SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
Tunda deenah take rayuwarta shekara goma sha biyu kenan bata taba sanin ba zainaba ce ta haifeta ba duk da kuwa yarda mutanen gidan kan zageta da hakan amma bata daukan hakan da komai amma bangaren kabiru kuwa ta san bashine mahaifinta ba tunda ko a makaranta ba sunansu iri ɗaya da su salima ba sannan sau da dama yakan zageta da othman yabar masa gadonta na tsiya amma bayan ita babu tsiyar da ya barmasa duk da kuwa da wadataccen dukiyar da ya barwa iyalansa suka danne.
Tsugunne deenah take tana shan dan kokon da aka kawo musu da gari yawaye bayan sun dawo daga makarantar asuba ,zainaba ce ta fito daga ɗakinta falan ɗaya da yanzu ta dawo bayan aurenta da kabiru ɗan yanzu bangarensu na da ya zama na hutawarsa.
Kallanta zainaba ta tsaya yi cikeda tausayinta ,
Tanasan bawa deenah rayuwa mai kyau amma itama bata da wani gata kuma bata da karfi ,
Mahaifinta da mahaifan su othman yayan mace da na namijine,
Gaba ɗaya rayuwarta gidanta tashi sabida ita ko iyayenta bata riska da rai ba,
Sauda dama idan tayi kokarin daukar deenah su gudu a gidan sai tafara tunanin idan ta dauketa sun gudu ɗin ina zasu?
Zama tayi kusa da ita tace deenahn mami maisa kike shan abu a tsugunne bayan nasha faɗa maki hakan bashi da kyau,
zama Deenah tayi tace "wallahi mami sauri nake ne na tafi makarantar gidan gona kar yauma malam ilu ya mun bulalar latti,
Wallahi yana bani haushi mami ni bansan mai yasa kowa baya sona ba ,duk gidan nan ke kadai ne kike sona haka makaranta ma bani da kawaye fa dukkansu kawayen salima ne ,idan wata ta kulani sai su salima su hadu a lungun tsalha su maka duka ,
Haka Malam Ilu ɗinnan wai saurayin salima ne shine take sawa ya zaneni shima ya tsaneni,
Mami kijifa yar salima ɗinnan da duka wata biyar ne ta bani ,
Kallanta zainaba tayi tana mai ɗan murmishi tace ,"deenah na kina wannan zubar ai zakiyi wani lattin da shi malam ilu ɗin zai zaneki sannan dama ai ba kawaye kikaje makaranta ba karatu kikaje ,ko bakiga kinfi ita salima ɗin kokari ba ai saboda ke ba kawaye kikaje makaranta ba dan haka ba ruwanki da wasu kawaye ,
Sannan duk wanda kika ga dama baya kulaki Allah bai tsarasa cikin rayuwarki ba kuma bashida amfani,
Sannan kar na kuma jin kince kowa baya sanki ,ni maminki ina sanki kuma sona ya ɗara na kowa a duniya indai kina da soyayyar mahifiyarki to ta kowa banza ce.
Washe hakora deenah tayi tace "wallahi mami ina sanki sosai ,Allah ya bani kudi,so nake nayi karatu sosai nazama likita na siya miki katon gida na dauke ki daga gidan marna,
Dadine yacika zainaba dan a kullum idan deenah na fadan irin haka sai ta tsinci kanta cikin jin dadi da wata soyayyarta da take ratsata dan ita har mantawa take ba ita tayi nakudar deenah ba,
Rabiatu ce ta karaso gurin da sarsarfa tana faɗin ya deenah kizo mutafi gidan gona mun kusa lattifa,
Jakarta ta dauka tana mai aje kofin kokon tana cewa"mami sai na dawo".Kamar yarda deenah ta guda suna zuwa kofar shiga makaranta gwamnatin dake cikin garin na kan tudu malam ilu yana kwafe a bakin gate din shiga hannunsa da doguwar bulalar bedi,
Suna zuwa bakin gate din yace "uwar yan latti anzo kenan maza zo ki dage mun wandanki na zane wadannan kafafun masu kama da tsinsiya,
Kuka ta fara tun kan ya fara dukanta amma duk da haka ko kadan bai ji tausanta ba ya zane kafafunta inda rabiatu ke gefe tana ta challara kuka kamar ita yake duka ,saida ya zane mata kafafu tas kafun yace su shige.
Haka ranar ta gama jinyar kafafu wanda salima da kawayenta sukayi ta tsokanarta a makaranta.Suna zaune kan tabarma zainaba na shafa mata man zafi a inda take fadin yana mata ciwo kabiru ya shigo ,
Fancham fancham ya karaso gurin yayi fatali da kwanon da zainaba ta aje mata dan waken da ta siyo mata kafun ta dawo daga makaranta,
A tare suka tashi sakamakon ɓata sun da yayi,
Zainaba ce tayi karfin hali wajen faɗin Alhaji lapia kuwa,?
Kamar jira yake ya fara kumfar baki yana faɗin"ban sani ba ,ban sani ba nace miki zainaba ,ko zaki dake ni ne eye?
