KALUBALENAH
5
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.ORCHID HIGH SCHOOL.
Tsaye 15 years old deenah take a bakin gate ɗin tamfatsetsen gate din makarantar kirjinta na dukan uku uku tana tunanin yarda zata shiga cikin makarantar tayi mu'amala da ahalin cikinta,
Tuna kalaman zainaba tayi inda take ce mata "deenah babu talaka sai wanda ya mayar da kansa talaka a zuciya ,kidaina sawa kanki cewa ke talaka ce ,sannan ki cire tsoro a ranki na wannan makaranta da kika samu ,
Dama ɗaya ce wadda idan ta wuce ki to da wuya ki sake samun irinta dan haka ki saki jikinki kiyi amfani da wannan damar taki,ki kuma saka aranki karatu ne ya kaiki wannan makarantar kuma Allah ne ya kaiki sannan yin Allah bana mutum ba ,dan haka tunda ya kaiki wannan makarantar yana da manufa ,
Kiji ki ƙi ji ki gani ki ƙi gani,
Babu ruwanki da takalar faɗa kiyi kokari ki zauna da kowa lapia sai kiga kinci ribar rayuwa.Gyara beret ɗin kanta tayi cikin ƙwarewa dan tunda ta fara mafarkin makarantar ta ke kokarin taga ta kware wajen koyan abubuwa da dama,
Necktie ɗinta ta kara gyarawa zama sosai ,
Tayi tuck in na long sleeve white ɗin dake jikinta cikin dark and light brown skirt ɗin da ya wuce gwiwa da kadan wanda da kyar maminta ta lamunce mata tasaka ,shima dan tasaka dogun skin tight mai safa ne baki,
Sai armless brown top wadda take mahadin uniform ɗin,
tayi kyau sosai a cikin sabon uniform ɗin da makarantar ta bata,
Jakarta ta gefe da baƙin takalmin da mama kaltu ta siyo mata a gwanjo ta kuma kalla tana jin baya ita kuma bazata bari wani ya faɗan mata otherwise ba.
Kai tsaye ta nufi wawakeken gate ɗin shiga makarantar da yake a wawake kamar yarda taga sauran daliban nayi,
Bata kuma nutsewa cikin kallo ba sai da ta ganta cikin yalwataccen harabar makarantar da dalibai ke kaikawo nazuwa ajujuwansu,takawa ta cigaba da yi dan nemo nata ajin wanda yake ss1A,
Bayan ta gama zageye kasa bataga ajin bane ta nufi matattakalar benen da zata sada ka da ajujuwan dake first floor,
Othman Deenah Ali,
Juyawa tayi jin an ambaci sunanta nervously ,
Wata kyakyawar malamace wadda kallo daya zaka mata kasan yar gayu ce gata very young ,
Kada kai deenah tayi tace "yes"
Follow me shine abunda malamar tafaɗa ta fara tafiya ,
Babu musu Deenah tabi bayanta da ɗari ɗari,
Wani office suka shiga bayan ta aika tace a kira mata class rep na ss1A,
Tsaye deenah tayi a gaban matar da ta zauna a mazauninta,
Cire glasses ɗin dake fuskar ta tayi tace"
You're welcome to orchid high deenah,and I hope you will abide by the rules ,
I am miss suraj Aafiyya ,ss1A class master ,
No fighting,no bullying ,cult,exam malpractice etc,
Girl you'll have to shun all the bad things because if you are caught in any of sort act, then its a total withdraw,
And If you have any problem in the school I believe you know the door to my office ,
Once again you're welcome to orchid high.Tsaf deenah ta fahimci abunda matar ke faɗi dan ihsan kanwar binyamin tana mata lesson na English duba da sabon da sukayi wanda ihsan ɗince ta fara janta a jiki dan duk da girmewa deenah da tayi tana jin santa a ranta ,
nacine da deenah sosai dan haka cikin lokuta da basu da yawa ta kile a yaren,
Sannan ihsan kan bata wayanta tayi research na vocabularies sannan ta yarda da bibiyar dictionary ɗinta,"Thank you aunty and i promise to abide by the school rules .
Miss suraj ,malamar ta faɗa cikin sigar gyara na aunty ɗin da deenah ta faɗa mata .
Murmushi deenah tayi cikin nauyi tace I am sorry ,"miss suraj .
Dan ita ta saba a bokon su ko wacce malama mace aunty ce.Knocking Kofar akayi,izini miss suraj ta bawa mai knocking din da ya shigo,
Wani yaro ne ya shigo jikinsa sanye da uniform ,
Kallansa deenah tayi aranta tana mai furta "gaskiya yayan masu kudi daban suke,fatarsu kawai abun kalla ce ,
Gaida malamar yayi cikin halshen turanci kafun ta amsa ta masa izini da ya zaga da deenah makarantan sannan ta mika mata key din locker ɗinta wanda yake dauke da number 59 tace ya rakata,
Babu musu deenah tabi bayan kyakyawan yaran da fuskarsa babu yabo babu fallasa,
Lockernta ya fara rakata ya nuna mata kafun suka fita dan yayi mata tour na guraren da ya kamata ta sani a cikin makarantar,
Shiru suke zagaye filin sport ɗin dake makarantar kafun ya katse shirun ta hanyar kallan tag ɗinta yace ,
Othman Deenah Ali.
Sunanki mai dadi,
Kallan tag ɗin nata da ta fahimci daga nan ya ga sunanta tayi tace nagode,
Sake sakin fuskarsa yayi fiye da da yace sunana umar izziddeen saraki"
But you can call me DEEN
And nini class rep na ss1A ,
Hannunsa ya mika mata for a handshake taki karba,
Sosa sumansa yayi yace ooopz you don't shake,?I'm sorry" ta furta"
No its okay yafada yana mai cewa nan cheerteam ke zama,i will introduce you to the leader Idan kinasan joining,
cikin sauri tace"no nagode".
