SALMAN MALEEK!

44 8 0
                                    

SALMAN MALEEK!
Na shiga ban ɗauka ba...

            Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya
(Matarso)

GODIYA
Dukkan yabo da godiya, su tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin sa su tabbata a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (SAW).

SADAUKARWA
Wannan labarin sukutum ɗin shi, sadaukarwa ne ga ƙawata, wato masoyita (dear) Ummi Sunisi, ki yi yadda kike so da shi, I really love u, Allah ya bar ƙauna.

Shafi na ɗaya 01

بسم الله الرحمن الرحيم

"Jameel, ni fa zan faɗi gaskiya, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, game da abin da muka aikata, ina mai tabbatar maka alhakin shi bazai taɓa barin mu ba, gwara tun wuri mu faɗi gaskiya, kamar yadda wancen barristern  ya yi mana alƙawari cewa, in har muka faɗi gaskiya za ayi mana sassauci".

"Ka ji irin shirmen ko, ai ban taɓa sanin daƙiƙi bane kai ba, sai yau, mu faɗi gaskiya! ashe kai jaki ne, kanka ba ya ja, to bari kaji, duk wani waye-waye ƙarya yake, so suke su mana in giza mai kantu, kana faɗar gaskiya zaka rufta, in zaka iya bakinka ka iya, ka gane ai, ka daina banzan tunani." ya ƙare maganar yana bugun kafaɗar shi, kamin yabar gurin.

"ƙwal uba kaga wani kamar biri."
A cewar Habu da sarkin gida ya turo shi yaga wa'inda sukai saura basu je wurin karɓar abinci ba.

"Kai tunanin me kake yi haka ka zabga uban ta gumi? Ko babarka ce ta mutu?."
Ya yi maganar irin ta yaran nan gagararru.

Ɗago da kanshi ya yi ya sauke su akan shi.

Cikin maganar sa ta y'an shaye-shaye ya ce "Kai kamar ma kuka kake yi, naga hawaye kwance a Kuncinka, to kasan ba zaka iya ba, uban wa ya aike ka kayi laifin da aka kawo ka, kai dallah malam ware, in zaka ware ka saki jikinka ka ware, uban wa ma kake wa kuka anan." yasa ƙafa ya share shi ƙasa, kana yabi takan ƙafafun ya wuce.

Cike da dana sani ya tashi, ya karkaɗe jikinsa, gami da ɗaukar robarsa, ya nufi gurin karɓar abinci.

Tafe yake yana zuƙar sugari, yana fitar da hayaƙi ta hanci ta baki, ji yayi an ce "kai zo ka bani sigarin nan."

Oga Tajo da ya ji maganar, amma bai ga kowa ba, har zai wuce, sai kuma ya hange shi zaune bisa siminti, ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Bayan ya matso kusa da shi, ya gama ƙare mishi kallo ya ce
"kai ba ayi mana hauka anan, nan gidan ɗan kande ne, ba gidan ku ba."

"I na san da haka, zaka bani ko sai dai ƙarfina ya bani?."
Ya faɗa yana mishi kallon gargaɗi.

"Bazan baka ba, na ce bazan bada ba, kaga yaro, kai har ni zaka yiwa barazana, ni zaka nunawa zafin kai, wa'inda suka fi ka ma naji dasu a gidan nan, ballantana..."

Bai iya ƙarasa maganar ba, ta maƙale, a sakamon hannun sa daya kama ya banƙare shi baya.

Ƙara oga Tajo ya saki, tare da magiya, akan bai san abin haka yake ba, don Allah ya yi haƙuri ya ƙyale shi, in dai sigari ce ya ɗauka duka ma, tsabar azaba, har da sakin fitsari ba tare da ya sani ba.

Shiko Salman dariyar mugunta yake saki, yana nishaɗantuwa da ihun da Tajo ke yi.

"Kai! kai!."
Wani gandiroba daya hango abin da ke faruwa ya tawo, ko da yazo dukan shi ya fara da kulkin da ke hannunsa, amma ko gezau be yi ba, sai da ya tabbatar da kafaɗun shi sun yi ƙara, kana ya sake shi, gami da zura hannu a aljihun shi, ya cire sigarin da letar, ya kunna bayan ya zuƙa, ya hura musu hayaƙin a fuska, sannan ya bar wurin.

"Ogo Nura, don Allah duban ka gani, ya tsinke min kafaɗu?."

"kafaɗunka suna nan Tajo." Oga Nura ya bashi amsa.

SALMAN MALEEK! Where stories live. Discover now