10

62 3 0
                                    

10



Lokacin da Ale Faruƙ ya auri Zainab Kurma matan sa uku ne, dan bai jima da sakin ta huɗun ba. Da ganinta da auren duka-duka sati huɗu ne.

Mama Asabe har ga Allah bata so aka yi auren ba, ba kuwa saboda halin Ale Faruƙ ɗin bane na auri saki sai dan saboda ayyukan da Kurma ke mata. Duk wani ƙarfin sana'arta to Kurma ce.
Ita da Malam Sabo dai sun yi ƙarfa-ƙarfa sun mata gado da tabarma da buta daga nan kuma kowa ya tsuke Aljihun sa. Duk da kuwa irin kuɗin da Malam Sabon ya yaga a wajen Ale Faruƙ ɗin.

Inna Talatu wacce ta reneta lokacin tana yarinya da kuma wasu cikin 'yan uwan mamanta su suka haɗu suka mata sauran kayan ɗakin.

Lokacin da aka kawo Kurma gidan ɗakin Iyani aka fara kaita wacce ta ke Uwargida sannan aka wuce da ita ɗakin Fulani wacce ta ke matarsa ta biyu a gidan, matar da ta zame masa ƙarfen ƙafa ita bata haihu ba amma ta ƙi tafiya duk da kuwa rashin mutuncin da take shukawa a gidan. Sai ɗakin Halime matarsa ta uku wacce shekaransu uku kenan da aure.

Lokacin da aka kaita ɗakin Tabawa ko kallon kirki bata yi musu ba, ta ɓantari goro tana taunawa tace "Faruƙu kenan. Abin nasa yanzu ya koma kan Miskinai. Allah rufa asiri"
Inna Talatu ta harzuƙa zatayi masifa wata yayarta ta hanata. Kafin su fita kuwa Inna Talatun ta kirata da tsohuwar banza. Tabawa ta biyosu tana zagi tana tsinuwa amma babu wanda ya kulata.

Rayuwar Zainab a gidan Ale Faruƙ tamkar 'yar aiki ce a gidan iyayen gidanta. Sati ɗaya da Ale Faruƙ yai yana kwasar amarci ya dinga tattalin Zainab, shi yake siyo mata abinci daga waje: nama, bredi, ƙwai da madara sune cimarta. Baiwar Allah har ta fara sake jiki tana godewa Allah tunda rayuwar da take ciki yanzu akwai daɗi ba kamar gidan Mama Asabe ba.
Lokacin da aka fara rabon girki nan ne ta ƙwammaci kiɗa da karatu. Gidan Ale Faruƙ babban gidane wadatacce dan kowacce mata ciki da falo gareta, shima sashensa ciki da falo ne, sai ɗakuna huɗu na yara sai ɗakin mahaifiyarsa Tabawa, sannan akwai ɗakuna uku a zaure na saukan baƙi. A lokacin daya auri Zainab 'ya'yansa goma shabiyar ciki kuwa bakwai ne da iyayensu. 'Ya'yan Iyani su guda shida, maza biyu,mata huɗu sai Halime dake da 'ya ɗaya.

Da farko Fulani ce ta fara ɗaurawa Zainabu nauyin girkinta daga baya Iyani da Halime suka biyo baya. Kafin kace me gaba ɗaya ranakun girkinsu ita ke yi. Fulani kam hatta Sana'arta na shinkafa da wake da take da rana sai da ya zamo Zainabu ce ke yin komai , ita dai sai kawai idan ta gama ta zauna ta dinga siyarwa.
A hankali Yaran gidan da suka ga iyayensu na saka Zainab aiki sai suka fara taɓawa suma. Lokaci lokaci sai su bar mata wanke-wanken gidan ko kuma  su jiƙa kayan wanki su ƙi wankewa saboda idan Kurma ta zo ta gani tana son amfani da baho ko bokiti dole sai dai ta wanke musu kayan tunda bata da mugun zuciyar da zata bar musu kayan a ƙasa. Ranan da ta fara zuwa ta ga sunyi haka, ɗakin yaran ta je tana musu bayani akan za tayi amfani da bahon wanki. Haka suka manna mata hauka akan basu san mi take faɗa ba, abin takaicin yawanci bahon nata ne dan Fulani da Halime basa taɓa barin nasu a waje. Ita kuwa Kurma ko bata fito da su ba yaran sukan shiga ɗakinta su ɗauka babu yadda ta iya.

Cikin zalunci da ake yiwa Zainabu ba abar Tabawa a baya ba. Itama ba ta taɓa ragawa Zainabun ba, dama duk cikin matan Ale Faruƙ babu wanda ta ɗauki mahaifiyarsa da daraja haka ma jikokinta. Kafin zuwan Zainabu gidan Tabawa ke wanki da kanta, haka ma abinci sai abinda aka zuba mata amma Zainabu Kurma bata taɓa mata rowan abinci ba haka nan wankinta da gyaran ɗaki duk ita ke yi.

Kafin shekara ɗaya  Zainab ta zabge ta koɗe. Aikin da take a gidan Ale ko rabinsa bata taɓa yi ba a gidan Mama Asabe.
Ale Faruƙ ya san mi yake faruwa a gidan tunda shi ba makaho bane amma halinsa dama shine idan mace ta shigo gidansa komai ta tarar ruwanta ne, sai dai ta ƙwaci kanta daga sharrin sauran matansa amma shi ba zai tanka ba.

Akwai lokacin da Zainab tayi ɓarin cikin sati uku bata sani ba bata ma san cikine ba dan jinin  al'ada ta ɗauka.
Tana zaune ne a gidan amma gaba ɗaya komai na gidan ya fita mata aka. Akwai lokutan da take tunanin gara kawai Ale Faruƙ ya saketa. Sai dai dokar sa ce baya sakin mace kafin ta cika shekara biyu. A cewarsa lokacin bai gama morar kuɗinsa ba.

MATAR GWAMNA 1 (Best Hausa novel ever)Where stories live. Discover now