To wallahi ni nagaji da daukar nauyin wannan shegiyar yarinyar ,ko ku fito da miji ayi mata aure ko kuma na kaita gidan marayu ,
Ina dalili yarinya kullum a cikin neman mun magana take ,nan nan yanzu ladi ke kawo mun kararta akan tana zuwa lungun gidan almajirai ɗakin samarin nan to wallahi da ta dauko mun abun magana gwanda nayi maganin abu''
Cikin kuka deenah tace"wallahi baba karya ake mun wallahi tallahi ni layin lungun almajirai ma bana bi ko aikena akayi kuma nasan salimace zata faɗawa baba ladi haka walllahi na rantse da Allah baba karya take ,
Kamar jira yake yayi kanta yana cewa au matar tawa kike cewa tana karya dan uwarki gayyar tsiya ?
To Bari na fasa maki baki sai uwarki da ta gudu ta barki tasa babanta mai kudi ya ɗaureni shegiya gayyar tsiya,
Gabansa zainaba ta shiga ranta a mutukar bace tace wallahi baka isa ka daketa ba yau kabiru sai dai kabi ta kaina idan har zaka daketa,Tsaye yayi yana mai kama kugu yace kabiru?
Ni kike faɗawa kabiru ko zainaba ?
To ko mijinki baya cemun kabiru gatsetse sai ya sakaya,amma yau zaki gane ni ba sa'an wasanki bane,
Kafun tace me ya fara kai mata hannu ,
Kuka deenah take a bayansa tana basa hakuri ganin yarda yake naɗar zainaba amma hakan bai sa ya bari ba ,
Wasa wasa saida yayi mata ligif sannan yace ta tattara ta bar masa gidansa ya sake ta Saki biyu dama ta ishesa.
Duk wannan bidirin da ake babu wanda ya fito a cikin gidan dan kawo mata dauki ko basa hakuri duk da kuwa sunajin duk wani abu dake faruwa .
Barin gidan yayi bayan ya lillisata yace kafun ya dawo kuma ta tabbata tabar gidan,
Kallan deenah tayi wadda kukanta yaki yankewa yace "kukan kuma wai na menene haka ?
Ba komai ya wuce ba ,
Share hawayenki yanzunnan ,zan ɗaukeki muje gurin da kowa zai soki ,gurin da babu wanda ya san mu ma bare ya tsangwamemu,
Cikin rashin fahimta tace "yanzu mami kina nufin kowa da kowa zamu bari danginmu muyi nisa sosai da su?
Ni dai mami duk da basu sona amma kar mu gudu nan ne gidan mu idan mun gudu su baffa baza suji dadi ba,
Kallanta zainaba tayi tana mai maida hawaye dake neman kwace mata ,
Tasani Allah ya azurta deenah da zuciya mai kyau duk da ita din yarinyane amma duk da haka bata jin kin yan uwanta ,
Sauda dama takan mata korafi na rashin santa da basuyi amma yau gashi tana fada mata zata dauketa su gudu amma tunanin ta na kan danginta.
Tana tsaka da wannan tunanin taji hayaniya na dosu sashen su,
Jan deenah cikin ɗakin tayi ta kulle kofa dan tasan wata tsiyar ce ke dososu ,
Kamar yarda tayi tsammani kuwa matan gidan ne da wasu daga cikin mazan dake gida ciki kuwa harda mahaifin othman da kabiru wanda muryarsa tafi ta kowa tashi yana mai faɗin,"wallahi baffa wannan matar ni kaina mamaki naji da na shigo wai da tsakar ranar nan ta kawo mun kwarto shiyasa nikuma baffa na kasa dannewa na saketa sai kuma daga baya nake tunanin ku da kuma abunda zakuce idan kukaji na saketa dan nasan kuna santa banda zabi ne".Maihafinsu ne da ya manyanta sosai a yanzun amma zuciyarsa na nan tsatsaura yace "ni ai kamun daidai kabiru me ake da baragurbi?
Maza ku buga mata ta bude a yanzu yanzu ta bar gidannan dan zuri'ar marna bata da abun kunya kuma baza mu fara akanta ba ,
Tana jinsu ta jawo jakar kayanta ta hade dana deenah dan tasan babu shakka zamanta gidan ya kare ,har ranta taji kunar sharrin da kabirun yayi mata taji ba dadi sosai kuma bata tunani akwai ranar yafiya tsakaninsu saboda taso ace koda zata bar garin yazamana da darajarta tafita amma a yau kabiru ya zubar mata da wannan darajar sannan gidan marna ba gida bane da ake sauraran mace ta yi bayani na nata bangaren.
Ajiyar kudinta da take da akwai boyayyiya ta bankado a karkashin gado dama ta boyene saboda rana mai kamam ta yau wadda tasan zata zo koman dadewa ,
Sokesu tayi a habar zaninta sannan ta kara bankadawa ta dauko dan kunnenta na zinare wanda othman ya siyan musu ita da maimunatu wanda babu wanda yasan da wannan kyautar,
Duk wannan abun da take deenah na tsaye tana hawaye musamman muryoyin da take jiyowa a waje suna zagin mahaifiyarta,
Shahada kawai zainaba tayi ta bude dakin, ai kamar jira sukeyi su ka hau mata tofin Allah tsine,
Babu abunda tace illa jan hannun deenah da tayi suka fice a gidan baki alaikum inda babu wanda ya dakatar dasu daga tafiya din.CHUCHUJAY