Murmushi yayi yace "as you wish,
And now the last place is the cafeteria,then sai muje aji kiga class mates ɗinki saboda we will be having class by nine"
Ba musu ta bisa tana mai yaba kirkinsa .
Babu kowa a cafeteria ɗin haka suka gama tour ɗinsu suka nufi class ,
Tana lura da yarda mutane ke nuna ta musamman yan matan amma ta zabi da ta toshe kunnuwanta ta rufe idanunta tunda dama tasan ai ita ba tsarar su bace.
Glass door din ajin deen ya tura ,kowanne dalibi acikin ajin saida ya juyo dan an riga an kawo musu tsurkun scholarship student tazo tana tareda class rep ,
Tana shiga gabanta ya cigaba da duka ganin classy yaran dake cikin ajin wanda gasu dai cikin school uniforms suke amma a jikinsu sai kaga fancy abu kar ma ace matan ,
Kamar ance ta ɗaga idanunta ta sauke su kan azad,
Duk da basu ga miciji amma at least taga wanda ta sani and tasan bazai mata wulakanci ba cikin makarantar kilan ma wannan ya zama silar shakuwarsu tunda ajinsu ɗaya,
Tsintar kanta tayi da yi masa murmushi ,haɗe fuskarsa yayi ya mayar da headphone ɗinsa kunnensa ya koma ya rufe idanu,
Azad na ɗaya daga cikin big boys din makarantar wanda ko wacce mace burinta ace saurayinta ne saboda haka ne Allah ya ɗora masa girman kai bugu dakari kuma yana dan masu makaranta shiyasa yaran ke masa fadanci,
Tsaye deenah take bakin board tare da deen wanda yake so su bashi attention ɗinsu kafun ya fara introducing deenah wadda ya umarta ta faɗi sunan ta,
Cikin sakin fuska tace"hello class my name is Deenah Othman ali,
We saw that dummy ,
Ɗaya daga cikin yan matan ta faɗa wanda hakan yasa dukkansu suka kwashe da dariya,
Ba dai tayi kasa a gwiwa ba tana mai san sake magana wata acikin daliban mata tace "
Hey miss scholarship wanne designer company ne suka maki jaka da takalmi,
Ai kamar jira suke yan ajin suka sake kwashe wa da dariya suna faɗin "gucci .
Suna cikin wannan dariyar iskancin aka turo kofar,
Juyawa sukayi baki dayansu dan ganin wanene,
Karar takalmin ta mai tsini shi kaɗai kake ji sannan kamshin designer perfume ɗinta,
Beret ɗinnan a karkace sai expensive black human silk cut wig ɗin dake kwance luf a bayan ta da gefen fuskarta ,
Shigowa tayi tana wani taunar chew gum ɗinta hannunta dauke da karamar hand fan pink,
Necktie ɗinta Kansa ba na makaranta bane something fancy ne"
QUEEN yan korarta suka faɗa inda ita kuma take jin kamar ana fasa mata kai ,
Chan gefen azad wanda idanunsa ke rufe kunnensa a toshe wata yarinya wadda taji ana cewa benaxir ta nufa da saurinta ta jawowa gwanar da ta shigo seat,
Zama tayi tana mai harɗe kafafunta wanda sai a lokacin ta kula da deenah dake gefen deen a tsaye,
Dan murmushin gefen fuska tayi kafun tace "ita kuma waccan sabuwar teacher ce mukayi ne,
Banazir dake gefenta ne tace scholarship student ce,
Yar dariya yarinyar tayi kafun tace ,kuce mun new fun toy"
Benaxir introduce me to the new toy"
Ganin abunnasu bana kare bane yasa deen wanda shima ba sauraransa suke ba saboda kowa naji da Kansa yace "
Deenah use that empty seat ɗazu aka shigo dashi its yours and do not mind them,
Babu musu ta nufi seat din wanda yake daga gefen na deen ,
Tana kokarin zama tajita akasa benazir ta janye,
Tum ta faɗi a kasa wanda a take suka sake fashe mata da dariya,
Sosai taji zafin faɗuwar amma ta danne ta daddafa ta mike ta jawo seat ɗin ta zauna tana mai kallan WIDAD wadda kallo daya ta mata ta gane ta duk da kuwa rabonta da ita tun zuwanta abuja farkon zuwanta gidan,wanda ranar ta tsinci mahifiyar azad na faɗa masa widad suntafi mexico na shekara biyu.Sam widad bata ganeta ba dan ita bama ta da time ɗin da zata tuna ta,
Benaxir ce ta nuna mata widad tace hey little poor kid,Idan kika bi widdy kin haye a orchid saboda babu ya ita idan kuma kikace zakija da ita ki shirya shiga uku so kisan matsayinki na mai mana running errand,
Suna kan maida dariya malamin dake daukar su English ya shigo,
Yar dariyar rainin hankali widad tayi lokacin da yace Good morning class,
A fili tace the oval head is here,
Yana jinta baice mata komai ba sai yayi choosing yayi ignoring nata dan yaran makarantar kamar jira suka ka taɓasu kaji shamaci,
Deenah ya tasa ya ce tayi introducing kanta yana san sanin student dinsa ,babu musu ta tashi ta fadi sunanta ,
Har zata zauna yace mata wane school ta Bari,
Ba tareda kyamar makarantar ta ba tace community school,
Ai take suka kara fashewa da dariya wanda har saida malamin ya daka musu tsawa sannan wasu sukayi shiru amma banda rikakun yan iskan aji,
Ana gama basu karatun malamin ya fita,
Yana fita deenah taji an finciki hannunta an jata waje.CHUCHUJAY.