5

765 26 0
                                    

EPISODE 5️⃣


Ahankali cikin muryan bacci wata kalan siririyan murya mai shegen dadi da zaki tace "Gwaggo yunwa" shiruu kakeji banda sound na munshari dake tashi acikin duhun dakin, cikin wani irin raw voice din nan dake nuna bacci mutum yake ko cikin bacci mutum yake maganan tace "Gwaggooooo yunwaaaaaa!" Firgigit munsharin dake tashi daga dakin dakeda duhu nan ya tsaya kaman anyi ruwa an dauke karan hannu kawai ketashi daga dakin dake nuna ana tattaba gadon alamun abu ake nema sai chan aka kunna wani bright torchlight daya wani kalan haska dakin bauuuu kaman wutan lantarki, wata tsohuwar mata ce da akalla zatai 70 kokuma 72 haka kwance kan wani makeken gado mai kyau tana sanye cikin riga bubu da zani na atampa gefenta kuma wata yarinya ce mai jiki sosai kwance ta kankame Yar tsohuwar kaman zata koma cikinta idanunta akulle tana daure da wani pink towel, kallon fuskanta yar tsohuwan tayi tace "Ohh ni Safara'u Allah ubangiji ka nunamin ranan dazanyi bacci tundaga farkon dare har karshe batare da wannan fitinanniyan yarinyar ta tadani tanajin yunwa ba, Ya ubangijin sammai da kassai Ya ubangijin dake busa numfashi rokonka nake Allah ka kawomin ranan nan da gaggawa" cikeda takaici tace "aisai kitashi ga shayinki chan cike a flask, namanki da somasa nacikin kula, buredi ma na wajen idan kuma harda shinkafa zakici to wlh dakanki zakije kitchen kidebo dan kin ganni nan ban barin gadon nan Lulu" still cikin baccin batare data bude idanunta har lokacin ba tace "Gwaggo wlh ki kawomini nan" tai maganan kaman mai shirin kuka dayasa babu shiri Yar tsohuwan takai hannayenta ta kabarda hannunta dake kan jikinta tace "aisaiki sakeni intashi yarinya kaman jikan mayu" tashi daga kan gado tayi tasauka tawuce wajen da flask da wata katuwar kula da cup da duk suke kan faranta ta duka da kyar ta dauka tazo gaban gadon ta ijiye sannan ta kalleta still idanunta arufe suke tace "tashi to kici" kaman jira take ahankali ta tashi zaune idanunta still arufe tana rike da gaban towel dinta dake shirin zamewa sannan ta gyara daurin zanin da kyau tana turo baki tashiga bude idanunta ahankali, wasu hadaddun kitson kalaba ne kan yarinyar dasuka zubo mata har tsakiyan baya an jera beads a bakin kitson kaman wata Yar yarinya, wani kalan kibane da yarinyar bana wasa ba, irin asalin yaran nan ne da ake kira da chubby, idan kaga jikinta zaka dauka she's about to burst ne dankoni dazu dana ganta kwance kan gadon nadauka Babba ne sai yanzu dana kalli fuskanta Nagane yarinya ce da duka duka bazata wuce 19-20yrs ba, wasu kalan cat sexy eyes gareta dayasa idan ka kalli fuskanta saika kasa janye idanuwanka akanta for some seconds sabida kyawun idanunta, tanada cikan gira kuma baki sidik hakama gashin idanunta da dan siririn hancinta, tanada kumatu rubu rubu dasu that looks super cute on her dawasu kananun succulent pink lips da kana kalllonta yana bada all this kananun jariran yaran nan dakeda kiba din nan sosai, skin dinta is like butter ne ko milk banmasan yanda zan siffanta muku ba but kaganta zaka dauka idan ka latsa jikinta jini zai fito ne, everything about her is chubby harta yatsun hannuwanta dana kafafunta burbur dasu kaganta kaman zata fashe, sauka tayi ahankali daga kan gadon tana kara gyara daurin towel dinta da kyau sannan akan soft carpet din tana bude flask din ahankali duk cikin bacci itakuma Gwaggo tawuce tabude bandaki tashiga. Shayin tazuba cikin wani babban cup dayaji madara da Milo yana tururi sannan tabude babban kulan samosa ne kusan 20 aciki da naman kaza da akai pepper chicken dasu guda 5 da sauri tashigaci tass ta shanye shayin kofin takara bude flask tadeba tacika tacigaba daci itakuma Gwaggo tafito ta shimfida dadduma kawai tahau tass ta shanye shayin da samosan da duka naman gyatsa tayi sannan ta tashi tahau gado ta gyara kwanciya ta kwanta murya chan kasa cikin bacci tace "Gwaggo kizo mukoma bacci" hararanta Gwaggo tayi tace "nafila zanyi gwarama kiyi baccin ki dan kinsan da asuba zan tadaki yau monday zakuje iskuko oho dai amakaranta" dan gajeren tsaki yaja tanajan bargo ahankali akuma shagwabe tace "ni bazanje ba Mandawari na zaiyi live broadcast karfe shadaya na safe yau" hararanta Gwaggo tayi tace "asheko dake da shegen gantalallen Mandawarin daharyau baimasan ko akwai mai kamanki aduniya ba babanku zai hada yaci ubanku" murguda baki tayi tareda lumshe ido kafi kacema bacci yay awon gaba da ita ganin haka itama Gwaggo ta kishingida da bango danta dan runtsa kadan tasan inhar batahau ba nan bada jimawa ba zata tashi da kanta dan Lulu bata iya bacci bataji ta rike mutum ba tun tana yar kankanuwan ta take haka.

SAKON SOWhere stories live. Discover now