page 8

190 15 2
                                        

*SAI NAGA BAYANKI*

              *NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*PAGE 8*
                   
Alhaji wada

        Wani irin zufa ne ya ringa keto masa duk da  a cikin Ac yake,ya cigaba da Kiran Kishatu a waya sai dai wayarta a kashe yake,Taya zaije ya saki Rasheeqa ma ya Auri kishatu,Yana san kishatu sosai dan daga yadda yake kishinta yasan Yana balain Santa,har ga Allah da ba kanwar Rasheeqa bace zai iya aurenta sai dai dangantakar dake tsakanin su yasa bazai Yu ya aureta ba,bai kuma taba kawowa zai rabu da ita ba,yanzu kuma abinda ya daga masa hankali cikinsa da tace tana d'auke da shi,yasan zata iya daukar ciki,dan baya amfani da roba idan zai sadu da ita,kuma karshen tarayyarsu a ranar tayi wanka wanda dakyar ya daure da take jini,a waje yake kawowa Amma a ranar a ciki yayi,wanan wane irin kwamacala ne kanwar Rasheeqa kuma d'auke da cikinsa mai yasa kishatu take so ta tona masa asiri Mai yasa kishatu take so ta tozarta shi,taya zai saki Rasheeqa da yake ji bazai iya rayuwa batare da ita ba,ya cigaba da Kiran Kishatu a waya so yake yaji a inda take saboda ya samu ya shawo kanta dan ya lura idonta ya rufe ta kasa gane abin kunyar da take so ta aikata,haka ya rike wayarsa yayi ta gwada wayarta a kashe,jiki ba kwari ya d'auki hanyar gida Yana ji kamar ya fadi saboda tashin hankali itama Rasheeqa baisan Mai yasa ta dage sai ta kori kishatu ba,da yasani yayi fuska ya nuna mata bai dace ta kori kishatu ba,gashi yanzu ta b'allo masa ruwa,da wane ido zai Kalli Rasheeqa idan ta gano Yana soyayya da kishatu haka yayi ta sake sake ya dauki hanyar gida baya so yayi laifi da yawa a wajen Rasheeqa dan ko kadan baya San bacin ranta da bazama zai yi wajen neman kishatun,amma yanzu idan yaje zai fito nemanta kila tana wajen da suke zuwa shakatawa.

Rasheeqa

            Bansan Mai kishatu take takama dashi har ta iya kallon cikin idona tamin rashin kunya sai a yanzu na fara nadama da barin ta da nayi tazo min gida ta zauna,a yau ta fito min da halinta  da ban taba Sanin ta dashi ba,dan biyayya take min sosai tana girmamani na d'auka data ga kayanta a kasa,zubewa zata yi a gabana tayi ta magiya watakila na janye korar da nayi niyyar mata tunda nima Ina morarta yau aikin da bata min ba yasa min Jin haushinta har na yanke korarta na ja dogon tsaki wai kanwata da muke uwa daya fada muke da ita tana burin ganin bayana,yayata da muke uwa daya uba daya itama so take ta ga bayana, dole ma na mike tsaye duk da ni bansan ta inda zan fara ba,ba wani hulda nake da kawaye ba a lokacin da nima na dawo garin nan Aunty Ama bata barina nayi kawaye,tafiso duk abinda zanyi na fada mata hakan yasa nima sai na Saba da rashin kawayen,bansan yadda ake bin bokaye ko mallamai ba,amma zama bai kamani ba tunda yan uwana sun zama makiyana dole na nemi tsari daga sharrinsu amma kafin na samu mafita ko ciwon Kai nayi  daga Aunty Ama har kishatun wallahi kulle su zanyi tunda sun Sha alwashin ganin bayana nasan Aunty Ama muguwa ce ta karshe,idan har zata iya kashe mutum dan ta tsaya tsayin daka dan taga bayana bazan mamaki ba,haka nayita sake sake ganin lokaci na tafiya yasa na tattara tunanin da nake na watsar.

Na fada kitchen duk da bana san aiki haka na zage na dora abincin dan yau nice da girki duk da haushin Alhajin nake ji amma bana wasa da duk wani abu  daya shafe shi, Ina San daukar Yan aiki Ina tsoro azo ayimin kwacen Alhaji,Amma yanzu dole na nemi tsohuwa duk da suma tsofaffin idan suka tashi tsiya zuwa suke da jikokinsu daga nan labari sai ya canza,yanzu da na daidaita Alhaji da mmn mujaheed dole na Kara zagewa wajen karkato da hankalinsa kaina,kowa ya iya allonsa ya wanke kawai.

Sai wajen shidda na fito daga kitchen na jera abincin akan dining na fada bandaki,sai da nayi wanka na Fito na daura alwala Ina iddar da Sallah na zauna a gaban mudubi na ci kwalliya da kananan kaya yau so nake na koma yarinya sharaf,hakane yasa nayi shigar riga da wando na tsaya a gaban mudubi Ina kallon cikina yadda yayi flat ba mai yarda nayi tumbi a baya kamar wacce zata haihu nono na ma kamar ban shayar ba dan ko brezia ban Saka ba, dole na karo magungunan Aunty zeem dan naji dadin amfani dasu sosai

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 12, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SAI NAGA BAYAN KIWhere stories live. Discover now