Chapter 31

99 9 0
                                    

KALUBALENAH.

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

31

A hankali deenah ta fara sakin jikinta da situation ɗin da ta tsinci kanta saboda yarda take samun soyyayyar binyamin a duk yarda take santa ,ta yarda dashi dan ta kuma sakin Jikin ta akan bazai ci amanarta ba ,

Kamar kullum ta gama shirinta na zuwa makaranta ,akai akai takan duba agogon dake makale akan kyakkyawan tsintiyar hannunta ,
Dan karamun tsaki tasa sabida she's getting late already ga uban tafiyan nata kuma yaki fitowa ,
Takun takalmin sa ne yaja hankalinta ta ɗaga kai ,
Daure fuska tayi lokacin da ya bayyana gareta ,
Karasowa yayi yana murmushi dan yasan yayi laipi ,
Jakarta ta ɗauka ta kara haɗe rai ta juya,
Rungumeta yayi ta baya yayi kissing wuyanta yace "im sorry dee nasan nayi laipi naƙi shiryawa da wuri amma Kinsan other way round laipin kine kema cos ke kika hanani bacci jiya kwata kwata cos yanzu kema kinzama irina kinga maja kenan,

Kwace jikinta ta fara yi jin abunda yake faɗa wanda tasan tsokanarta ne yakeyi,
Jawota yayi yana Mai rike dariyarsa yace "im sorry baby tuba nake muje to .

Har suka shiga harabar makarantar bai daina tsokanarta ba Dan tun tana cin magani har ta dawo ta saki ranta tana biyesa tana ramawa .

Yana parking motansa wata Bakar RR ta faka a gefensu ,
Deenah ce ta fara fitowa inda shima ya fito yana Mai kara tsokanarta yana faɗa mata babyn baby".

Budewa motan da ta faka gefensu tayi inda matar dake tuka motan ta fito,matar ranannace ,da fara'a ta kalli binyamin lokacin da idanunta suka sauka kansa ta nuna sa da yatsa tace "binyamin ko?

Da nasa mirmushin ya amsa yace eh ,aunty ina kwana,
Kara faɗaɗa fara'ar fuskarta tayi tace ashe zan gane ka ya gida yasu amminka ,it been a long time gaskiya,

Lapia kalau"ya bata amsa ,

Kallanta ta mayar kan deenah tace ,i remember you" lady din da mukayi gware ranan ba ,
I couldn't get you out of my head ashe zamu sake haduwa ne is she your ?

Distance cousin ya bata amsa cikin sauri cos yasan tasan ammin sa and last abunda zaiso yanzu shine ammi tasan aurensa ,

Au Masha Allah kina karatu anan ba ,
"
Eh deenah ta bata amsa tana Mai jin matar har ranta,

"Allah ya bada sa'a ya taimaka ,
My office is on 5th floor ,MRS MAIKANO written boldly ,just come to me when ever you need anything.

Sallama ta musu ta bar gurin,
Kallan binyamin Deenah tayi tace "last i remember cewa kayi idan ka sake haduwa da ita zakace im yours ashe ma you're just a coward,im tired of this hide and seek already ,
Kafun yace wani abun ta bar gurin,

Dan murmushi yayi dan shi kadai yasan yarda zai shawo kan Yar matarsa .

MRS MAIKANO,staff member ce a school ɗin,mijinta babban maikuɗine wanda ya rasu ya barta da arziki mai yalwa,duk da cewa ita ɗin yar masu arziki ce ,ɗansu ɗaya farouk wanda duka duka yanzu shekarunsa biyar,bata da bukata na wani salary da za'a biyata amma kasancewar ta mutum wadda bata san keɓewa ita kaɗai yasa ta nema aiki a nan orchid din wanda gladly ta samu gurbi mai girma.

"""""""Tunda deenah ta shiga uni bata da wata ƙawa kuma bata da niyar yin ƙawar saboda bashi ne ya kawota ba sannan bata san koda wasa wata ƙawar ta shiga jikinta ballantana ta gano sirrinta,

Tana zaune a cafeteria tana cin abinci sakamakwan wata yunwa dataji Tana ji after lecture din afternoon ,cos akwai na four dan haka she needs food,

ƙaran wayanta ne Ya katseta daga loman abincin da zata kai bakinta,
Sabs ke kiranta facetime ,da murnanta ta dauka inda sabs ta bayyana tana mai fadin"baby girl.

Baby girl deenah ta fada tana Mai nuna tsantsan farin cikinta cos tunda sabs ta tafi basu taba facetime ba cos bama ta da lokaci dan binyamin ne kawai a gabanta yanzun,

Wait beb I'm not understanding naga kinyi wani kyau kinyi fresh mene sirrinne,

Dan blushing deenah tayi tace"im out of stress na trouble ɗin sister ɗinki mana ba dole nayi fresh ba ,talking about her ,how is she?

