Albi (my Heart)

20 0 0
                                    

   Na
*ASMY B ALIYU*
   Da
*HAJJA CE 👈*

PAID BOOK.... #(500)

*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta 08086207764

*Katin waya na MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp.*

*Free Page 2*

"Kayi shiru saboda kasan banyi karya ba ko?" Imran ya kunna motar yana faɗin. "Zan dena soon kiyi min addu'a." Rahama tai saurin dagowa ta zuba masa beauty eye's ɗinta masu kama da na mage tana faɗin. "When Imran? Ina so naga ka dena please." Yasa hannu tare da kamo nata yana matsawa wanda yake so softly. "When we got married Rahama, Insha Allahu nima wani time ɗin bana san shan beer, wani lokacin kuma ina jin idan ban sha ba zan iya losing hankalina, but I'm Imran Matawalle zan dena shan beer." Bayan hannunta ya sumbata sannan ta maida kanta bayan kujera, lumshe ido tayi cikin zuciyarta tana cewa. "I love you so much Imran." Ya tada motar suka bar wajan. Imran yana mamakin yadda yarinyar takesan shi, gashi dai yarinya ce so younger than him, but yadda take bashi kulawa abin yana bashi mamaki sosai. Yai perking wajan wani mall, Rahama cikin farin ciki ta kalleshi tana murna tace. "Really Imran? Me zamuyi a ciki?" Ya shafa sumarsa da har lokacin bata dena walwaliba yace. "Muje ki dauki abinda kike so, just for you Rahama." Tsalle tayi ta faɗa jikinsa hakan yasa Imran jin wani irin feeling, ya rintsa ido yana janyeta daga jikinsa saboda wani bugu da zuciyarsa keyi. Suka fito a tare suka shiga kai kace brother and sister ne saboda yadda suke ɗan wani fisgazar kama da juna. Uban siyayya Imran Matawalle ya mata, suka sa a mota ya  wuce dasu yawo kafin su nufi gida. Ummi tuni ranta ya gama baci rashin dawowar Rahama dan tuni Ra'is ya daɗe da dawowa gida, Adamu driver ya dawo dashi wai sun duba ko'ina basu gantaba a school ɗin. Da gudu ta shiga tana murna, Ra'is dake zaune yana lunch ya cije baki cikin ɗaga murya yake kiran. "Ummi ga Rahama ta dawo." Ummi ta fito shaye da toka ta kalli inda Rahma take, kayan hannunta ta kalla tare da faɗin. "Daga gidan ubanwa kike Rahama? Wannan kayan waye ya bakisu?" Rahama ta shiga ja da baya "Imran ne ya siya min." Cikin sauri Ummi ta kifa mata wani gigitaccen mari, tasa ƙafa ta harba mata, rai a mugun bace tace. "Yaushe ne zaki dena bin wannan ɗan iskan yaron? Har me Imran Matawalle kedashi da zai ruɗeki Rahama? Sokike yaje ya lalata manake ya cuce mu, tunda ba tarbiya yake da ita ba?" Ummi ta ɗauke leda bag's ɗin dake gaban Rahama tayi wurgi da ita, kayan ciki duk suka tarwatse. Kuka ta shiga yi cikin tashin hankali itama take faɗin. "Ummi kidena zagin Imran, Imran yana da kirki, yana kulawa dani shine mafa yaje ya ɗakkoni a makaranta." A haukace Ummi tayi kanta. "Zakiyi min shiru kosai na fasaki a gurin nan, dan ubanki duk kulawar da zai baki ya kai namu me? Who is he? Nace waye shi banda banza mashayi?" Kalaman Ummi sun sake sosawa Rahma rai, ta tashi da gudu tayi stairs tana ihu kamar wacce ake yankawa. Wannan dalilin yasa ko parlorn ƙasa Rahama bata fito ba, komai ta haƙura dashi dan makaranta ma hanata zuwa Ummi tayi saboda karma ta sake shiga harkar yaron.
After three day's.

