*SAI NAGA BAYAN KI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*PAGE 2*
Ban kalleta ba na tsaya da kyau dan bazan Kara bari ta cigaba da juya ni ba
Ta tako cikin palon ta tsaya a gabana jikinta na wani irin rawa da jajjayen idanun ta ta fara magana cikin kaushin murya tana "Rasheeqa nice yau kike wa rashin kunya har kina na barki ki samu nutsuwa a gidan mijinki ni Amabuwa kike fadawa magana"?
Jarumtaka na aro na juyo na kalli cikin idanunta dan idan ban kawo karshen wanan juya nin da take ba zan wayi gari ba ni da komai na fara magana Ina "Ba rashin kunya nake miki ba Aunty Ama gajiya nayi da yadda ki ka sa kani a gaba ki ka mai dani bankin ki,bayan kinsan ni ba aiki nake ba,duk kudin da na ke baki daga wajen Alhaji nake karba kudi kuma ba kanannu ba yau da gobe dole na gaji Aunty,tun Alhaji na bani kudi watarana dole shi ma yaga na ishe shi da karbar kudi,shekara shidda ba'a wata baki amshi kudi a hannuna ba ni kaina baki barni na samu ko dan kudin na tara ba kinci iya rabon ki ki barni nima naci rabona Aunty shine kawai ba batun rashin kunya"
Ja da baya tayi dama idan ranta ya b'aci jikinta rawa yake ta kasa tsayawa ni kuwa na koma na zauna ta hau zagaye palon sai da ta gaji ta tsaya a gabana tana "Ni zaki yiwa butulci Rasheeqa Yau bani na zama silar da kika taka wanan matsayin ba?bani na nemo miki Alhajin kika aura ba?
"Ko baki Nemo min shi na Aura ba mijina ne kuma ai ban roke ki ki nemo min mijin Aure ba,kuma ai baki fada min kina da manufar daya Saka kika jajirce wajen tsayawa na auri Alhaji ba Aunty Ama kefa yayata ce ba haifata kika yi ba da zaki ce lailai sai na Miki biyayya kin tsara min yadda zanyi da rayuwata,idan ma taimakon da kike ganin kinyi min zan biya ki ai na dade da biyan ki daga aurena da Alhaji zuwa yanzu ke kan ki ba za ki iya lissafa kudin da na ba ki ba,ko ta silarki ko bata silarki ba Allah yayi Alhaji mijina ne tunda gamu da Yara uku Abu kadan sai ki hau yimin gori toh a gaskiya na gaji ki barni na sha iska sisi bazan Kara badawa ba,mijina ba a kasa yake tsinko kudin ko bai San zafin kudinsa ba da zaki ringa saka ni karbar kudi Ina baki ,har kyautar gida da mota ya miki ni na baki kudi bazan iya lissafa wa ba idan ma kadara zaki yi ta siya kudaden da nayi ta ba ki ya isa ya siya Miki kaddara da yawa na gaji bazan Kara bada ko biyar dina ba"
Nace Ina hucci
Aunty Ama da na kasheta da mamaki taja baya ta fara tafi tana "Ba shaka Rasheeqa wuyan ki ya isa yanka dole ki fada min maganganu kin manta ba dan na dauko ki a kauye ba da kina can kina haifar yayan shegu kina bin Yan talla suna dirka miki ciki,kin manta da yadda na dauko ki na kawo na raine ki na tsaya tsayin daka ko Yar dana haifa a cikina ban mata abinda na miki ba,saboda ki kawo matsayin nan ni nasan kudin da na kashe da wahalar da na sha akan ki kin manta kalar rufin asirin da na miki,saboda ke na shiga daji sai da na samu kwana uku nayi kazamar rayuwar da ko makiyina bana masa fatan yayi,na shiga na fita kika kawo matsayin nan sakayyar da zaki min shine ki butulce min,kimin rashin kunya akan kudaden dana san basu taka karya sun karya ba kike wulakanta ni,kudin da ba'a Aljihunki zai fito ba a Aljihun mijinki zai fito Wanda ni nasan kamar naira goma yake a wajensa shine zaki wulakantani Rasheeqa"?
A fusace na fara magana Ina "Na gaji Aunty Ama da anyi abu kadan sai ki hau yimin gori naga ni da ace nasan badan Allah duk kika min abinda kika min ba wallahi bazan yarda ma ki dauko ni daga can ba daidai da allura da kika siya min kimin gori kin siya min,idan ma biyanki kike so nayi a cikin shekara shidda ai na biyaki har da riba wallahi dan haka Dan Allah ki rabu dani tunda ba haifata kika yi ba kije ki samu kubura ki cigaba da juyata ni dai kam wallahi sisi bazan Kara badawa ba kinci rabonki haka Ina dalili zaki matsamin da takura da gori,kuma ko baki nemo Alhaji ya aureni ba kema Kinsan zan samu Mai kudi da zai Aureni"

YOU ARE READING
SAI NAGA BAYAN KI
Não Ficçãolabarin Sai naga bayanki labarine Mai taba zuciya da tausayi daya kunshi cin Amana