FARKO

41 2 1
                                    

Mafari, FARKON komai!

Assalamu alaykum!
Wannan zai wanke maku fushin "MARAICINA" da kuke Insha Allah

********

KURFI,KATSINA STATE, NIGERIA 1999.

Durƙushe take gaban wuta tana hurata da baki, lokaci zuwa lokaci take ɗaga kanta ta kalli tagwayen jariran dake shinfiɗe can kofar ɗaki nesa kaɗan da ita, yaran da sukayi kutse cikin rayuwarsu tare da wargaza Farin cikinsu. Yaran da KADDARAR Su ta kasance mai girma, har Allah ya bata nasarar kamawar wutar.

Ware murya tayi da ɗan karfi tana fadin

"Safi...."

"Safiyya....."

"Safiyyatu....."

Ta jera kiran sunayen ukku a tare, shiru taji ba ansa
Kara bude murya tayi da fadin

"Hooo safi wai kina ina ne,wannan Ƴa da kulaficin daki kike"

"Ayya...ganinan fa ina ansawa"
Wata siririyar murya datafi kama da ta yaran da lafiyar jiki bata gama wadata ba ta amsa tana fitowa daga dakin.

Dagowa Ayyar tayi jin muryarta a kusa.

Kallon yanda iskar daminar ke barazanar kadeta
take kafin wani kayataccen murmushi wanda karfinshi bai hana ganin tsantsar tausayin safin dake cikin idonta b aya bayyana.

Sai da ta tsaya ta gyara yaran dake kwance sannan ta karaso da kai a duƙe.

"Gani ayya" ta fada.

" fansoman saƙon kudin adashen nan a wurin tabawa"inji Ayyar da tun kafin ta ƙarasa take ganin Safin na mata kallon "dan Allah karki aikeni" da ta saba duk lokacin da Ayyar zata aiketa.

Sau dayawa idan Ayyar taga haka haƙura take da aiken har sai Allah ya kawo mata wanda zata aikan

Amma yanzu kam ta daina insha Allahu kamar yanda tayima kanta alƙawari safiyar yau.

Ganin Ayyar batako mata kallon kirki ba yasata bude Baki tace

"Dan Allah Ayya.........."

Bata karasa ba ta katse ta da faɗin

"me kike jira? da yanzu kinyi nisa"tana mayar da kanta wurin wutar

Jan ƙafa tayi a hankali .

da "to Ayya" ta ansa tana komawa ciki domin sako hijabin ta.

**********

FIKA,YOBE STATE, NIGERIA 1999.

Gari yayi tsit! Kasancewar dare ne, dare mai tsananin duhu irin na damuna,bakajin komai sai kukan tsintsaye da ƙaran hadarin dake hararramin tasowa.

Durkushe yarinyar macen da baza ta shige ma shekaru 16 take cikin wani ɗaki mai tsananin duhu, ɗakin da sai kayi tsai zaka iya hango abun da ke ciki ta cikin disasshen hasken fitilar kwan dake ciki.

Murƙusu take tare da wani irin gurnani na ban mamaki haɗe da keta uwar zufar da daga kallo ɗaya zakasan ta azaba ce!

Tsohon ciki ne jikinta da yayi tsini sosai wanda hakan ya nuna NAƘUDA take.

Dattijuwar mace ce ke riƙe da mafici tana fifita mata haɗi da yi mata sannu lokaci zuwa lokaci.

Gefen hannun hagun ta kuwa wata tsohuwar mata ce take kunce wata baƙar leda ga kuma kaskon garwashi da ya gama ruruwa yayi jajir a gabanta!

Ledar ta gama kuncewa ta ɗebo  barkono kusan shidda ta watsa man garwashin inda cikin lokaci ƙalilan dakin ya gauraye da hayaƙi mai haɗe da zafin barkonan, ba shiri suka fara zabga tari ɗaya bayan ɗaya ba ƙaƙƙautawa.

Haka sukayi ta tarin har hayaƙin ya wuce amma sam Rabi bata sauka ba.

Ungozomar ta sake ɗauko wata zabgegiyar muciya irin ta abincin gayya ta kama bakin saada ta zungura ciki

Ba shiri ta fara kakarin amai da ƙarfi amma sam matar nan bata kyale ta ba.

Haka Rabi tayi tashan wahalhalu iri iri har kiran sallar Assalatu wanda ya taho mata da wani sabon azababben ciwo data ga kamar kwanaki biyun data ɗauka tana naƙudar wasa ne.

Ji tayi kamar bayanta zai ɓalle saboda tsabar azaba, ba shiri ta damƙo ƙafar matar dake kusa da ita wacce ta kasance surikar ta.

Wani dogon nishi ta sauke wanda yayi daidai da fitowar Kan yaron, ungozomar tayi saurin taimakwa ta fiddo jaririya MACE.

Numfashi saada keta saukewa daga gani ba karamin jigata tayi ba.

cikin muntuna ƙalilan aka gyare wurin da mai jegon tsaf tare da jaririyar dake ta tsanyara kuka.

Kukan da ya sanar da maƙota  bakin duniya sun iso.

*******

AGUIÈ, MARADI  ÉTAT NIGER.

zaune take kan kujera ƴar tsugunni tana fere kabewa tare da rera ƴar wakarta ta Nishaɗi.

daga kallo daya zakasan cikin nishaɗi take ainun.

Sallamar yaro taji ta ɗago kai tana amsawa

"wai anche Saada taje inji oumarou"Yaron ya fada

lokaci daya faraar dake fuskarta ta dauke kamar bata taɓa faraa a rayuwar ta ba.

Ganin baa amsaba yaron ya ƙara sauti yana maimaita saƙon wanda kafin ya dire ta katse shi da faɗin

"kaje kache batta nan sai ƙaunarta ka taddo" ta fada

Ansawa yaron yayi yana ficewa a guje.

********

Zaune suke a majalissa suna hira, gefe kadan butar shayi ce irin shayin buzaye da sukema ganyen laƙabi da "Taibuz" da ƙananan kofuna na tangaran.

Ga kuma shisha pot da kwalayen sigari suma a wani ɗan faranti na silver.

"amadou kana ji mun ƙaunar ka wai ni ke zuwa gareta tana cewa ace baa taddo ta ga gida ba'?" Oumaru ya fada.

"wacce ƙaunar tashi? Hala saada?" cewar wani can gefe dasu

"itta hwa frére (ɗan uwa)" ya ansa mishi

"sau da dama nasha hwaɗi makka frére ka rabbu da itta ka je ma wassu mataye can daban, batta da mutumci ko kaɗan yarinyar ga" amadoun ya bashi ansa.

"hmmmm ka rabbu da itta in ta san watta ai bata san watta ba" inji oumaroun

Dariya suka sheƙe da ita sosai dukansu.

wani saurayi ne ya karaso da leda hannunshi yana bin su da kallon"dariyar me kuke" kafin ya zauna yana jawo wani madaidaicin faranti na silver ya juye kayan ciki a ciki

goro,Gâteau (cake) ne ciki mai dan yawa da bonbon (sweets) a wata ƙaramar  leda a ciki.

"yan ouwa, wannan shi ag goron saka amre na, dix-août (10-August) in Allah Ya amince"

Ihu suka saka gaba daya suna zagaye shi da rawa.

******

Ya kikaji tafiyar tamu?
Kamar Kullun dai akwai gargada a hanyar!
Don't judge yet Amma😃
Ina jiran raayoyin ku

Next update on Sunday Insha Allah

#Boddozee
#Bahaushiya

BAHAUSHIYA.Where stories live. Discover now