******
Cikin sassarfa take sakkowa daga saman benan wanda yasha ash ɗin tiles mai zane-zane yana ta faman sheƙi, tana yi tana riƙe karfen jiki har ta ƙarasa sakkowa, kai tsaye kuma ta nufi ƙofar da zata bar cikin katafaren falon gidan. Kiran sunanta da akayi ne yasa ta saurin tsayawa cak tana rintsa ido saboda tsaida ita da aka yi. A shagwaɓe ta juya tana turo baki fuska cike da taɓara tana kallansa yace mata.
"Come here Rahama." Ta ƙarasa wajan nashi tana bubbuga kafafuwa.
"Abba please kabarni naje na dawo." Alhaji Abubakar Galadanci yasa hannunsa tare da janyota ta ya xaunar daita gefensa .
"Ina zakije haka kike sauri?"
"Waje zani yanzun nan zan dawo Abba." Ya kalli kanta da babu hula sai yara-yaran kalbar da akai mata yace.
"Ina ɗankwalinki?" Tayi saurin shafa kanta taji ashe hular bata kanta, gabaki ɗaya ta ruɗe ne so take kawai ta ganta a wajan motarshi da ta hango zai bar cikin gidansu.
"Gatacan a bedroom ɗina bari naje na ɗakko." Tana gama faɗa ta zare hannunta daga nashi ta koma sama da gudu, bata jima ba ta sake dawowa ta fice dan karma Abba  ya sake kiranta.
Wata rantsatsiyar mota kirar marsandi fara sol ta fito daga cikin wani arnan gida wanda yake facing gidan su Rahama, sauran kaɗan motar ta doketa sakamakon gudun da takeyi dan ta isa wajan. Imran Matawalle ya kama birki da sauri ya take motar ta tsaya. Wajan glass ta ƙarasa tare da bubbuga masa, ya kalli inda take tsaye yana sake kare mata kallo ba tare da ya zuge glass ɗin ba. Duk a tunaninsa yau bazai hadu da itaba ashe tana nan shi take jira kamar koda yaushe. Yasa hannusa a hankali ya zuge glass ɗin tare da zuba mata touching sexy eyes ɗinsa dasu suke sake jefata cikin mugun kaunarsa.
"Ya aka yi ne R A Galadanci? Anything from me?" Ya faɗa kasancewar haka yake kiranta dashi kullum.
"Yauma tafiya zakai bazaka tafi dani ba ko?" I Matawalle ya kalleta da sexy idanunsa masu kama dana mage yace.
"Yeap ba yau ba, kuma ba gobe ba kisan dai matsalar dake tsakanin mu." Riko masa hannu tayi taji wani irin shock ajikinta, da sauri kuma ta sakar masa saboda gudun fadawa wani abun tace.
"Take me where you want to go Imran, Idan har kabar gurin nan babu ni zuciyata bazata zauna cikin nutsuwa ba. Muje zan rakaka duk inda zakaje." Ta nufi ɗaya ɓarin tana shirin shiga taji an mata wani irin kira daga cikin gidansu. Gabanta ya bada wani irin bugu, cikin fushi da bacin rai Honorable Abubakar Galadanci yace.
"Idan kika sake taɓa motar nan sai na kakkaryaki, kishigo gida kafin nasa a ɗakko minke."
Magana yake tun daga can saman stairs ɗin gidan nashi fuskarsa cike da bacin rai. Imran Matawalle ya kalli inda Rahama take wacce harta fara kuka, sam batasan wannan bala'i da masifar da iyayansu keyi, ita bataga dalilin da zai sa gabar dake tsakanin Abbanta dana Imran ya shafi alaƙarsu ba, sai dai yanzu ba yadda zatai ta juya xuwa  gida tana fashewa da kuka. Shima Imran jan motarsa yayi a fusace har yana sata yin hayaƙi dan Alhaji Abubakar Galadanci yagani. Tun a parlor Rahama ta saki wani irin ihu tana faɗawa mahaifinta yayi hakuri ya yafe mata. Wayar wuta ya ɗauko ya shiga binta da ita yana duka. Kamar zata shiɗe ta riƙesa sosai tana sake fashe masa da kuka mai cin rai take faɗin. "Kayi hakuri Abba wallahi bazan ƙara ba." Ta faɗa hawaye na rolling down akan tattausan cheeks dinta. A fusace Abubakar galadanci yayi jifa da wayar yana haki da mugun tsawa yake fadin. "Tashi daga nan nabar ganinki a gabana kona karya ki." Da rarrafe Rahama ta miƙe ta nufi ɗakin barcinta. Kallon jikinta ta shiga yi yadda Abbanta ya fasa mata fata, jikinta yayi wani burɗin-burɗin abuka ga farar fata, bulalar ta fito sosai a jikinta. Yinin ranar a ɗaki ta yi shi, ƴar aiki har abinci ta kawo mata ɗaki amma ko kallon abincin batayi ba. Sosai take missing Hajja kakarta wacce ke zaune garin Abuja wajan yayan mahaifina. Da dadaddare Ra'is ya shiga ɗakin nata ɗauke da plate ɗin abinci yaja center table dake tsakiyyar room ɗin ya ɗora, ya zauna cikin soofa yana kallon sister ɗinsa da fuskar damuwa yake fadin. "Ki sauko kici abinci dan Allah Yaya Rahama." Ta harɗe hannunta a kirji tana fadin. "Zakayi min wani alfarma Ra'is? idan kayi min zanci." Da sauri Ra'is yace "Zanyi miki Yaya tell me mekike so?" Rahma tayi saurin cewa "Wayar Ummi nake so ka ɗauko min." Ra'is ya zaro ido yana fadin. "Kinsan fa Ummi bata barin a ɗaukar mata waya, musamman make da kike kiran Imran." Rahma da sauri tace. "Kai ni ba Imran zan kira ba, Hajja zan kira tazo muna hutu nan gidan." Murna ya shiga yi yana cewa. "Owk zan gwada, idan kuma Ummi ta kamani me zan faɗa mata Yaya Rahama?" Yayi maganar sounding so childish. Ta buɗe masa hannu tana faɗin. "Bazama ta kama kaba, yaro minti nawa ma ya isa mu mayar mata ka tsaya surutu. Nasan yanzu tana part ɗin Abba." Ra'is ya girgiza kai kawai ya nufi kofa. Bai jima ba ya dawo da waya a hannunsa ya kalli plate ɗin abincin hannun Rahama har taci fiye da rabin abincin. Da sauri ta ɗauke plate ɗin, jikinta na rawa ta mika hannu zata karɓi wayar Ra'is da sauri ya maidata ita baya, shaye da toka yake faɗin. "Promise me Yaya Rahama Hajja zaki kira ba Yaya Imran ba, karki jamin a wurin Ummi?" Ya faɗa yana kallonta, ta juya ido tana faɗin. "Ka taɓa ji nayi maka karya ne Ra'is?" Ta faɗa tana tsaresa da ido. Miƙa mata wayar yayi ta nemo sunan Hajja ta danna mata kira, ba'a ɗaga ba still ta ƙara ƙira nan ma dai shiru. Haushi ya kama Rahama ta kalli Ra'is tana faɗin. "Wayyo Allah bata ɗaga ba." Ra'is zai yi magana wayar ta fara ringing, Rahma ta ware ido ganin sunan Hajja ce mai kiran. Cike da farin ciki ta ɗaga da wani irin murna. Daga can ɓangaren Hajjah tace. "Yau kin tuna dani? dazun nan muka gama maganarki da Maminku ta nan." Rahama ta taɓe baki kamar tana kallanta, da sauri tace. "Dama Hajja tambayarki zanyi yaushe zaki zo Kano? Ni wallahi inata kewarki." Ta faɗa cikin kwantar da murya. "Ahh ni! Sai dai idan kun samu hutu sai kizo nan, ke matsalarki bakya son ɗagawa ko'ina kullum kina manne da iyayenki, idan kukai hutu kiyitahowarki nan. Dama kinga jibi ɗan gidanki zai dawo daga can ƙasar da ya tafi karatu, wai ya kammala gaba ɗaya, kinga sai maganar Auren ku kawai."
Wani irin dummn Rahama taji, lallai kam ita wallahi dariya ma Hajja ke bata idan tana maganar Aurenta da Farook Galadanci, wani irin mutum ne shi mai girman kai wanda yake yiwa mutane kallon wulakanci da kaskanci, yana ɗaukar kansa a wata tsiya, gashi mugu ne na bugawa a jarida. Saurin rufe idonta tayi dan ta tsani koda tuna fuskarsa n. Rahama ta haɗe rai tana faɗin. "Ni dai kizo nan dan Allah, nayi kewarki wallahi Hajja." Hajja tayi murmushi tana faɗin. "Shikenan zamu zo tare da Farook idan ya dawo." Rahama tace, "Zuwa yaushe kenan?" A hasale Hajja tace. "Ke kin fiye jaraba wani lokacin wallahi, duk randa Allah yayi." A fusace Rahama ta katse kiran tare da goge kiran Hajjan dan kar Ummi ta gane, ta mikawa Ra'is wayar ranta duk babu daɗi.

