SALMAN MALEEK!
Na shiga ban ɗauka ba...Na
Siddiqahtulkhaireey yahya
(Matarso)بسم الله الرحمن الرحيم
Shafi na biyu 02
Tashi Ummey ma tayi tabi bayanta.
"To tsaka uwar munafukai, kin tashi zungwi-zungwi, woto zaki bi ta ki ƙara kitsa mata yanda zata zageni ko, kana dai gani Maleek, a gaban ka matarka da y'arka suka ci zarafi na."
kawai sai ta fashe da kuka tana "ba komai rayuwa ce, idan ka gaji da ni ne sai ka gaya mini nabar maka gidanka.""A haba Ammy, wane mutum in ji mutuwa, ai mutawa ce kawai zata raba mu, in sha Allah". Ya faɗa yana tashi daga kan dinning table ɗin, ya nufi gurin wanke hannu, dake wajen dinning ɗin, yana gamawa ya haura sama.
A kwance ya samu Samaheer a kan cinyar Ummey tana shafa kanta tana bata haƙuri.
Bayan ya shiga ya zauna wajen ƙafafun Samaheer yana ja mata yatsun ƙafa.
"Ummu Salman, Allah ya miki Albarka ke da yaran ki, kin gama mini komai a rayuwata, nagode ina godiya, wallahi ban san da me zan saka miki ba, nasan kina haƙuri zama da Ammy a cikin gidan nan, duk da baki taɓa kawo min kushe, ko ki nuna gazawa ba, amma dai bazan gaji da baki haƙuri ba, ki ƙara haƙuri, kin san iyaye idan suka fara girma, sai ana kai zuciya nesa ".
Hannun shi ta kama ta riƙe, ya kalleta suka haɗa ido, cikin juriya da dakiyar zuciya ta ce "Abu Salman, wai sau nawa zan ce ka daina mini godiya, ko ban haƙuri akan lamarin gidan nan? Nima fa Ammy uwata ce, kuma watarana sai labari, zan cigaba da taya ka mata biyayya a samu a rabu lafiya, in sha Allah." tashi ya yi, ya sumbaci goshin ta, kana ya dawo ya sumbaci ƙafafun Samaheer da take kwance kan cinyar Ummey ta kifa kanta, tana jin duk abin da suke cewa amma bata ɗago ba.
Hawayen da take maƙalewa ya surnano, da sauri yasa hannu ya share, ya ce "nasan jarumar matata ba ƙaramin abu ke sata kuka ba, saboda dakiyar zuciyar ta, ba don kar Muneera ta ce Maleek ya fiye azarɓaɓi ba, da sai in ce akan jarumi kuma sadaukin ɗanta take yi."
Bata san sanda murmushi ya ƙwace mata ba, har sai da kumatunta ya lotsa, ita kanta Samaheer da take kwance murmushin take yi, salon soyayyar Ummey da Abbey abar kwatance ce, ba ƙaramar burgeta suke ba, soyayya ce tsantsa ta tsakani da Allah, saboda soyayyar su suke ci kamar basu manyanta ba, addu'ar ta kenan, a kullum ba dare ba rana, Allah ya bata miji na gari irin Abbey ɗin su.
"Na daɗe da sanin jarumin mijina ya gama fahimtar wa ce Muneera, da na yi motsi kan nayi magana, zaka ce abu kaza ne, a yanzun ma ba kai kuskuren fahimta ba, ya kai jarumi uban sadaukin ɗa na, ya ya ake ciki akan batun sa?."
Murmishi yayi wanda ya ƙara fito da tsantsa gwaron kyan shi, duk da girman da ya ɗan yi, amma kallo ɗaya zaka yi mishi ka hangi tsantsar kyawun hallitar da Allah yayi mishi.
"Ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah, a wannan zaman za a samu mafita, saboda na tabbatar Nawal da Kareem suna kan yin bakin ƙoƙarin su, in sha Allah, Allah zai basu sa'a, a zama na biyun nan, wanda daga shi ne za'a yanke musu hukunci, sai dai idan bai mana ba mu ɗaukaka ƙara."
Cikin gamsuwa ta jinjina kai, ta kuma ɗora da cewa.
"Shi ne shima da uban taurin kai, ya ƙi ya buɗe baki yayi bayanin abin da ya faru, amma wallahi ina da yakinin ɗa na ba ɓarawo bane.""Nima nasan ban haifi ɓarawo ba, kawai sharri suke masa, amma in sha Allah zai koma musu." a cewar Abbey da ya fiddo waya daga aljihu, domin ganin wanda ke neman shi.
Haka sukai ta tattaunawa kan lamarin, ba tare da Samaheer ta ce ƙala ba, saboda ita bata daga cikin mutanen nan masu magana, miskila ce ta bugawa a jarida.
YOU ARE READING
SALMAN MALEEK!
RomanceSalman maleek! Sabon salon wani labari ne, wanda zay matukar kayatar da mai karatu, labarin wani mashahurin mawaƙi ne mai ban al'ajabi, ha'inci, sadaukarwa, makircin dangin uba, zagon kasa, uwa uba akwai zazzafar soyayya mai ratsa zuciya, wacce take...