*SAI NA GA BAYANKI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*
*PAGE 3*
Bai bani amsa ba ya ja motar muka cigaba da tafiya ni kuwa jikina yabi yayi sanyi kalau,ko makaton mu bana Jin Alhaji zai bari su Sha wahala haka,ko yaron daya dauki yarinya nan ina ganinsa a hanya nasan jinin Alhaji ne yaran sa ya bari suke yawo a Rana har da Yar shekara biyar ko shidda,Alhaji bazai iya lissafa motocinsa ba daidai da Imrana motoci biyu ya siya da sunansa suna nan a ajiye,ni kuwa motocina uku manya ya siya min,ya za'ayi har ya kasa barwa matarsa mota daya a ringa jigilar Kai yaran makaranta,mai yasa naji yarinyar na Umma bata da kudine shi yasa bata basu kudin mota ba,nasan Alhaji Yana fiffitani akan matarsa Wanda ni na d'auki hakan a tsabar san da yake min ne,dan kamar ma bani da kishiyar haka nake jina tunda ran girkin ta ne baya kwana a wajena amma cin abinci komai har ma mu farantawa juna ma anan yake yi Koda ran kwanan ta ne,a kishi dai namu na mata yasa ban wani damu ba ni dai tunda na fita matsayi a wajensa shikenan,tunda muka yi Aure sau daya na tab'a ganin matarsa lokacin Ina amarya Alhaji ko gate baya fita sallah ma a gida yake mun tafi wata biyu a haka kafin watarana naga mai gadi na hayaniyar bazai bar wata ta shigo ba na fita lokacin da kaina a jike dan fitowa na daga wanka kenan Alhaji kuwa bacci ya d'auke shi aikin kenan dan baya daga min kafa indai gyaran jiki ne ba'a barni a baya ba zan iya kashe daruruwa Wanda duk training din Aunty Ama ne, daga ni sai wani doguwar riga kamar shimi nace Mai gadi ya bar ta ta shigo na ga wacce haka ta dage tana neman Alhaji,sai kuwa gata ta shigo kyakyawa ce zata iya girme min da shekara uku haka bak'a ce ba wuluk ba kana ganin ta kasan itama ba baya bace wajen kyau sanye take da doguwar riga ba dai tayi shigar daukar ido ba,ni kuwa na yamutsa fuska Ina tambayarta daga Ina,sai tace min ba waje na ta zo ba wajen Alhaji tazo na ma sa magana, wani kallon sama da kasa na mata Ina ita a su wa,sai ta saki murmurshi tana "Dadin abun idan Babu duniya akwai lahira duk abinda ka shuka zaka girbe shi,bulalan da kika zanne ni dashi watarana kema bulalan na iya Zane ki rayuwa ce karki damu ni Hafsatu da na cutar dake gwara ke ki cutar dani"
A lokacin Ina ganiyar kishi haka ne yasa na gano itace matar Alhaji ce na kama kugu na hau zazagin ta, nace mata banza ballagaza ayi mace kamar namiji ai ni Alhaji ma ni ya cuta daya hadani kishi da ita har na gama ci mata mutunci bata kalleni ba illa ma girgiza kanta da tayi ta fita waje,a lokacin ko kadan bana so wata macen ma ta kalleshi dan kafin ya aureni ma da zai saki matar tasa Dadi zanji,Ashe ma gwara da nayi blocking din lambarta a wayar Alhaji dan Aunty Ama ce duk ta bani shawarar yin hakan ta tusa min kiyayyar kishiyata Wanda sai daga baya ma na cireta a raina da naga so iya so mijina na min kuma ba Abinda zata gaya min balle ta hada kanta dani,dan a wajen Aunty Ama nake Jin labarin yadda Alhaji ke balain san yaga mace fara Allah bai kaddara zai Kara aure ba sai a kaina.
Har ga Allah da na kwana biyu banji a raina zan cutar da matarsa ba nidai idan zai fiffitani akanta ya nuna min bata Kai ba ya gama min komai,sai dai ban kawo fifiikon har ya Kai haka ba,ban kawo zai iya bari yayansa su tafi makaranta a kafa har su dawo a kafa ba bayan nasan Yana da motocin da ko shi bai Kai su ba driver zai iya Kai su,Yana nufin matarsa ma bata da mota kenan da ita zata dauko su har ana Umma bata da kudi.
Parking din da muka yi a katafaren restaurant din da sai wayanda su ka jiku da kudi kawai ke iya zuwa ya katse min tunanin da nake.
Alhaji ya Bud'e motar ya fita bayan ya sauke Abul da Abla,Imrana kuma ya bude ya fita dan Yana da tsayi da girman jiki Jin Dadi yasa kana ganinsa zaka dauka yayi shekara goma ga kiba.
Wajene na manyan mutane irin rayuwar dake balain burgeni,Alhaji ke shimfida min,Koda muka shiga wajen vip muka yi da ba kowa muka zabi abinda muke so aka yi serving din mu, hirar da Alhaji ya fara min na shagon da yake tunanin Bude min ya d'auke min hankali daga sake masa tambayar dake cina a rai, na fara murna dan yace zai Bude min shagon kayan Yara za'a na kawo min kayan daga waje,sosai na tsinci kaina a farinciki duk da ba wai shine karo na farko da zai Bude min ba Ina da shaguna biyu da ya bude min na kayan kwalliya da saloon.

YOU ARE READING
SAI NAGA BAYAN KI
No Ficciónlabarin Sai naga bayanki labarine Mai taba zuciya da tausayi daya kunshi cin Amana