Na
*ASMY B ALIYU*
Da
*HAJJA CE 👈*PAID BOOK.... #(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta 08086207764*Katin waya na MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp.*
*Free Page 1*
Yau tun ƙarfe bakwai tayi shirin zuwa school kasancewar ranar monday ce, Ummi ta fito daga kitchen tana kallon Rahama dake tsaye tana kallon Ra'is dake breakfast a hankali. Da mamaki Ummi ke fadin. "Ke bazaki yi breakfast ɗin bane kin tsaya masa aka.?" Ta turo baki tana fadin. "Munyi latti Ummi idan naje school zanyi." Ummi ta tabe baki tana faɗin. "Toh ki zauna ya gama mana." Ra'is ya kalli Ummin nasu da sauri yana faɗin "Duk tabi ta dameni Ummi, dakyar nake turasa." Ra'is ya faɗa cike da jin haushin Rahama cikin muryarsa ta yara dan shine ƙarami. Yana da kusan 10 year's ita kuma tanada 13 year's, shekara ukku ne a tsakanin su. Nan da nan suka fita gate ɗin gidan. Da sauri ta kalli Adamu driver ta marairace masa tana fadin "Dan Allah Yaya Adamu kabari na gansa minti goma yayi yawa." A fusace Ra'is ke faɗin. "Wallahi idan kika tafi tafiyar mu zamu yi, sai dai shi wanda zakije wajan nasa ya kai ki. Idan kuma Abbah ya fito ya ganki cikin motarsa kinsan kasheki zai yi." Ya faɗa yana wani haɗe rai. Wani kallo ta shiga yiwa Ra'is tana faɗin. "Kai! Ba dai ni kake yiwa rashin kunya ba? kaga wanda xai tayaka home work." Ra'is ya wani yakune fuska yana faɗin. "Shikenan kije kiyi sauri kizo mu tafi." Da sauri ta ɓalle marfin motar dama tana zaune a baya Ra'is da driver kuma na zaune a gaba. Da gudu ta nufi gate ɗin gidan su Imran Matawalle.
Hangota maigadin gidan yai ya haɗe rai yana faɗa aransa cewar. Allah ya waddaran naka ya lalace, idan banda iskanci yarinya kullum sai taje ɗakinsa? Allah kadai yasan lagudar da yake yi mata tunda shima Imran ɗin kowa ya shaidesa cewar ɗan iskane. Tayi knocking gate ɗin ya leƙa, Mai gadin yana ganinta ya haɗe rai yana cewa. "Ke sabida tsabar rashin tarbiya ba makaranta zaki tafi ba?" Ta juya ido tana fadin. "Ina ruwan ka? ka buɗe min ƙofar wallahi ko nayi maka sharri a wurinsa, kadai san halinsa sarai." Maigadi ya mata mugun kallo dan yasan zata iya, kuma yasan Imran ɗin akanta zai iya yi masa rashin mutunci, akan hakama zai iya barin aikinsa. Washe baki tayi ganin ya buɗe mata ƙofar, kai tsaye ta nufi part ɗinsa wanda shine a farkon gidan.
Jin yarda ake danna door bell ɗinsa kaɗai yasan aikin Rahama ne, gashi jiya sai biyu na dare ya shigo gida sabida sunyi taron wani birthday party ɗin wani abokinsa. Farar vest ce ajikinsa da kuma boxer haka ya sauko down stairs ya nufi ƙofar ya buɗe mata. Ta kallesa sama da ƙasa, shaye da toka ta shiga cikin parlornsa. Ta gaishesa tamkar bata so, kafin ta ɗora da faɗin. "Bakayi sallah ba Right?ƙarfe nawa yanzu dan Allah.?" Ta faɗa cikin sanyi murya. Kallonta kurum yake yarda uniform ɗin dake jikinta sukai yi mata wani mugun kyau, suka fito da kyakkyawar farar fuskarta. Ta mike tsaye ta nufi ƙofa a fusace lokaci ɗaya taji ya fisgota ta dawo gabansa. Ƙoƙarin kwace hannunta take ya mata rikon da bazata iya kwacewa ba. Wani abu yake jin yana fisgarsa game da ita, ya ware mata ido yana fadin. "Tell me duka fushin na menene?" Ta turo baki tana faɗin. "Bakayi sallah ba." Ya ɗage gira yana fadin. "Toh ai yanzu zanyi shikenan?" Ta ɗage kafaɗa tana cewa. "Yanxu sai da rana ta fito zakayi sallah? bakajin kunya kai?" Ta faɗa tana kallon cikin idanunsa. Ya saki hannunta yana shafa sumar kansa mai kama da ta larabawan asali yana faɗi mata"Sowiee zanxo na ɗaukeki idan kuka tashi daga school." Ta juya ta nufi ƙofa tana turo masa baki yasan tunda bata amsa masaba fushi tayi, har tabar cikin parlon idonsa na kanta.
