26

537 22 1
                                    

EPISODE 2️⃣6️⃣

Jama'a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/

Shuku Anty Binta tasa akamata mai bala'in kyau, mai style yan kanana nan da nan tayi kaman ba itaba, tasa aka wanke mata kumbunan kafa da hannu Anty Binta sai kallon yatsunta take both nakafa da hannu sunada bala'in kyau gasu so chubby sannan yatsun farare dogaye, mace mai ni'ima kana iya ganewa daga yatsunta both na kafa da hannu, bakaramin addu'a take kan Ya Imran yafara son yarinyar nan ba dan Lujain is a gift from Allah, kyautanta Allah yamai bayan wahalan rayuwan dayayi, 13yrs ba mata sai zaman kadaici da bautan Allah saisa Allah yabashi Lujain cus babu abinda Lujain batadashi gatada shiga rai, bala'in shiga rai, daga zuwanta saloon din nan harsun fara sonta, mai saloon din harda cema Anty Binta tanason sister nan nata tamata influencing saloon din nan adauki pictures nata zata biyata da kyau, saida tanuna musu matan aure ne mijinta bazai yarda ba sukabar zancen.

Biyan kudi sukayi sannan suka fito wani babban super market sukaje jakunkuna Anty Binta tasaya mata da takalma masu kyau da yankune da agogo, bracelets irin na yanmata dinnan, da kayan sawa english wears masu kyau sosai su sexy gowns, shorts, shirts, jeans dan sotake tadinga sawa Ya Imran yasoma dawowa hayyacinshi, takara mata abayoyi, da turaruka, harzasu fito tace "Anty su Chocolate" wajen chocholate sukaje sai alokacin Lujain tafara deban chocholates dasu biscuits dabama tasan dasu aduniya ba ita Anty abin dariya ma yabata tace "ai saisa kike kiba sweet tooth ni mutafi" biyan kudi sukayi aka kaimusu kayan mota sannan suka tafi bayan magrib suka shigo anguwan Anty Binta ke tuki gidan dake kusada nasu sukaga an bude ana shiga da sababbin furnitures Anty Binta tace "kowaye yasai gidansu Maman Adam oho" kallon gidan Lujain tayi dayake abude sai gyare gyare ake har fenti anyi, Anty Binta dake tuki tana kallon gidan tace "Maman Adam makotan mune sunada kirki gidansu ne amman sun saida sabida mijin zai koma US yasami aiki a chan" daidai anbude musu gate suka shiga cikin gidan, parking tayi suka fito zare hijab din school Lujain tayi tadauki ledan chocholate dinta tayi gaba mai gadi natayasu daukan sauran kayan sallama tayi tashigo falon ahankali daga Hajiya sai Musty da Abee afalo Musty ne ma yadago shi daga masallaci dabai shigo gidan ba sai bayan isha'i, kallo daya Abee yamata yadauke kai Hajiya tace "yan makaranta an dawo" Gyadamata kai tayi batare data karasa wajen ba tace "ina wuni" sannan takalli Musty ahankali tace "ina wuni" murmushi yamata yace "lpy lau" Hajiya tace "aiko kitson yay kyau mekika riko mana a leda" ledan takalla for the first time dan murmushi tayi tace "chocholate dina ne" dan dariya Hajiya tayi tace "sabida bakiso kibani ne kike cewa chocholate dinki ne ai shikenan jekisha Lujain" akunyace tadan sunnar da kanta kasa kaman mai koyon magana tace "Allah ni zan baki Hajiya" shi kanshi Musty dan murmushi yayi jin yanda tai maganan Hajiya tace "to nagode Allah amfana jeki cire kayan makarantan saikizo kici abinci" Gyadamata kai tayi tawuce sama, tana shiga dakinta taga jakan school nata an ajiyemata waje daya, bayi tawuce tacire kayan school nata tareda jefawa a washing machine sanan tai wanka da ruwan zafi tafito daidai Anty Binta na shigowa dakin rikeda manyan ledojin kayanta Maman Aneesarh ma natayata dan kallon Lujain din Maman Aneesarh tayi yanda kitson yamata kyau tace "Ya school"? Ahankali Lujain tace "lafiya lau ina wannan baby"? Murmushi Maman Aneesarh tayi tace "tayi bacci" sannan tawuce tafita daga dakin, Anty Binta saida tajera mata kayan tass dan ita bata salla sannan tawuce tafita itakuma tana idarwa zama tayi kan gado tabude ledan chocholate nata tashiga sha saida tasha daban daban kusan guda 7 sannan ta tashi tasakeyo alwala tafito tahau kan dadduma tana salla shigowa Anty Binta tayi ta ijiye mata abinci a kula tana idarwa taci batawani ci dayawa ba sabida yanda tasha chocholate din nan hawa gado tayi ko 3min batayiba sai bacci danta gaji.

SAKON SOWhere stories live. Discover now