40

767 22 0
                                    

EPISODE 4️⃣0️⃣

Jama'a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Dago manyan idanunta tayi ta kalleshi yanda ya tsareta da idanu yasa takai bayan hannunta tagoge fuskan nata tass murya chan kasa tace "sabida nace zan bita idan zata koma gidan mu" tunda take maganan lips nata da kumatu yake kallo, dauke kai yayi yace "jeki cemata nace takara miki" dasauri tadago idanunta takallai, wani mugun kallo yamata yace "tunda bakijin magana, what did I tell you about this thing" yay maganan yana pointing towel na jikinta da hannu, dasauri ta tura kofan dakin tashiga tareda maida kofan yarufe girgiza kai kawai Abee yayi yawuce yatafi dakinshi.

Tunda Gwaggo tashigo gidan gidan yakara wani kalan dadi da annashuwa Baba yay kiran dubiyan nan Gwaggo taki dauka wai ita barata komaba saitagama hutun datazoyi agidan nan koda wasa kuma babu wanda yataba muna ta isheshi koyagaji da ita saima dawowa datayi kaman itace asalin Gwaggon gidan.
Kullum dare Gwaggo saita kadata dakin Abee dakin Anty Binta take zuwa ta kwanta dan Anty Binta ta tafi gidanta babu kowa adakin, ita rabon datasa Abee a idanu tun ranan Sunday dan Hamza ne ke kaita school yanzu, hakama Mandawari abin bakaramin damunta yayi ba bata ganinshi gashi babu halin taje koda kofar gidansu ne dan ba fita takeba.

Yau juma'a Baba cire kunya yayi shida Hadi sukazo har gidan bayan magrib awaje suka tsaya dan gani sukayi Gwaggo batasan abin kunya ba tazo gidan da jikanta ke aure ta tare tun ranan asabar haryau juma'a kwananta shidda kenan haba mana ai bai daceba.

Abee na masallaci Abdallah yazo yakirashi baiwani jimaba yafito tareda Abdallah har zuwa wajen su Baba cikeda girmamawa Abee ya gaidasu, Baba shima cikin mutunci yace "Imrana dan Allah kuyakuri da halin Gwaggo wlh fitinace da ita haba tazo ta tare taki tafiya" dan murmushi Abee yayi yace "bakomi bismillan ku" dasauri Baba yace "ai muna nan munriga munsa maigadi yakirata ta fito mutafi" danjim Abee yayi dan baisan mezaice ba, ahankali yace "dan Allah ku barta duk randa takeso saita dawo" dasauri Hadi yace "Bakasan Gwaggo bane Imrana bazata taba dawowa ba"........

Sosai Gwaggo tafashe da kuka afalo kowa na falon lallashinta yake tanuna kanta tace "ni su Hadi kema bakinciki sabida nazo gidan jikata nahuta shine harda zuwa har kofar gida amaidani gida karfi da yaji ko...." Bude kofa Abee yayi yashigo Gwaggo takallai tana sharce hawaye tace "Imrana sunki tafiya sunce saisun tafi dani ko"? Dan shiru yayi yakalli yanda Gwaggo ke kuka dakuma Lujain dake gefenta ahankali yace "eh" saikuma yawuce sama baiwani dade saman ba yafito da bandir yan 1k guda biyu a hannunshi yazo har gaban Hajiya yabata alamun tabama Gwaggo, murmushi Hajiya tayi tabama tace "Gwaggo gashi Imrana yace abaki" ganin kudade mikakku farare fes yasa duk wani kuka da Gwaggo take ya tsaya tace "wayyo Allah na dubu dari biyu, Imrana nagode nagode Allah maka albarka ubangiji Allah yakawo ciki da goyo tsakaninka da Lujain bari natafi" tamike tana tura kudin lalita duka yan dakin murmushi sukayi, tashi Lujain tayi kaman zata bita tace "Gwag......" wani kallo da Abee yamata yasa dagudu ta juya tai stairs tana kuka Gwaggo tace "aisai kiyi tunda bakida hankali ne da aurenki zan tafi dake jama'a saduwan Alheri" duk rako Gwaggo sukayi har compund ta tafi Abee kuma yakoma masallaci.

Sosai Lujain tai kuka jitayi zuciyanta yamata nauyi da zafi Kwanan nan da Gwaggo kenan gabaki daya ta manta menene bakin ciki ko fushi har damuwan Mandawari ta manta dashi amman daga tafiyan Gwaggo saitaji komi yamata duhu sosai ahaka bacci yay awon gaba da ita.

Tun wajajen 3:30 tafarka tabude idanunta hakanan kawai gabanta sai faduwa yake abin namata kaman ma zazzabi zazzabi takeji, saukowa kasa tayi ahankali tareda daura kanta akan gado hawayene yazubo mata she's soooo sad and she's hungry again, all abinda takeso shine taganta agidansu.
Bude kofa Abee yayi 4 dot yafito sai kanshi yake yau Jallabiya ce ajikinshi fara da hula akanshi kofan Lujain ya kalla saiya karasa wajen anatse yabude kofan dago kanta tayi takalleshi suka hada idanu kafinma yamata magana ta mikeda sauri tawuce bayi dan haushin shi takeji daya hanata bin Gwaggon ta jiya dan jim yayi ya tsaya kaman mai tunanin wani abu saikuma yajawo kofan yarufe yawuce yatada su Abdallah yasauka kasa yajirasu suka fice tare zuwa masallaci.

SAKON SOWhere stories live. Discover now