Washegari batayi gigin zuwa ganin Imran kamar yadda ta saba ba, saboda Abba ne zai kaisu makaranta anyiwa Adamu rasuwa ya tafi garin su. Akan idonta suka wuce ƙofar gidansu Imran tana ta kallan gidan kamar ta shiga, bugun zuciyarta taji yana fita da sauri da sauri ta rintsa idanuwanta. Har Abba ya saukesu a school babu wata walwala a fuskar Rahma.
Yau kam koda suka tashi Ummi ce taje  ɗaukar su, Rahama na hangota tayi saurin  haɗe rai, duk a tunaninta ta ɗauka Ummi na asibiti sai yamma zata dawo. Kasancewar Ummi likitan yara ce a asibitin malam Aminu Kano dake cikin Kano. Ra'is ne ya fara gaida Ummin nasu ya buɗe back seat ya shiga ya zauna. Rahama ta buɗe gaban motar ta xauna sabida al'adar sune in har Ummi xata jasu a mota toh Rahama ce a gaba. Idan kuma Abba ne ko Adamu toh Ra'is ne zai xauna a gaban motar. Baki Ummi ta buɗe tana kallon Rahama ganin yadda take wani cin magani. Ta kalli Ra'is tana faɗin. "Ita kuma wannan ita dawaye?" Ra'is ya ɗaga kafaɗa yana faɗin shima bai sani ba tun safe haka mood ɗin ta yake. Jin yadda ake tambayar meke damuna yasa ta buɗe baki tace. "Ummi ina yini?" Ko kallonta Ummi batayi ba tayiwa motar ta key suka bar wurin. Ra'is ne yace da Ummi taje dashi shop zai duba wani text book. Har suka isa gida Rahama bata magana. itama kuma Ummi shareta tayi ta cigaba da hirarta da Rais...