"Ever been told that you're kind?
Sabs ta tambaya tana mai kurawa deenah ido ta cikin screen din,

Fahimtar abunda take nufi yasa deenah cewa "you just did "
And yea ni you know me best i don't hold grudges ,i hope She's coping 

"Well Yea ,she's bitching a little bit amma yanzu she's coming around bata daɗe da fita bama ,
Kinsan widad bata bakunta duk inda zata ,she even make some friends amma ni kam as you know i will always be loyal ma"

Dariya deenah tasa jin abunda sabs tace tace nima im loyal kar ki damu bamai daukan gurinki,
Kuna magana da azad kuwa he cut all contacts.

Yea munyi magana sau daya but after that ban sake ji daga garesa ba i guess everything is okay sha,ina masoyinmu da yayi ma yayana kafa.

Masoyina dai ,deenah ta faɗa da sigar tsokana ,
A tare sukayi Dariya ,
Sun jima suna hira wanda hakan ya kashe ma deenah time har lokacin last lecture ɗin taga yazo mata da sauri.

*********************************

Tunda ta dawo gida bata ganshi ba Dan yau da kanta ta koma gida sakamakon kiranta da yayi yace ta wuce sakamakon aikin da yayi masa yawa ,

Gyara ko ina tayi na gidan kana ta dora doya cos tana da liver sauce warming kawai zatayi,
Wankanta ta ɗanɗasa bayan ta gama komai ta hakimce kan kujera tana jiransa tana Mai adduan Allah yasa kalau dan wayansa ma baya shiga,

Ringing wayanta Ya fara,
Mami ce Mai kiran ,dafe goshinta tayi da ta tuna fa yau kwata kwata bata kira Mami ba wanda daily routine ɗinta ne ,
Waya sukayi cikin soyayya irinta ƴa da uwa,
Duba agogon wayanta tayi lokacin da takare waya da Mami taga karfe 8 na a dare ga babu shi babu alamunsa,

Wuraren karfe goma lokacin ta cika tayi makil message ɗinsa ya shigo inda yake faɗa mata wai ta kulle gida cos bazai kwana nan ba ,

Tashi tayi ta kulle ko ina ranta na mutukar Kuna ,babu abunda ya kuma bata mata rai kamar message din da yayi mata maimakon ya kirata ,
Duk wani tsoro da take tunanin zataji take ta nemesa ta rasa saboda fushi.

Washe gari dama ba makaranta zata ba ,yunwar cikinta ta tashe ta ,kai tsaye kitchen ta nufa tayi warming doyan da ta dafa masa kana ta haɗa coffee,
Tana kan ci taji ana ma kofa key,
Dauke idanunta tayi daga kallon kofar ta mayar kan abincin da take ci,

Da sallama abakinsa ya shigo falon hannunsa a kan kunnuwansa ,
A kasa yazo Ya zauna gabanta yana Mai pouting lips,
Ko kallansa batayi ba.

Kara matsawa gabanta yayi yace baby"im sorry ,nayi laipi amma tuba nake,
Tashi tayi da niyar bar masa gun,
Kamota yayi yace "Dee please mana ki saurareni ko sau ɗaya ne,
Wallahi i was trapped ammi ne ta Sani gaba akan bana kwanan gida tana sane dani so jiya nan sai da nayi bacci tabar dakina bansamu daman kiranki ba dole sai text.

Kwanakin da sukayi tare yasa tayi wani irin sabo da shi a kusa da ita har ta kaita da tana manta auren su ba sannanne bane,amma ai bazai iyu su dauwama ahaka ba ,idan kuma ammi ta hanasa zuwa baki daya fa yazatayi,
Wannan tunanin ne Ya Kara harzukata tace "ni gaskiya Im ready yakamata ace mun bayyana aurenmu cos Allah shaida nane i can't be here alone without you i can't even phantom the thought so ni ashirye nake da daukan komai indai har iyayenmu xasu amince da auren mu.

Gabansa ne Ya Faɗi musamman da Ya tuna babban dalilin ma da ya kaishi gidan har ammi ta tarfasa,
Wasu ta kardu Ya dauko ya bama ammar da zai wuce and team dinsu ya kirasa akan contract din da ya cike na 8 months da zaiyyi ,tunkan ya hadu da deenah ya cike wanda da yasan zai hadu da ita bazai taba cikewa ba and gashi nan da kwana biyu ake bidarsa gashi babu yarda zaiyyi yayi terminating cos ya riga yayi,
Tunanin ta yarda zai faɗa mata yake tuntuni amma reaction dinnan nata akan kwana daya da yayi baya nan ya zata kasance idan ta san zai tafi na wata takwas kuma fa?

Koma dai yaya ne yazama dole ya sanar da ita ta yarda zata fahimta,
Zaunar da ita yayi akan kujera shima ya dawo ya zauna kusa da ita dan wannan aiki yana bukatar ya kakaro dukkan basirarsa,
Rike hannayenta yayi yace Dee listen,
Ni kaina Bana jin dadi idan Bana tare dake Allah ya sani amma yanayi shike jawowa ,
Kalla Dee akwai abu Mai amfani danake San sanar dake...

CHUCHUJAY.

KALUBALENAH✔(free novel)Where stories live. Discover now