Juyawa yai ya shiga bathroom, sai da ya fara yin toilet sannan yai wanka har zai fito ya tuna beyi alwala ba ya koma yayi yana tunawa da yanayin yadda Rahama ta fita dan kawai bai yi sallah ba. Shiryawa yayi cikin riga white da wando jeans red colour yaje ya hau kan sallaya, ko five seconds beyi ba harya idar, babu wani addu'a bare salatin annabi kawai ya tashi ya nufi wajan mirror. Sumar kansa ya shiga gyarawa cikin style kala-kala, duk wacce yai sai yaga sam batayi masa kyau ba, yaja tsaki lokacin daya yamutsa sumar, yasa mataji ya taje tare da fesa turaruka wanda sunfi kala shida. Yana gamawa Side ɗin Mommy ya nufa yana jefa car key ɗinsa sama yana cafewa. Mommy na zaune falo cikin farar soofa, gefenta gas meat ne tana ci da teethpath, Imran Matawalle ya ƙarasa ciki yana gaisheta. "Good morning Mom." Sai da ta ƙare masa kallo shaye da toka ta amsa tana cewa. "Meya hanaka zuwa jiya da daddare ka kawo min medical glasses ɗin Bassam?" Imran Matawalle ya shafa kai be kalli fuskar Mom ɗin ba yace. "Ban dawo da wuri ba, saboda mun daɗe a wajan birthday party " Ta jefeshi da wani banzan kallo. "Oya tashi kaje ka kawo min." Imran yace. "Sorry Mom banje asibitin ba but yanzu zanje na karbo miki." Cikin bacin rai Mommy ke kallansa. "How dare u zan sakaka abu kakiyi Imran? Naga alamar tunda kasan bani na haifekaba kake min iskancin da kaga dama, this is the last warning da zan aikeka bakaje akan lokaci ba Imran." Mommy ta ƙarasa faɗa cikin masifa. "Sorry Mommy zanje idan na fita." Bata kulashi ba kawai taci gaba dacin gas meat ɗin. Miƙewa Imran yai ya fita daga side ɗin, kai tsaye ya nufi mota zai shiga yaji muryar mahaifinsa yana kiransa. Ya juya ya ƙarasa wajansa suka shiga cikin parlorn shi.
Cike da nuna soyayya da kulawa senator Bashir Matawalle ya kalli gudan jininsa yana faɗin. "Kayi breakfast kuwa?" Imran ya ɗaga kafaɗa bece komai ba, Alhaji Matawalle ya kamo hannunsa, wajan dining suka isa inda aka gama jera komai naci dasha. Waya Imran ya ɗakko ya shiga dannawa, da kanshi ya shiga haɗa masa tea kamar wani ƙaramin yaro yana ce masa. "Kadena zama da yunwa my son." Imran ya kalleshi cikin yanayin na shagwaɓa yana faɗin. "Daddy ina san kuɗi, I mean account ɗina is too low kuma ina da uzuri." Tea ɗin ya miƙa masa, karɓa yai besha ba ya ajiye yanaci gaba da latsa wayarsa.
