14

771 23 0
                                    

EPISODE 1️⃣4️⃣


Gwaggo kotakan su Baba batabi ba bangarenta takoma tana shiga tamaida kofan dakinta tarufe tasaka sakata ta ijiye kwalin sweet da goron data shigo dashi akasa sannan tawuce uwardakan tana kallon fuskan Lujain dake kwance kan gado daure dawani farin towel kanta babu dankwali idanunta sun kumbura sosai da fuskanta ma, karasawa gaban gadon Gwaggo tayi tazauna ahankali tana kallon fuskanta murya chan kasa tace "bantaba sanin kankanin abu na faruwa ba dazai kawo wani rayuwanka wanda hakan yake kaman aya agareka ne sai akanki Lulu, ninafi kowa sanin yanda kikeson wannan gantalallen dan kwallon Mandawari, yau agabana kika fasa zunzurutun asusunki kika kaima wanan kuran kudin Samira dan kawai ta aramiki waya ki kalli dan daudun mesaka hakorin makka, ni tsabagen yanda nama tsani yaron da kullum kike nunamini awaya idan yana magana zan ma iya zanashi da pencil naganshi, ranan sabida shi bokon ma bakiso zuwa ba dan kada yazo baki kalli video ba amman Allah bless yasa kikaje makarantan, jibidai yanda nida idona da muna kallon video naga bayin dakiketa nema akasa ki shiga baki ganiba domin Allah ya daukemiki idanun awajen so yake kije sama kihadu da Imrana, kikaje saman kika bangajeshi kika bata mishi kaya da fanta amman fuskanki nakan waya shaidanin nan kike kallo kika wuce bayi nafi kowa sanin yanda kike neman waje shiru ki natsu duk sanda zaki kalli Mandawari dan ko ni nan idan zaki kalla uwardaka kike shigewa ko nazo ina kwalamiki kira shiru kike ki kyaleni" shiru Gwaggo tayi sannan ahankali tace "Allah ne ya aiko miki Imrana diyata, shima kuma Allah ne ya aikamishi ke rayuwanshi saikuma Allah yakaddara cewa ba kaddara mai dadi bace zata fara hadakuba hasalima na batanci ne, na kalli fuskan yaron nan nakara kallo babu abinda nagani kan kwayan idanunshi Sal dumbin alkhairai, nasan baki sonshi shima bayi sonki, baki sanshi ba bai sanki ba amman kuma Allah yahadaku! Allahandaya hadaku shinake roka ya dawwamar daku awanan rayuwan Auren har abada Allah yasamishi sonki da kaunar ki dakuma tausayinki kema Allah yasamiki haka, koyau nafadi namutu Alhamdulillah, kullum banda zullumin daya wuce wazaki aura wazai auri Lulu na, amman kinga wannan mutumin yanada yara da sunma girma miki Dan haka ina mai kyautata zato zai iya tafiyar dake da kyau" hannu tadaga ta tottafa addu'a sannan tashafama Lujain a fuska kafin takashe wuta ta kwanta kaman jira Lujain take kankame Gwaggo tayi Gwaggo tace "ahap aini nasani duk yanda takai ga bacci inhar taji dumin mutum saita kwakumeshi" kafin kaceme Gwaggo tafara jan minshari.

Suna kaiwa gida Abee bai kula kowaba fita yayi daga motan dasauri yay flat dinsu Hajiya zata kirashi Liman yace "kul Hajiya kubarshi, kubar yaron nan shi kadai yasan meyakeji" yajuya yakalli su Ibro yace "ku kira likitanshi kuji" gyadamai kai yayi sannan Baba Liman yace "saida safen ku" godiya duka sukamai yawuce, Musty da Harun ma sukama Hajiya sallama dan tun ahanya suka sauke Abdul ya sauka a police station dinsu sukuma sauran suka shige gida.





