02
***
A chan wani ƙaton gida da ke GRA wasu manyan mutane ne guda huɗu ke zaune a wani katafaren falo daya amsa sunan falo saboda girma da kuma irin kayan alatu da aka zuba a ciki.
Ɗaya daga cikin su wanda kusan shi za a kira da babban su ya kalli wani da ke sanye da farar shadda da farin hula ya ce "Kachallah kana ganin za mu samu abunda mu ke buƙata a wajen sa?"Kachallah ya ce "inada yaƙinin haka Yallaɓai. Shi mutum ne mai biyayya"
Wani mai baƙin suit ya tari bakin Kachallah da cewa "inada shakka akan wannan"
"Mr Paul mi kake so ka ce, ba dai kana nufin za a rusa tsarin wannan gwamnatin ba..."
"Mr Paul, Alhaji Kachallah wannan ba abun ɗaga hankali ba ne. Har yanzu akwai sauran lokaci dan haka zamu cigaba da saka mishi ido kafin lokacin ya cika. Ko mi ka ce Yallaɓai?"
Yallaɓai ya kalli Mutumin da yai magana sannan ya maida dubansa ga Alhaji Kachallah da Mr Paul. A hankali ya fara shafa gemun sa yana yi yana murmushi. Murmushin Yallaɓai na da ma'anoni daban-daban amma a wannan lokaci dukkan su sun yarda cewa yana nufin su kwantar da hankalin su ne, wato akwai nasara a dukkan tsare-tsaren su.
***
LADIES HALAAL SALON & SPA waje ne da ya amsa sunan sa, domin kuwa dukkan abubuwan da ake gudanarwa a wajen suna ƙoƙarin tafiya da tsarin da bai kaucewa tsarin musulunci ba. Waje ne da Asiya-Shahida, Queen Bee da Alhaja Oyiza su ka buɗe saboda samawa mata wajen kula da jikin su. Ma'aikatan wajen dukkan su mata ne. Cikin ayyukan da su ke gudanarwa a wajen akwai wanke gashi, drying da kuma stretching, suna gyaran farce (menicure and pedicure). Ana kitso da kuma ƙunshi sannan watanni biyar da su ka wuce da su ka dawo sabon shagon su da ke anguwar GRA suka fara gyaran jiki da spa treatment a wajen (wanda ya haɗa da body, hair and foot massage, facial treatment da sauran su)
Shigowar Shahidah sashen da ake yin gyaran gashi da kitso ya sa wajen yai wani irin tsit. Precious da ke yiwa wata mata kitson wig ta tsaya da kitson tana kallon Shahida jikinta na ɓari.
Matar ta ɗan ɗago ta ce "ya ki ka tsaya?"
Tunda ba sa saida gashin wig kenan matar ce ta zo da abinta. Shahida ta faɗa a ranta.
Precious ba ta san ma Shahida na cikin shagon na su ba da ba za ta yi gigin fara yiwa matar nan kitson wig ba. Ta san dokar shagon su amma wannan matar Comissioner ce, duk da ta hannun Queen Bee ta zo ta tabbata za ta raɓi maiƙo a jikin matar, shiyasa da matar ta nuna kitson wig za a mata ba ta iya yi mata musu ba.Shahida ta ƙaraso gaban matar sannan ta kalli Precious ta ce " ina bawa mutane dama ɗaya tak a rayuwa, na ƙarshe kenan da za ki sake taka mana dokan wannan shago. Ki maida mata kuɗinta ta bar mana waje"
"Malama ban gane mi ki ke cewa ba. Da alama ba ki san ko ni wacece ba ce"
"Duk wanda ya shigo wannan waje domin a masa wani abu a nan to sunan sa customer. A dalilin an ɓata miki lokaci za a maida miki kuɗin ki dan haka ki wuce wajen da su ke yin irin wannan kitso a ƙarasa miki a chan"
"What nonsense" matar ta faɗa a fusace tana miƙewa tsaye.
"Idan kin fita ki ɗan ɗaga idon ki sama za ki ga sunan wannan waje. Saka gashin wig baya cikin services na mu"
Daga haka Asiya-Shahida ta bar wajen. Tana jin matar tana ta zage-zage amma ko ajikinta. Ta yiwa matar farin sani. Habiba sunanta a ƙasan layinsu ta taso. ta tsula bariki sosai kafin ta auri kwamishinan ilimi shekaru uku da suka wuce.
Dole ta yi magana da Queen Bee ta jawa Precious kunne tunda ita ta bata aiki. Idan irin haka ya cigaba da faruwa Salon ɗin su zai zama babu wani banbanci tsakaninsa da sauran gama gari...
YOU ARE READING
MATAR GWAMNA 1 (Best Hausa novel ever)
RomanceMatar Gwamna. Labarin Gwamna Saifuddeen Kachallah da matansa guda biyu. Bilkisu Kachallah da kuma Asiya Shahidah Faruƙ Baba.