****
Matawalle place..

Baki sake Mommy ke kallonsa cikin wani irin bakin ciki take faɗin. "Yanzu ma tafiyar da zaka yi sai ka saka Imran a gaba tamkar wanda ake bawa nono? toh wai shin wazai riƙa kula da hidimar gidan?." Wani banzan kallo Matawalle ya shiga yiwa Mommy cike da gajiya da halinta yake faɗin. "Haka kawai zan kama hanya naje karbo takardun Imran na makaranta shi meye amfaninsa? wasu abubuwan dole shi da kansa zaiyi su fa. Wai ke me yasa kin fiye son kanki da yawa ne? meyasa bakin ciki ya cika zuciyarki musamman akan duk wani sha'anin ɗana gudan jini na Imran Matawalle? Toh bari kiji, ko kiso ko kirki so Imran shine zai maye gurbina wata rana. Haka kuma shi zai kula da kannensa wanda kika haifa, ki kama mutuncin ki tun wuri, dan akan Imran zan iya ɓatawa da kowa wallahi, dan shine sanyi idaniyata..."
Matawalle yayi maganar so pissed up. Wani turirin bakin ciki ya cika zuciyar Mummy ganin yadda Matawalle ke zuba mata bakaken maganganu duk akan soyayyar da yake yiwa Imran. Ai kuwa kota tsiya kota bala'i sai ta saka wannan soyayyar sun zama makiyan juna. Yanzu kam suje a karbo kwalin Imran na digirinsa na biyu a ƙasar Russia wanda tasan medicine ya karanta, haka kuma matawalle yana da burin ya buɗewa Imran babban asibiti da sunan sa. Tayi murmushi tana kallon Matawalle, Imran ya kalleta sama da ƙasa ya watsar, daga karshe ma ya mike tsaye ya nufi ƙofa dan shi ko kaɗan baya son wannan tafiyar zuwa Russian kuma wai shi da Daddy zasu.
Shi kam ya zaiyi da wannan uwar rigimar tashi  Rahama idan taji? Tabbas yasan idan yace mata zai yi tafiya fushi zatayi ko ta buɗe baki ta yi masa kuka. kuma sanadin damuwa ta kwanta ciwo mai tsanani. ...

#Asmy b Aliyu
#Hajja ce

ALBI(MY HEART)Where stories live. Discover now