Na
*ASMY B ALIYU*
Da
*HAJJA CE 👈*PAID BOOK.... #(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta 08086207764*Katin waya na MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp.*
*Free Page 3*
Weekend ne yau kowa yana gida, Rahama bata da buri irin na tasa Imran a cikin idanunta. Duk da karanci irin na shekarunta hakan be hanata sanin cewa tayi matuƙar damuwa dashi ba. Cikin sanɗa ta leko falon ƙasa tana dubawa ko zataga Ummi da Daddy. Shiru dataji ne ya tabbatar mata da cewa basa nan, ta sauke ajiyar zuciya ta fita waje da gudu. Birema mai gadinsu ne yai saurin tare bakin ƙofar yana kallan Rahama yace. "Bazaki fita ba, saboda Hajia tace duk lokacin dana bari kikaje gidan Matawalle abakin aiki na. Ki rufa min asiri Rahama na cigaba da samarwa iyalina abinci ta wannan aikin." Shaye da toka ta kalleshi tana kallan bayanta take faɗin. "Barema kana da mata?" Ya kalleta fuska cike da mamaki yace. "Ban miki kama da mai iyali ba ne Rahama? Ina da mata harda yara huɗu." Ta juya ido ta matsa kusa dashi, da sauri Birema yaja baya yana girgiza kai yaji tace. "Ya kakeji idan kaje ka kalli matarka?" Besan lokacin da ya saki murmushi ba yana faɗin. "Ina jin daɗi Rahama, me yasa kika tambayeni?" Tayi kasa da ido
"Kabarni naje naga Imran, ina ganinsa zan dawo yanzu."
"Zakija min wallahi Rahama, dan Allah kiyi hakuri." Juyawa tayi da sauri ta koma tana jin haushin Birema. Balcony ɗin gidan ta nufa, ta janyo farar kujera daga cikin kujerun da aka ƙawata gurin dasu. Wajan katanga ta nufa ta taka kujerar, haka ta haura sai gata a bakin titi da yake titin ne ya raba tsakanin gidan Abubakar Galadanci da gidan Matawalle. Da gudu ta isa gidan tana bubugawa, maigadi ya leko. Ganin Rahama yasa shi dafe goshi ya ɗan leƙo da iyakar fuskarsa yana faɗin. "Waike dan Allah baki da kunya ne? Ba mahaifinki ya hanaki zuwa ƙofar gidan nan ba bare kice zaki shiga?" Rahama ta riƙe kugu tana kallansa da cat eye's ɗinta Tace. "Baka son naxo gidan nan ko? Toh wallahi saboda hakan zan gayawa Imran a canza mana kai dan ba zaka hana mu ganin juna ba. Yanzu zaka buɗe na shiga ciki ko sai nayi sanadin barinka gidan Matawalle?" Jikinsa ya fara rawa yasan ba ƙaramin aikin yarinyar bane ba, kuma akan abinda ta faɗa tsab Imran zai aikata dan shima akan yarinyar zai iya rufe ido ya karta maka rashin mutunci. Sai da ta shiga sannan ta kalleshi tayi masa gwalo.
Part ɗin Imran ta nufa, hannu tasa zata danna door bell sai kuma ta fasa hannu tasa ta tura ƙofar, ganin ta buɗe yasa ta shiga ciki tana dube-duben ta inda zata hangoshi. Parlorn babu kowa sai karar ac. Rahama ta nufi stairs ɗin da sassarfa, bedroom ɗinsa ta nufa tana ɗaga labule ta hangeshi kwance saman katon royal bed ɗinsa. Bacci yakeyi ya barbaje dagashi sai boxer ko vest babu a jikinsa. Kallansa ta shiga yi tana murza idanuwa ta kurawa kawantaccen gashin kirjinsa ido. Kallan bedside tayi kwalbar beer ne da glass cup ta ɗauke wacce ba'a buɗe ta shiga bathroom ɗin cikin ɗakin. Gabaki ɗaya ta juya a cikin sink ta fito tana yamutsa fuska. Imran Matawalle yai wani irin juyi wanda yasa shi kusan faɗowa daga kan gadon, Rahama tai saurin zuwa ta tare shi tana cewa. "Imran be careful please." Kamar a cikin mafarki yaji muryarta ta daki kunnansa, ya shiga buɗe idanunsa a hankali.
"Rahama.!" Ya faɗa yana kamo mata hannunta, gabaki ɗayan su suka ji wani irin shock. Imran ya lumshe ido tare da janyota ta faɗa jikinsa yasa hannu ya rungume.
Daga can ƙasan stairs sukaji Matawalle na kiran Imran, Rahama ta fizge jikinta zata fito Imran yai saurin rikota. "Karki fita wait me here." Ya miƙe ya sako jallabiya, fara kal yasa ya fito yana murza idanuwa. Sakkowa yai ƙasan yana saka hannu ɗaya cikin aljihun rigar yace. "Daddy. Matawalle ya kalleshi cike da kulawa yana faɗin. "Kasan 2:30pm jirgin mu zai tashi ko? Ya kamata ka shirya komai kafin lokacin ya yi." Imran Matawalle ya langaɓe kai. "Daddy please asa wani ya karbo min, bana san barin Kano Daddy." Matawalle ya kamo hannunsa ya jashi jikinsa tare da faɗin. "Ina so duk wani abu da zai xama na ci gaban rayuwarka ne ka dinga yi da kanka, Imran bana san ka zama lusarin namiji. I know da mahaifiyarka na raye itace zata dinga ƙarfafa maka guiwa, but ka godewa Allah ina raye gashi ina doraka akan hanyar da ko Aisha na raye abinda zata yi maka kenan." Rahama ce ta fito da wani irin kallo Matawalle ya bita sai rabe-rabe take.