Chapter (2)

7 2 0
                                    

Alhaji  Auwal Sanam sanannan mutum ne a fadin nigeria dan kasuwa ne kuma yana taba siyasa shiyasa sunanshi yayi kaurin suna a Nigeria da kewayenta , Matarshi Daya Hajia Aisha da diyarsu daya tal AIZA , Maaifiyarshi tana nan da rai hajja Fatima wadda suke kira da hajia , mahaifinshi Allah ya mashi rasuwa da dadewa tun kanwarshi tana shekara 8 a rayuwa , hajia Sophia ita kadai ce kanwarshi tana aure a bauchi da yaranta 4 Abubakar (ABUL) , Fatima, Muhammad da auta Aisha.
Hajia Aisha (mommy) iyayenta nan da ransu mutanen katsina ne, Malam  Abdullahi sunan mahaifinta sananne ne a garin katsina malamin addine ne sosai farin tsoho mai farar aniya kenan lakabin da mutane ke mashi kenan, Hajia Rukayyah tsohuwa mai ran karfe kenan suna da yara 5 , Alhaji Ismail , Alhaji Bashir, Alhaji Abdulmalik, Hajia Ni'imatu Da Hajia Aisha (mommy) sune yaran da Allah ya azurta su da su duka a garin katsina suke aure sai Hajia Aisha( mommy) da take aure a Abuja.

                (Abuja)
Tsaye suke a katafaren parking space din wanda cars 5 ke ciki, AIZA ce tsaye cikin shigar turkey Abaya black ta rataye side bag a hannunta dayan hannunta kuma trolley ce riqe tana magana da Malam umarru driver , mommy ce da daddy cikin shiga ta alfarma , riqe suke da wasu warmers masu kyau da gani kudi sun koka aciki, malam ummaru bude boot din motar yayi yazo ya anshi kayan da ke hannun su daddy yasa sannan yazo ya anshi trolley din hannun AIZA ya saka shima, side hug taje tayi ma daddy da mommy tace mun tafi sai mun dawo Allah ya tsare su daddy sukayi masu ta shiga motar malam ummaru yaja gate man ya wangale masu katoton gate din suka fice.

                 BAUCHI
Motarsu ce ta kutsa cikin gidan wanda yaji kyau har ya gaji...Motar na tsayawa AIZA ta sauko kallo daya zaka mata ka gane ta gaji sai ya mutsa fuska take, malam ummaru bari  in shiga zanyi magana a kawo maka abinci ka huta , tohm rankiyadade, shiga tayi parlour din tana sallama duka mutanen da ke prlour din suka jiyo suna facing din kofa with surprise a saman face dinsu suke amsawa auta Aisha ce ta rugo ita da fatima sukayi hugging dinta suna fadin yA AIZA wannan surprise haka baki fadi zaki zo ba, murmushi AIZA tayi tace surprise nake so na baku, ida shigowa sukayi cikin parlour din Mama sai murna take tana mata sannu da zuwa , wuri ta samu ta zauna ta gaishe da mama, Ina  Hajja ne naji gidan tsit ko bata nan ne, daga wani daki sukaji ana cewa Ehh dama hajja uwar surutu ai ina daki dole aji gida shiru, murmushi duka parlour din aka dauka tashi AIZA tayi taje tayi hugging din yar tsohuwar da ke sanye da wani lace wanda kallo daya zaka  mashi ka gane yaji kudinshi, Haba hajja ta i missed you wallah AIZA ta fada murmushi a fuskarta kuma taqi sakin tsohuwar, jama'a ku kamani kar wannan abun ya kadani, wai wacece ma tukun zaki zo ki sabauta ni ne? Qara makalkaleta AIZA tayi tace I'm sorry hajja ta gani nazo ai, daria hajja tasa tace ahtoh ai nasa kun yafe ni ne keda iyayenki, kama hannun hajja tayi sukaje suka zauna ka shiga fira , hajja tace sallah fa, AIZA tace hajja ai mun tsaya mosque munyi sallah a kaima malam ummaru abinci a nuna mashi inda zai huta gobe zai juya , tashi fatima tayi ta kawo mata abinci tace ba ynz ba sai anjima, ta fita ta kaima malam ummaru abincin aka nuna mashi inda zai huta, mama wai inasu YA ABUL ne da Moha ne, Aisha tace ai ya Abul yana aiki moha kuma barci yake baya jindadi, Ayyah Allah ya bada lafia, fira suka shigaba sai ga masu aikin na shigowa da kayan dasu AIZA suka zo da shi, Trolley din Fatima taja ta kai dakin AIZA din wanda idan tazo take sauka, Warmers din kuma aka aje su nan parlour, hajja tace mi nake gani haka kamar ance nan din da yunwa ake bari na ne? Bude warmers din tayi dayan bayan daya sai kuma tace Allah sarki Aisha yar aljanna ta iya kama kafar surukkai toh nima dama tuni na fidda ta daga suruka ta koma diyata yoo Allah na tuba kodan Qawata hajia rukayyah ai kunga ta zama diyata ko? Kowa na dakin kallonta yake yana murmushi saboda ansan halin hajja.

Story of a young girlWhere stories live. Discover now