ASMY B ALIYU
Da
*HAJJA CE*PAID BOOK...#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764*Katin waya ta MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp.*
*Free page 4*
Hawaye kawai ke rolling akan face ɗinta, ta kasa baiwa Ummi amsar da take buƙata, maganar auren da Abbanta ya faɗa zai yi mata yafi komai tsaya mata a rai. Tabbas bata shirya yin aure yanzu ba, tana son tayi karatu mai zurfi da shine babban mafarkinta a duniya ta ganta a cikin jami'ar Ado Bayero. Da ace da Imran zai haɗa auren da sauƙi. Ƙara rushewa tayi da wani irin kuka mai cin rai da sauri ta rarrafa gaban Ummi ta rike hannunta still hawaye na zubar mata take faɗin. "Ummi kina jin aure Abba zaiyi min? Aure fa Ummi ni ina na isa aure Ummi? Da kananun shekaru irin nawa. Wallahi Ummi ina son na zama likita tamkar keda Imran. Karatun likitanci fa yayi shima Ummi, ki taimakeni Ummi wallahi ban isa aure ba, kuma kin san Abba zai iya Ummi." Rahama ta faɗa a haukace.
Da sauri Ummi ta fisge kanta daga riƙon da Rahama tayi mata tana yi mata wani irin kallo take faɗin. "Bakison aure Rahama meya kaiki gidan su har cikin ɗakin barcinsa? shin bakiji yarda mutanen unguwar nan ke tsinewa hallayar Imran matawalle ba.? Ai wallahi da kije ki kwaso mana abun kunya ƙara ayi maki auren kowa ya huta, tunda ke magana ɗaya bata shiga kunnen ki. Nayi faɗa, nayi nasihar, nayi addu'ar amman duk a banza. Wallahi Rahama kafiyarki tayi yawa akan wannan tsinannen yaron, ko mahaifinki ya yarda da auren Imran Matawalle, ni bazan yarda ba wallahi koda bayan numfashina ban yarje maki auren wannan tsinannen ba." A fusace Ummi ta nufi stairs ba takarabi takan Rahama ba, wacce tsabar shock zama tayi akan marbles tana jin zuciyarta tamkar zata fito saboda tashin hankali. Duk yarda taso ta farantawa iyayenta akan dena zuwa wajen Imran kasawa takeyi, zuciyarta ta hanata hutawa daga bugawa duk akan ƙaunar da take yi wa Imran Matawalle. Tana ƙaunar Imran Matawalle tun kafin ta ma san meye so, ko yanzu bawai tana banbance soyayyarsa bane acikin zuciyarta, tasan dai kawai ganin Imran Matawalle a idanunta yana sakata wani irin farin ciki. Murmushinsa a gareta, tafiyar sa , komai dai na Imran Matawalle tana sonsa tana kuma girmamasa. Komai zai faru bazata yarda da wannan auren da Abbanta ke son yayi mata ba. Bazata karɓesa ba ko hakan zaisa iyayenta su juya mata baya, dan indai akan Imran Matawalle ne kowa zai ɓata da ita. Ta share hawayen idonta ta nufi stairs tana jin wani ciwon kai na damunta ga tafiar da taji Matawalle na faɗar zasuyi da Imran a yau, wanda Imran ɗin bai sanar da ita hakan ba. Ra'is na kallanta har ta haye, ya girgiza kai, ita dai Yaya Rahama kullum sai taja an doketa akan wancen guy ɗin. Ya juya shima ya nufi wajan tv.*****
Ya daɗe cikin bad mood saboda rashin shan beer, ya rarrafa da kyar ya janyo wayarsa. Al-Amin ya shiga kira ana ce masa wayar a kashe take. A ranar jirginsu Imran ya ɗaga zuwa ƙasar Russia. Matawalle yana kula da yanayin sa, sai dai ya sharesa ko acikin jirgin ana bada abinci amman Imran babu abunda yaci. Gaba ɗaya hankalinsa yana kan Rahama dan ya san yanzu tana can mahaifinta ya mata duka duk sabida kulawarta a garesa, dan yanaji a jikinsa duk inda take a halin yanzu bata cikin yanayi mai daɗi, kuma duk ta sanadiyarsa. Tabbas da zai iya durkusawa Abubakar Galadanci, da yaje ya duƙa yace ya basa auren Rahama. Amman bazai iya wannan kasadar ba, dan yasan ko ya durkusa masa akin banza ne, yarda yake da zuciyar arnaye. Kwana biyu da tafiyar Imran bai samu ya kira Rahama a waya ba, dan dama landline ce suke yi a ciki. Basu san duk yarda za'a haɗu Rahama da Imran ta kowace ƙofa Abubakar Galadanci ya toshe ta, kuma shi da kansa yake kai Rahama makaranta, haka zalika shi yake zuwa ɗaukar ta.
Kamar kullum dawowar su kenan daga makaranta a bakin gate mahaifinsu ya aje su sai da ya tabbatar da shigar su ya juya motarsa zuwa office. Haka su Rahama suka shigo parlorn fuskarta tamkar hadari sai dai ganin Hajja zaune a parlorn yasa ta wani ruga da gudu gameda buɗe hannayenta duka biyu tana jin hawaye na cika idonta lokaci ɗaya ta fashe da kuka tana ƙanƙame Hajja.