Wuraren 2:30 wani kalan bakin yunwa ne yatadata daga bacci muryanta ya dishashe sosai sabida kuka ahankali tace "yunwaaa" firgigit Gwaggo tafarka tocula tajawo ta haska dakin yay haske sannan ta tashi zaune tana kunna wutan dakin tace "mussamman nasan yau dole kitashi da wuri dan babu abinda kikaci kikai wannan wahalallen baccin, sauko ga abincin ki nan a tray" Gwaggo tai maganan tana jawowani katon tray gaban gadon ta zauna tana bubbude mata kulolin, sannan tadau wani babban kofi tana juye mata tea dayaji madara da Milo dake tiriri akan a cup din, daidai nan ta sauko tana gyara kullin towel din kirjinta, Gwaggo tadauki cup din shayin tabata ahankali takarba takai bakinta tana karban buredin da Gwaggo kebata data yagomata kato ahannu, Gwaggo takai hannunta saman goshinta tace "kinga har jikinki yay zafi, nida har sadaka saida nayi na murnan daina zuwa asibiti yanzu kuma zaki maidamu ne" shiru tayi kawai shan shayin take da buredin da sauri da sauri tass ta shanye shayin tana mikama Gwaggo kofi tace "karamin" karasa juyemata ragowan tea tayi shima yacika cup din takai bakinta tanasha maganan su princess ne yadawo mata sabo aranta jitayi shayin da abincin gabaki daya yafita aranta, ahankali tasauke cup din daga bakinta ta ijiye akasa dasauri Gwaggo tace "menene kika ijiye shayin kuma keda ke shanye shayinki tass" ahankali takai hannunta kan katon kumatunta tabuga tagumi dasauri Gwaggo tasa hannunta tacire tagumin tace "bana gayamiki babu kyau tagumi ba" kaman jira take wani kalan rushewa da kuka tayi  sosai tanuna kanta tace "Gwaggo su princess sunce wai ni Yar iskace, ni karuwa Gwaggo ai kintuna lokacin dana fara period kince min ko hannun namiji yarike zanyi ciki ko" Gwaggo ta gyadamata kai itama kaman zatai kuka ganin yanda Lujain ke kuka bitterly, cikin mugun kuka tace "wlh Gwaggo, wlh wlh ko yatsana bai tababa, baimazo kusadani ba, Gwaggo bantaba ganinshi ba sai ranan, Gwaggo nida banda saurayi babu wanda kesona sabida ni katuwa ce inada kiba, dawane zanyi iskanci? Gwaggo ni yanzu konaga mutumin ma bansanshi ba baranma ganeshi ba, Gwaggo nayi ihu daga ganshi bisa ka na abayi sabida nasaka earpiece banmaji karan tafiyan da ba, ganinshi akaina yasa nai ihun nan ba wannan ihun wanda wanda..... wanda naji aaaa........" tawani kalan fashe da kuka sabida yanda abin kemata ciwo, hannunta Gwaggo takai zata share mata hawayen cikin kuka kaman wanda ta tuna wani abue tace "shine suke kirana fasika, karuwa da Yar iska, Gwaggo ni, ni ni Lujain ce karuwa" tanuna kanta tana wani kalan kuka mai tsuma rai dayasa Gwaggo tafara matse hawaye tana kallonta takasa lallashinta tace "Kola harda cewa wai zaiyi Iskanci dani ya siyamini shawarma guda biyar da Fanta goma sabida nine mayyan abinci dazan iya iskanci idan zaa bani abinda zanci, wlh banyi komiba Gwaggo ni danasani da banmaje excursion dinba dan dama banso zuwaba" yanda take kuka yasa Gwaggo tahau matsar kwalla tace "Allah kaimu gobe wlh wlh har ajinku zanje sainayi dambe da gantalallun yaran nan masu tallan bushahhsen gero, shegun yara wayanda ba'a haifesu ranan juma'a ba, ai gasunan sune zasusha kunya tunda Imrana ai yanzu mijinki ne" duk wani kuka da Lujain keyi tsayawa yayi ta kalli Gwaggo da rinannun idanunta tana zarosu tama kasa tambayan komi wani kalan washe baki Gwaggo tayi ganin tana kallonta tace "ai wlh kinyi goshi Lujain dakika sami miji irinshi ga kudi, ga kyau gakuma hankali jibi girman kampaninshi barima kiga" Gwaggo ta tashi da sauri tayi falo ta kwaso mata kwalin giro dana sweet din tace "kinga goro da sweet na daurin aure, jiya da daddare kina bacci aka daura gaban kawunanki da duka dangin su Imranan anan falon babanki bakiga idanun Maman su Samira ba kaman zasu fado kasa sabida bakin ciki taga Allah yabaki mai kudi daga sama ita dake cewa barama kisami mai aurenki ba balle mai kudi yanzu ai gashinan ke kinyi miji nata zankadaddun yaran dabata basu abinci suci su koshi sabida karsuyi kiba na nan agabanta" Gwaggo takara washe baki tace "dazaran kin tare da yan kwana biyu nima zan tattaro yinawa inawane nadawo gidan naku ina zan iya zama gidan talaucin nan ubanki na fama da saida atampopi akasuwa too wlh badani ba" wani kalan mugun kuka Lujain tasaki tace "Gwaggo ninace muku ina sonshi ne dazan aureshi dazu nadauka tsoratasu kawai kikayi akanme zaki auramin mutumin dabanma san kamannin shiba?  Mandawari na fa"? Wani mugun harara Gwaggo tamata tana tabe baki tace "kina ganin yanzu da wannan video naku ya zagaye yanar gizo mandawari zai yarda ya aureki idan ma ya kulankin kenan? Yau shekara nawa kina bibiyan yaron dabaimasan da zaman ki adoron kasan nan ba" cikin kuka tace "eh nidai shinake so, ai dama celebrity basa amsa messages da wuri, kinsan followers nashi nawa ne almost 400million global followers, baruwanki da ni da Mandawari, wlh wlh banason Auren nan nibaran aureshi ba" dan dariya Gwaggo tayi tace "aure kuma tuni ya dauru yarinya naki wasane, bakida hankali yanzu lamarin nan na manya ne kimana shiru kawai ki kalli ikon Allah" wani kalan kukan datake yasa taji cikinta na hantsinewa ta tashi da gudu tana kukan sai bayi Gwaggo tabita duka shayin datasha amayo dashi tayi tadasa uban kuka tun Gwaggo na lallashi ta tana bata baki harta shareta ta kwanta akan gado abinta tai bacci itama daga baya anan kasa baccin yay awon gaba da ita.

SAKON SOWhere stories live. Discover now