigaba da aikin da yake , kallonshi take kamar ta taba ganinshi kuma muryarshi ma haka ta rasa gane inda ta sanshi ,fuskarshi take so tagani amma marks din fuskarshi ya hana gefe taja ta tsaya har ya gama zai juya ta tafi ta tare shi tace wait please! Tsayawa yayi har ta iso ta kalleshi idanunshi kadai take gani wanda suke da matukar kyau MashaAllah, tace Thank you so much but please dont go ina zuwa tafiya tayi ta shiga cikin gidan kafin ta fito ta iske wayam, tsayawa tayi tana matukar mamaki , wannan wane irin mutum ne a hka ta juya ta koma gida.

Ranar sunday tana assignment a study room dinta ta window taga kamar Mr.marks kamar yarda take ce mashi idan ya fado mata a rai kuma har yau wani time din sai dai ta fito taga Motar ta wanke fess but bata ganinshi tun time din nan, tashi tayi ta fita da gudu amma bata ganshi ba haushi ne ya kamata ta juya kenan ta ganshi tsaye a gabanta tsoro ya kamata ta tafi zata  fadi ya riqo ta da sauri ya tsayar da ita, yace mata lafia kike nemana she was so surprise da taji hausa tace tohm shine sai ka tsoratar dani shiru yayi yana kallonta, juyawa yayi zai tafi tayi saurin riqo shi tace please kazo mu shiga ciki muyi magana please please, tsayawa yayi tana kallon yar yarinyar nan sake ni ya fada a dake, sakin hannun tayi tace please, ok yace tsalle tayi suka shiga gidan zama yayi a kujeara yace Are you alone? Nodding kanta tayi tana kwala kiran jessica, jessica ta fito ta gaishe shi ta koma ta kawo mashi drinks ta koma, kallonta yayi yace uhmm! Zama AIZA tayi tace please yaya ka cire marks dinka mana, wani kallon ya mata yace lafia kike nemana, saurin saukowa tayi ta zauna kasa tace inaso na mka godia ne fa kuma ban qara ganinka ba, yace it's ok, yauwa yaya please daga Nigeria kake, nodding kanshi yayi tausayi ya kamata tana tunanin maybe irin mutanen nigeria ne wanda suke zuwa aiki a kasashe, tashi yayi zai tafi tayi saurin ce mashi ai baka sha komai ba, I'm ok ai ya tashi ya fita ta biyo shi tace yaya please zaka na zuwa muna gaisawa ko? Yace maybe yayi gaba tana kiranshi ya juyo yace point of correction I'm not your yaya so stop calling me this name ok , yayi gaba abunshi ya barta tsaye har ta daina ganinshi, wai wannan wane irin mutum ne.

              Tun daga ranar bata kara ganinshi ba harsu daddy da mommy sunzo sun koma, haka rayuwa ta shigaba da tafia school dinsu ma yana ta tafia dai dai exams zasu fara kowa hankalinshi naga karatu ba wasa.
Cikin ikon Allah su ka gama exams dinsu lafia zataje holiday gida amma daddy yace ta bari sai next hutu da zasu sake saboda wannan duka 2 weeks ne haka ta hakura ta cigaba da hutunta a gida.
Taje wurare da dama cikin hutun ta ita da jessica sunje disneyland park,santa barbara da sauran wurare dai.
Ranar nan tana zaune a garden tana rubutu a diary dinta ranar gaba daya kewar family dinta ya kamata tana rubutawa tana kuka, tafiya taji a bayanta taqi dagowa maybe tasan jessica ce, tsayawa taji anyi dai dai kanta dagowa tayi ga idonta da hawaye taga Mr.marks saurin goge idonta tayi wani dadi ya kamata at lest dai taga dan nigeria tashi tayi tace you're welcome bro, zama yayi a chair din da ke facing dinta yace how are you? I'm good alhamdulillah shine tun ranar baka kara zuwa ba ? Shiru yayi mata ya miqa mata chocolate ansa tayi ta mashi godia , yace miyasa kike kuka ai kamar jira yake ta fashe da kuka tace I'm missing my family, shiru yayi sai can kasan makoshin shi yace "sorry" fira sukayi sosai amma duk yarda taso ya bata labarinshi yaqi sunanshi kadai ya fadamata MAHER suna zaune time din magrib yayi suka shiga ciki yayi alwala ta shinfida mashi carpet, ita kuma ta shige daki tayi tata sallah din tun daga ranar sai yana zuwa wurinta suna fita yawo kuma yana qara mata karatu na islama wani time din duka yan gidansu AIZA kowa ya son MAHER har video call sunayi dasu daddy idan sun hadu, ranar da ta fara ganin fuskar MAHER tayi mamaki sosai da yace mata dan nigeria ne he's damn handsome MashaAllah, komai yaji😂.

Ranar nan take tambayarshi miyasa yake wanke mata car, he smile sannan yace sana'a tace ai, kallonshi tayi tana mamakin tace amma baka ansar komai yace saboda ke yar kasa tace, kinsan AIZA ina aiki a restaurant , car wash, mall and wurare da dama dai,tausayi ya bata tace amma Ya MAHER miya kawo ka nan ne yace mata karatu mana, ni kinga yaron talaka ne na samu scholarship tohm tunda muka zo sai komai ya chanja so you have to hustle idan kana son karatu saboda kai zaka biya shine nake Sana'ar nan, hawaye ne suka zubo ma AIZA tace ka daina daga yau zan fadama daddy, murmushi ya mata mai tsada yace a'a AIZA ki barshi ba gashi ba har na gama masters dina saura kadan kinga kawai ki barshi idan kinsan zaki fadama daddy ma da ban fadamaki ba tun farko, hakuri ta bashi tace ba zata fada mashi ba sannan suka cigaba da fira.
Bayan sun rabu har ta kwanta ta dauki wayarta tana kallon hotansu wanda sukayi a Palm Springs yayi kyau sosai, tunani ta fada MAHER baiyi kama da talaka ba kamar yarda ya fadi ba , skin dinshi yarda yake glowing kamar yaron masu kudi and attitude dinshi kamar wanda ya fito daga gidan sarauta haka nan taji kamar akwai abunda yake boye mata.

Story of a young girlWhere stories live. Discover now