*SAI NAGA BAYANKI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*PAGE 6*
Alhaji dafe kumatunsa yayi Yana kallona yana "Akan na Saki Hafsa kika mareni"?
"Eee Alhaji na mareka ne dan ka dawo hayyacinka dan naga baka cikin hayyacinka,a gaban idonka yanzu tace ta barni da Allah,akan me zaka jawo min bakin jini,akan me zaka saka a ringa min kallon muguwa,Ina da kishi amma banida zuciyar mugunta da har zan so sila ta ka rabu da uwar yayanka mai yasa sai da na sako ka a gaba dan na shiryaku a lokacin zaka saketa a gabana,Alhaji wallahi ka Maida ta dakinta idan ba haka ba nima ka sakeni"
Duk da duk cika baki nake dan mutuwa nake fata ta Rabani da shi
"dalla ki rufewa mutane baki dama ai abinda kike so kenan kizo ki samu mata da mijinta da yaransu saboda rashin tsoron Allah ki shiga ki rabasu,kizo kina yiwa mutane wani munafirci indai wada ne gaki gashi wallahi sai ya Saka miki hawan jini kamar yadda ya sakawa Hafsa kuma idan Ina rayye Hafsa wallahi bazata taba tagayyara ba ni zan tsaya mata ita da yaranta"
Cewar wanan abokin nasa da na lura ya mugun tsanata maganarsa har ga Allah ya Kona min rai Ina shirin magana Alhaji ya dakatar dani Yana "Musa ka fita a harkar iyalina kasan irin maganar da zai fito a bakinka dan wacce kake gayawa maganar wallahi saboda ita na taka nazo gidanan,Ashe asirinka ne zai tonu dan bana zuwa shi yasa kake zagayowa wajen Hafsa kake mayye mata gurbina ka bararraje kamar gidanka na dade Ina zargin San Hafsa kake tun kafin ma na aureta toh idan burinka kaga na saketa ka aureta har kana kirarin bazata tagayyara ba na Maida auren daga yau karka sake taka kafarka kazo gidanan idan kuwa na sake ganin ka wallahi sai na daure ka munyi sharia dakai"
Ido Alhaji Musa kawai ya zubawa Alhaji wada dake magana cikin hucci har ga Allah yaji dadin Maida Hafsa da yayi dakinta dan Yana ta tunanin ya Hafsa za tayi da Yara bai kuma San irin taimakon da zai bata batare da an zarge shi kamar yadda Alhaji wada ke zarginsa ba a yanzu,
Fitowar Hafsa daga daki da katon akwati tana ja ya sa suka maida hankalinsu wajen kallonta.
Alhaji wada cikin hade rai Yana Jin kamar ana Kona shi da ganin Hafsa da yake shi Kansa bai tab'a tunanin zai iya sakin Hafsa ba tsabar kishin da ya rufe masa ido yasa ya furta kalmar daya ke Jin dacinta a bakinsa ko da Rasheeqa bata ce ya mai da ta ba bazai taba yarda ta fice daga gidan batare da ya maida ta ba, ya fara magana yana "Ki koma dakinki na Maida ki dan kema naga Allah Allah kike na sake ki ki komawa Musa"
Bata ko Kalli Alhaji ba ta cigaba da jan akwatinta har tazo zata wuce ni na kira sunan ta da "Hafsa ban tab'a Sanin irin zaman da kike yi da Alhaji ba sai a yau da Wanan abokin nasa yace kije Allah shine shaidata bani da masaniyar abinda ke faruwa ba kuma nida hannu a abinda ya shiga tsakanin ku,ban Miki dole akan ki yarda dani ba,ba abinda ya shafeni da rayuwarki da Alhaji Auroni yayi kamar yadda ya Auroki yadda bana fatan na rabu dashi kema bana Miki fatan ki rabu dashi banzo dan na wargaza tsakaninku ba sai dan nayi gyara dan haka ki sa a ranki ni ba makiyar ki bace abokiyar zamanki ce ko nace kishiyarki Babu sharri a zuciyata daga haka na wuceta dan duk maganar da nake bata juyo ta kalleni ba,Ina jin muryar Alhaji na cewa abokinsa yazo ya fice masa daga gida,kar ya sake ganinsa a gidan,naji abokin nasa na cewa Hafsa
"Kiyi hakuri ki zauna Hafsa tunda ya maida ki ki cigaba da hakuri ki barwa Allah komai,idan Wada a hayyacinsa yake wulakantaki kawai yake so yayi Allah zai miki sakayya da gaggawa idan kuma wanan matar juyar masa da Kai tayi tazo tana munafirci dan ta burge shi ace ita ta gari ce Allah ya tona mata asiri da gaggawa Kai kuma wada wallahi kaji tsoron Allah Idan Babu duniya akwai lahira Hafsa ba matar da ya dace ka wulakanta bace matar da ta zauna da Kai tun kafin kasan zaka kawo wanan matsayin itace yau Abar wulakantawar Ka da yaran da ta haifa maka da suke tunanin Saboda kana da wasu yaran ne ka juya musu baya,kuma kasani da zuciya daya nake taimakon Hafsa saboda irin zaman da muka yi da margayi ba wai dan wata manufa da Kai kake tunani ba,Hafsa na tafi kiyi hakuri komai zai wuce"

YOU ARE READING
SAI NAGA BAYAN KI
Não Ficçãolabarin Sai naga bayanki labarine Mai taba zuciya da tausayi daya kunshi cin Amana