"Zan tura maka my son, yanzu dai kayi breakfast." Tea ɗin ya ɗauka duk da ba so yake yi ba, burinsa kawai ya fita yaje yasha beer ko zai samu nutsuwa, masifar Mommy ta ɗazu ba ƙaramar kona masa rai tayi ba. Matawalle ya kalli Imran yana shafar gashin kansa. "Son kana da damuwa ne? Tell me kasan bana san damuwarka." Imran ya miƙe tsaye yana dire tea cup ɗin, sai da ya fara tafiya yace. "Bakomai Daddy kawai dai ka turo min kuɗin." Ko jiran amsa Imran beyi ba ya fito ya shiga mota, securities suka shiga tasu da nufin yi masa convoy, shaye da toka Imran ke faɗin. "No need please zan fita ni ɗaya." Yaja motarsa yabar gidan.*****
Dai-dai wani katon joint Imran Matawalle yai perking motarsa, Al-Amin ya kirawo a waya, yana dagawa, "Yeah kana ina?" Al-Amin cikin wani irin yanayi yace. "Ya akai?" Rai bace Imran yaja tsaki. "Dalla banza ya za'ai ina tambayarka zaka wani ce min ya akai? Kana ina nace?" Al-Amin ya ture Merry dake saman cikinsa yana cewa. "Ina club tun jiya." Imran bece komai ba, wayar ya ajiye ya kunna motar, kai tsaye ya nufi wajan Al-Amin ɗin. Shi kuma yana gama wayar ya kalli Merry, bandir ɗin 200 ya cilla mata yana fadin. "Kama hanya ki fita kafin wannan ya shigo ya ganki, baya san wannan harkar da nakeyi daku." Merry ta shiga girgiza masa kirji ya shareta dan baya san Imran Matawalle yazo ya sameshi da mace a ɗakin. Cikin sauri tasa kayanta ta fice, shi kuma ya shiga bathroom ya watsa ruwa shaf-shaf ya maida kayansa.
Shaye da toka Imran yake bin Al-Amin da kallo, "Hope akwai abin sha a ɗakin?" Cewar Imran yana buɗe wani mini fridge dake cikin ɗakin. "Half bottle ne idan kana so." Al-Amin ya faɗa yana ɗakko kwalbar giyar da suka rage jiya bayan an gama birthday party. "Nace maka zanzo, shine dan wulakanci baka tanadar min ba sai ragowa?" Al-Amin ya kalleshi da mamaki, sai kuma ya kasa magana, so yai yace bazai tanada ba, dan yaga kamar Imran ɗin yana son mayar dashi banza. "Ina so nasha yanzu kafin naje hospital."
Al-Amin ya tambaye shi "Hospital I Matawalle? Kayi me?" Imran yace. "Mommy ta matsa, ta takura ni wallahi, ace duk mutanan gidan nan da securities da masu aiki, but ni takeso naje na karɓowa Bassam glasses ɗin sa, can you imagine Al-Amin Ɗankwambo?" Suka shiga juya maganar a tsakaninsu. "Mom tana so ta nuna maka cewa ita ɗin Mommy ce, that's why kila take sakayin wasu abubuwan da masu aiki ne ya kamata suyi bakai ba." Imran yaja tsaki tare da faɗin. "Kuma bazanje ba wallahi, katashi ka samo min abin sha dan ƙarfe ɗaya zanje school ɗin su Rahama na ɗauketa." Cikin dariya Al-Amin yace. "Baka tsaron aje a gayawa A Galadanci?" Imran shaye da toka yace. "Kaima zaka iya zuwa ka gaya masa." Al-Amin yayi dariya tare da ficewa ya karɓo musu kwalaben beer ya koma, jikin Imran Matawalle har tsuma yake ganin an kawo, ko cup baijira ba ya kafa bakin bottle ɗin yafara kwankwaɗa.*******
Tunda ta fito daga cikin gate ɗin makarantarsu take faman zuba ido taga ta inda zata hango motarsa, tasan tunda yace zaizo ya ɗauketa ba zai taɓa saɓawa ba. Da sassarfa taga yana nufo inda take hannayensa duka biyun zube a cikin aljihun wandonsa yana tafiya cikin isa da taƙama. A cikin kowane taku da yake yi sai ka rantse cewa matsalar ƙafa gareshi saboda yadda yake ɗaga su tamkar anyi masa dole. Zuciyarta ce ta shiga faman bugawa lokacin da ya iso inda take, taja numfashi tare da lumshe idanuwa ta bude su akan kyakkyawar fuskarsa. Da ka yai mata nuni da cewa su tafi, ta tsaya a gefan hagunsa. Jerawa sukayi tare ko wanensu da murmushi ɗauke a fuskarsa, suka nufi inda motarsa take a Parke. Tana shiga cikin motar ta zauna tare da ɓata rai tana cuno baki. Ya ware mata golding eye's ɗinsa, ta kwantar da kanta cikin kujerar motar tana kallonsa da kyawawan idanunta tace. "Imran yau kasha giya wallahi dan ga warinta nan ya ciki motarka, Meyasa haka ne?!" Ta faɗa cikin rawar murya da ɓacin rai ta yadda shi kansa sai da zuciyarsa ta tsaya na ɗan ƙaramin lokaci.#Asmy B Aliyu
Da
#Hajja ce 👈
[10/29, 5:11 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*