BABI NA ƊAYA

68 4 0
                                    

*𝐎𝐧𝐞 𝐝𝐚𝐲 𝐲𝐨𝐮'𝐥𝐥 𝐭𝐞𝐥𝐥 𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐲 𝐨𝐟 𝐡𝐨𝐰 𝐲𝐨𝐮'𝐫𝐞 𝐨𝐯𝐞𝐫𝐜𝐨𝐦𝐞 𝐰𝐡𝐚𝐭 𝐲𝐨𝐮'𝐫𝐞 𝐠𝐨𝐢𝐧𝐠 𝐭𝐡𝐫𝐨𝐮𝐠𝐡 𝐧𝐨𝐰, 𝐚𝐧𝐝 𝐢𝐭 𝐰𝐢𝐥𝐥 𝐜𝐨𝐦𝐞 𝐩𝐚𝐫𝐭 𝐨𝐟 𝐬𝐨𝐦𝐞𝐨𝐧𝐞 𝐞𝐥𝐬𝐞'𝐬 𝐬𝐮𝐫𝐯𝐢𝐯𝐚𝐥 𝐠𝐮𝐢𝐝𝐞.

 
BABI NA ƊAYA

               *************


"Ba abin da kake ji yana tashi a cikin babban gidan sai haya niya , da ihu na mata da yara kamar ana ɗanbe.

"Wata mata ce naji ta na cewa cikin yanayi na rashin mun ci da faɗa, dan tana magana har miyau na fita a bakin ta dan Masifa tana cewa

"Wallahi an dai ji kun ya , in har da gaske ne kun aurar da yar taku Bama gan ta a zaune a gida ba.

Yarinya ta je tayi cikin shege kun guyi da bayan ta har kuna cewa tayi aure, to in tayi ina mijin.

Kai Ni duk wannan be dame niba har dai za ku fita a sabgar ɗana, haka kawai ɗan nawa guda kamar rai ina zaune lafiya baza a zo a shafa wa ɗa na masi fa ba.

Wata ta amshe zan cen da ɗangin tsiya dangin matsafa ba, dangi da suka gaji abin kunya, ai wallahi yaya sai kin tashi tsaye ko kina gani a goga miki tsiya .

Ina dur ƙushe a ƙasa ina kuka ga tsohon cikin da ke jiki na amma hakan bai hana matar ƙanin mahaifi na zagi na da aiba ta abin da ke ciki Naba wan da bai zo duniya Bama ,

Kuma duk wannan faɗan da take yi ban mata komai ba amma har da ƴan taye ta samu, basu ji tau sayin halin da nake ciki ba haka suka haɗu suka min duka .

Ba tare da wani ya zo ya ce ce Ni ba, abin haushin ma mahaifiya ta tana cikin gidan amma ko leƙo wa bata yiba .

Ko kadan ba kuka nake akan dukab da aka min ba, kuka nake akan ƙaddara ta , ta baya da wacce nake fuskan ta da kuma ta nan gaba da zata zo min.

Ina jin tsoron abin da zai faru in ƴata ko ɗana suka zo duniya,

A haka ma shaƙar iska mai daɗi acikin gidan mu , bana iya wa, to ya abin da zan haifa zai rayu acikin gidan nan, Ni da kai na tau sayin kaina nake ji.

Haka yan gidan mu manya da yaran da na girma ma suka gama zagina da cin mutumci kafin kowa ya watse,

Kamar ba ai ruwan su a gurin ba.

Abin da ke faruwa kenan duk ranar da wani ya gwada temako na a cikin gidan mu, nida gidan mu, amma bare a cikin sa yafi Ni ɗara ja.

Dadda fawa nayi na ta shi da kyar , na shiga cikin ɗakin mu jiki na duk yayi min tsami, a saman sallaya na samu mama tana jan car bi .

Bina da kallo kawai tayi bata ce dani komai ba nima ban ce da ita komai ba , na rasa kallo na ma da tayi na tausayi ne ko kuma na akasin haka,

neman guri na yi na kwanta ina kallon sama ,

In da sabo yaci ace na saba na halin ko in kula da mahaifiya ta ke nuna min.

Amma duk wannan ba shi bane damuwa ta a yanzu, damuwa sanin ina miji na yake , waye shi, da kuma inda zan same shi,

S

𝐍𝐈𝐒𝐀𝐍 𝐊𝐈𝐖𝐎Where stories live. Discover now