BABI NA BIYAR

20 3 0
                                    

Page 5

"Dumm gaba na ya bada Sakamakon jin muryar Haroon da nayi , wacce bata ɓace min a cikin zuciya da tunani na ba, tun Rana,

Sake sallama yayi jin ban amsa ba , dawowa nayi daga duniyar tunanin da na shiga , sannan na amsa sallamar, cikin siririyar Murya ta,

Ɗaga can ɓangaren Haroon yace ina fatan dai ba dai har kin yi bacci bane na tada ki, na amsa da aa ko ɗaya wayar bata hannu na yanzu na ɗauƙe ta,

Yace to masha Allah, kin gane me magana, na ce eh, sai ya tam baye ni da kin gane me magana,

na ce eh man, ya ɗan yi murmushi mai sauti wan da hat ina iya jiyo wa , sannan ya ce , to wa nene ke magana,

Ganin na kasa faɗin sunan shi na ce kai ne , ya ce ni wa , nace Kai wan da mu ka hadu ɗazu, haka dai mu ka cigaba har sai daga ƙar she ya sa na gayi sunan shi,

Sannan ya fara magana cikin natsu wa ba Kamar farko da yake tsoka nata ba,

Yace Kamar dai yadda na fada miki sunana Haroon ayuba , ni ɗan garin maiduguri ne acan aka haife ni iyaye na da kakan Nina duk ƴan can be,

bani da kowa a garin nan aiki ne ya kawo ni ina aiki a wani kamfani , na Jima ina ganin ki Allah bai bani damar yi miki magana ba sai yau,

Zahirin gaskiya ina Matuƙar son ki , ina fata zaki bani dama , shiru nayi ban ce ko mai ba, jin nayi shiru ban ce komai ba , yasa ya ce, shirun da kikai hakan Yana nuni da cewa baki amin ce dani ba,

Da sauri nace aa , sai yace to kina nufin kin bani dama nace , uhmm , yace in ko haka ne ina Matuƙar farin ciki,

Ba wannan ba yan zu yaushe zan zo gidan ku , yaushe zamu hadu na kosa ace na San ya idanu Wana a saman kwaykwar fuskar ki,

Dan murmushi nayi, sannan muka cigaba da fira , Yana ta tambaya ta abubuwa Kama ɗaga abubuwan da nafi so dadai sauran su,

Bamu farga ba har sha biyun dare ya kusa, kafin muka yi sallama, na tashi na rufo mana ƙofa na yi addua na kwanta cike da mafarki nida Haroon wai mun yi aure,

Haka abubuwan suka cigaba da faruwa a rayuwa ta, lamarin gidan mu ba abin da ya canza sai ma cigaba da yayi, lokaci ƙan Kani soyayyar Haroon ta shiga cikin zuciya ta mamaye , har a gida an San ni da shi , da irin mugun son da nake mai

Mun sha faɗa da zarah akan furi cin da take yawan yi na wai na kwace mata saurayi ganin irin hidimar da yake dani,

Bakin ciki zalla take nuna mini, a haka lokaci yaita wuce wa har muka fara shirin rubuta jara bawar fita daga secondary, sai shirye-shirye muke karatu ba Kama hannu yaro,

Har Allah yasa muka rubuta cikin sa'a ,

Cikin ikon Allah addimission ɗin mu ya fito , sai dai a wannan lokacin mun rabu,

da zarah da bina'yah, ni na samu addimission a baze University sun bani biochem, bina'yah kuma Nile University, zarah kuma tace zata shifa health school,

Baba ya min siyayyar kayan sawa da na kwalli ya da yawa, haka ma Haroon har da sabuwar waya ya canza min,

Bana zamun matsala a soyayya ta da Haroon , matsalar ɗaya ya cika kishi , ko ƴan uwana maza baya so in ɗin ga kula wa bare wani a waje,

Hakan Yana bani haushi,
Haka ranar da zan fara zuwa makaran ta na shir ya cikin dar dar , har cikin makaran ta baba ya Kai ni, sai da aka gama komai aka nuna min duk abin da ya kamata ace na sani, tare da nuna min in da zan dun ga lecture, kafin baba ya wuce,

Na shiga aji aka fara mana lecture, ina fahim ta sosai lecture din yana mun dadi, ina jotting wasu abubuwan a cikin littafin da nazo da shi,

Har nayi kwana biyu da fara zuwa wata Rana , muna cikin lecture aka kawo new student, ɗaga gani Wanda suka zo tare da ita baban tane sai shagwaɓa take zuba mai kowa ya saki baki Yana kallon ta ,

ta da kyar ta yadda ta shigo cikin class, sai magana take Kamar yarinyar da aka yaye, ni har birge ni tayi Dan ba kar ya akwai kyau

Can gefe ta zamu ta zauna, aka cigaba da lecture, bayan an gama yan class din suka hadun mata kowa na son yi mata magana, ai ko sai zuba musu shagwaɓa take , a zuciya ta na ce anya wanna lafiya take,

( Rabin labarin kadan ne daga cikin rayuwa ƙawata so dole nayi mentioning kaina ni Haya Iqbal a matsayin ƙawa gawa ga hafiza, duk shagwaɓa da nayi mentioning haka ne abin da ya faru ranar da na fara zuwa makaran ta a cikin sabon garin da ban taba sani ba )

Bayan wasu kwanaki biyun ina zaune bayan mun gama lecture naji an zauna kusa dani in juya, sai naga Haya shagwaɓaɓɓiyar ajin mu ,

ce zaune kusa dani murmushi ta min nima na mai da mata sannan ta ce sannu sunana haya Iqbal wasu na ce min cartoon za ki zama ƙawata , nace eh ba matsala ni kuma sunana Hafiza Hafiz Dan tsoho ,

Cikin iyayi ta ce la kin ga mun zama twin H kenan , sai muka ji ɗaga sama an ce aa triple H dai ga Haneefa ga hafiza ga Haya,

HAYA ce mata tayi cikin yanayi na rashin da muwa da maganar sa tayi ke kuma wacece karere , Haneefa ta nice Haneefa wato sabuwar ƙawar ku,

Haneefa tun fara zuwa na tare muke zama Amma ba matsayi ƙawaye ba sai yau da tayi mun magana , Haya ta ce mata karere a zuciya ta nace wannan yarinya akwai yarin ta ,

Haka muka zama ƙawaye mu uku a cikin makaran ta duk da cewa mun fi yawo da Haya, ada ina ganin Kamar tana da girman Kai Amma ina Ashe ba haka take ba , in bata sanka ba bata sakin jiki da mutu , Amma in ta saki jiki da Kai akwai ɗan ban zan surutu Kamar ta hadiye redio

( that me )

Mun fara nisa da karatun wannan zan ko , sai cutar Corona ta billo wan da hak........

Sai kun jini

𝐍𝐈𝐒𝐀𝐍 𝐊𝐈𝐖𝐎Where stories live. Discover now