1

1.2K 81 11
                                    

GOBE DA LABARI 🔊1

Batul Mamman💖

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalam alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.

Wannan littafi za a same shi akan manhajar ArewaBooks da Telegram.

Ga masu son saya zasu iya saka kudi ta wannan account din.
FCMB
Fatima Bello Salim
0908188010
N1000
(Sai a tura shaidar biya ta whatsapp ga wannan numbar 08129771791)

Idan kuma katin waya ne sai a tura katin MTN na 1000 ta wannan layin.
(08060823810)

Mazauna Nijar ga numbar da za ku yiwa magana domin biyan 1000c cf
Sister Massouda
(+22790663440)

Posting zai cigaba ranar Juma'a, 20/1/2023. Wannan zai bada isashen lokacin sanya masu biya a telegram group din. Allah Yasa mu fara kuma mu gama a sa'a. Amin

Nagode


Shimfida

Tabbas garin Abuja da ake yiwa lakabi da birnin tarayya yaci sunansa idan aka yi duba da yawan kabilun dake cikinsa. Kaso mafi yawa na ma'aikatan kasar sun fito daga jihohi daban daban ne. A cikin al'ummar da garin ya tara ne zamu tattaro manyan jaruman da zasu ja ragamar labarin nan mai suna GOBE DA LABARI.

Indai mun yarda ba a fafe gora ranar tafiya, to wajibi ne tanadin ruwan wanke tukunya domin tuwon gobe. Kullum muna fatan ganin da kyau, to amma wane yunkuri muke yi domin tabbatuwar hakan?

***

     ZABABBU

52 Mike Akigbe Way
Jabi, Abuja
The Nordic Villa

A duk lokacin da wani abu ya tunkaro dan Adam yana yi masa barazana da rayuwarsa, sai yaga kamar duk duniya babu abin da ya kai shi mahimmanci. A inda imani ya yi karanci ko wahala ta kaiwa mutum wuya ma babu abin da ba zai iya ba domin kawar da matsalar. Misali, tsadar kayan masarufi da karancin albarkar gona yana sa mutane ganin kamar abinci shi ne jigon rayuwa. Bullowar annoba, yajin aikin likitoci da rashin wadatar arzikin neman lafiya idan ya taso mutum a gaba sai ya rantse kowane mai lafiya sarki ne. Wanda talauci ya hana kumbar susa gani yake kamar yafi kowa shiga halin kaka-nika yi. Amma a yayinda rashin TSARO ya zama labarin yau da gobe a wani yanki, to lallai sai ya mayar da duka wadancan lalurorin nafila. Sai kana cikin ahalinka kake tunanin yunwa, talauci da rashin lafiya. Tattauna wadannan batutuwa shi ne makasudin bayyanar wadansu motoci guda bakwai farfajiyar The Nordic Villa da karfe goma sha daya na daren lahadi. A jere suka shigo, kowacce da tint a jikin gilasanta ta yadda na waje bai isa yace ga matukinta ba balle fasinjoji. Sha daya da minti goma daidai duka kofofin motocin suka dinga budewa ta hagu da dama. A lissafi mutane goma sha daya ne cif suka fito. Mata uku, maza takwas kowanne fuskarsa sakaye da takunkumin fuska bak'i (face mask). Daga yanayin suturun jikinsu da ma tafiyarsu ake gane su din wasu ne ta fannin aljihu sannan kuma da alamun sun zarce shekarun samartaka.

Haske ya wadata kayataccen koridon da wani matashi wanda ke sanye da shirt mai sunan hotel din da bakin dogon wando ya nuna musu. A jere kamar masu yin layi suka bi bayansa har cikin wani madaidaicin dakin taro (conference room). Daki ne mai fadi da dan tsayi wanda babu komai na kyale-kyale a cikinsa sai abin bukata kamar firij, dispencer da wani madaidaicin kabinet dauke da kwanuka (plates) da kofuna. A tsakiyarsa akwai katon tebur mai fasalin kwai (oval) wanda yake da kujeru goma-goma suna fuskantar juna hagu da dama. Kujerun dukkaninsu iri daya ne masu kyau. Sai guda daya daga tsinin tebur din ce ta bambanta da sauran a girma da kala. Wannan yake nuni da cewa nan ne mazaunin shugaban taron wanda kuma mamallakinta a wannan zaman da ya riga ragowar jama'ar isowa yake zaune a kanta. Fuskarsa a bude take ya janyo tasa facemask din kasan habarsa ta rufe sajensa mai sirkin bakin gashi da furfura yana rubuce-rubuce. Sanye yake da suit ruwan toka da riga 'yar ciki ruwan madara. Wuyansa da necktie mai ratsin layi layi baki da ruwan toka. A dan murmure yake na rashin yunwa amma babu kiba ko kadan sai tsayi. Bafullatani ne na ganin ido ko bai yi magana ba. A bayansa wani dan karamin tebur ne wanda aka dora laptop din da aka jona mata wayar majigi (projector). Wani mutum ne wanda shekarunsa basu kai nasa ba yake aikin daidaita fuskar majigin domin duka mahalartan su gani da kyau idan sun zauna.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 02, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GOBE DA LABARI (Paid)Where stories live. Discover now