*_K I K U L A N I_*
_(MALLAKIN ZUCIYA)💕__N A N A H A F S A T_
_MSS XOXO_
_F R E E - P A G E :003_
______*Da* sauri ta sakale kofar da dan kyallen da ta ke rufe kofar da shi a matsayin kwado. Ta janyo yaran nata jikin ta bayan ta koma ta zauna hadi da jingina bayan ta da bango..
"Zo nan Hadiyyah..." Ta riko hannun 'yar tata macen tana rarrashin ta. Yayinda mazan biyu ke rakube da ita suna ajiyar zuciya.
"Kuyi hakuri .. Allah ya mu ku albarka. Ya raya ku. Allah ya azurta ku . Ku tumbatsa har ku temakawa na kasa da ku. Allah ya baku ilimi mai amfani wanda zaku yi aiki da shi ." Ta karasa fada hadi da janyo su duka ta rungume su. Hawayen da ta makale suka shiga zurara daga idanun ta.
"Ki.. Dena kukka." Haidar ya fada yana kokarin share mata kumatun da hawaye ke tsiyaya.
Hammad da Hadiyyah ma suka shiga goge mata daya idon da hawayen ke zuba kadan kadan .
"Toh yan albarka...Na de na." Ta karasa fada hadi da matse su tsam a jikin ta.
Kan ta ne ya shiga sara mata sosai. Ta dan kwantar da kan nata a jikin kwalla. Ta ke bacci ya dauke ta. Tun yana daukar ta ahankali yaran na tashin ta. Har ya dauke ta baki daya. Ya yinda su ma sannu a hankali ya dauke su.
××Sun dau tsawon lokaci suna bacci kafin daga bisani Fadila ta fara farkawa.
A hankali ta janye su daga jikin ta. Hadi da gyara musu kwanciya. Tsayawa tayi tana kallon su suna sauke numfashi ahankali.
Gumi sai tsattsago musu yake ta goshi da wuyan su. Kasancewar zafi ake yi. Gashi dakin a tsuke ya ke ba masaaka tsinke.
Dankwalin ta da ke gefe ta ja ta daura akanta. Ta dauki muhucin da ke kasan dankwalin ta shiga fifita musu shi .
Ta dan jima tana musu fiffita. Dai dai lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar azahar.
Wata yar roba dauke da ruwa ta janyo ta tsiyaya a yar karamar butar ta. Kafin ta bude kofar dakin ahankali ta fice zuwa wajen tsakar gidah
Bandaki ta shige da sauri ta rage cikin ta. Sannan ta fito waje ta fara alwala. Tana yi tana kakkauda kai gefe da gefe saboda gudun fitina.
"Kai Kai Kai... A'ina kika samu ruwa? Cabdijan Malam fito nan." Ladiyo da ke tsaye kerere akan Fadila ta yage baki tana mai sake kiran,
"Malam wai kana ina ne?"
Fito da kansa yayi ta kofar dakin sa yana yamutsa fuska .
"Menene wai? Iyye?"
"Ruwa naga Fadila na amfani da shi. Kuma dai banga ta saya ba."
"Ke ... Wane dan jakar uban ne ya baki ruwa?"
Fadila ta kasa cewa komai. Ruwa ma batada ikon mallaka batare da an nemi ba'asin a'ina ta same shi ba.. Ruwan ma sai dai ta cire kudi ta saya guga daya nera ashirin a rijiyar gidan da Ladiyo tasaka a ka haka kafe ta tsare wai ta zama mallakinta.
"Kaga tayi shiru ko? ... Ai na gayan ka sata tayi. To wabillahi.."
"Wallahi ban diba miki ruwa ba. Anas daya shigo gidan nan jiya shi ne ya ebo mun a waje bokiti uku."
"Yana ina dan bankadaddiya? Wannan yaro wannan yaro ba dan ni na haife shi ba Allah ca zan ba jini na ba ne. Dan kan uba." Ta karasa fada hade da dankarawa Fadila harara.
"Allah ya baki hakuri."
"Da hakuri yayi gabas. Yamma nayi matsiyaciya. " Ta buga tsaki ta shige daki.
YOU ARE READING
KI KULA NI!!! (MALLAKIN ZUCIYAH)💞PAID NOVEL..
General FictionTUN RAN GINI TUN RAN ZANE... LABARI MAI TAFE DA WANI SALO NA DABAN. WANDA YA KUNSHI RASSA DA DAMA NA RAYUWAR BIL ADAMA. KUMA BABBAN JIGON LABARIN ZALLAR KAUNA CE WANDA ALLAH KE DASAWA ZUKATA..💞FIND OUT MORE IN....... KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYAH)💞...